2025-10-13@13:35:11 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1981

«Cibiyar Bauchi»:

    Labaran da suke fitowa daga kasar Falasdinu da aka mamaye sun nuna cewa kungiyar agaji ta Red Cross ta fara karban fursinoni yahudawa daga hannun kungiyar Hamas kamar yadda aka tsara. Tashar talabijan ta Almayadeen ta bayyana cewa kungun fursinoni yahudawa masu rai 7 ne kungiyar ta Karba daga dakarun Hamas a yankin da ake...
    Kungiyar ‘Yan Dako ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da Malam Muhammad Tajudeen Maigatari a matsayin sakataren kungiyar na jihar. Da yake jawabin a lokacin bikin kaddamawar a garin Maigatari, Shugaban kungiyar na jihar Malam Nasiru Idris Sara, ya bayyana shugabanci a matsayin rikon amana a maimakon hanyar tara dukiya da alfahari, a don...
      Sanarwar ta kara da cewa, “mun yi farin cikin ganin cewar yan wasan kungiyoyin biyu da jami’an wasan duk sun bar filin wasan ba tare da samun wani rauni ba kuma jami’an tsaro suka yi musu rakiya, kungiyar ta kara da cewa an kama wasu da dama da ake zargi da hannu a rikicin...
    A cewar NEMA, mutane 135,764 ne suka rasa matsugunansu, yayin da 115 aka bayyana bacewarsu, yayin da wasu 826 suka samu raunuka sakamakon ambaliyar. Bugu da kari, gidaje 47,708 sun lalace, yayin da gonaki 62,653 suka lalace a fadin jihohin da abin ya shafa.   Hukumar ta kara da cewa, daga cikin wadanda abin ya...
    A safiyar Litinin ɗin nan ƙungiyar Hamas ta saki rukunin farko na ’yan ƙasar Isra’ila bakwai da ta yi garkuwa da su a Zirin Gaza. A ɗaya ɓangaren kuma Falsɗinawa sun yi cincirindo a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan domin tarbar ’yan uwansu kimanin 2,000 da Isra’ila za ta sako. Tuni jami’an kungiyar agaji ta...
    Kasar Yemen ta gargadi gwamnatin mamayar Isra’ila kan fuskantar hare-hare masu zafi idan har ta karya yarjejeniyar Gaza A ranar Lahadin da ta gabata, Hazam al-Assad, mamba a ofishin siyasa na kungiyar Ansarullahi ta Yemen, ya gargadi gwamnatin mamayar Isra’ila kan karin fuskantar hare-hare masu zafi idan ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza....
    Cibiyar kula da lafiya ta Nasser Medical Complex da ke Gaza ya bayyana cewa: Yara 5,500 ne ke bukatar agajin gaggawa a kasashen waje Daraktan cibiyar kula da lafiya ta Al-Shifa da ke Gaza ya ce: Babu wani agajin jinya da ya shiga zirin Gaza duk da cewa an shafe sa’o’i 72 tsagaita bude wuta....
    Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan yadda shugaba Bola Tinubu ya yi wa wasu mutane afuwa, ciki har da waɗanda suka aikata manyan laifuka. A cikin saƙon da Atiku ya wallafa a shafinsa na X, ya ce ana yin afuwa ne ga waɗanda aka yi wa rashin adalci ko waɗanda suka...
    Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya ASUU a ranar Lahadi ta sanar da shiga yajin aiki na makonni biyu, wanda zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, a duka jami’o’in gwamnati na ƙasar. Shugaban ƙungiyar Farfesa Chris Piwuna ne ya sanar da hakan a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja, a ranar...
    Kasashe hudu da suka fi kokari a cikin wadanda suka kare a mataki na hudu za su fafata wasannin raba-gardama, sai wadanda suka samu nasara su sake raba-gardama da wasu kasashen na waje.   A yanzu daI manyan kasashen nahiyar ta Afirka irin su Kamaru da Nijeriya suke fuskantar barazanar rasa gurbi, duk da haka...
      Nasarorin da kasar Sin ta samu a cikin gida, sun kafa ginshikin jagorancin duniya, wajen samar da ci gaban harkokin mata, musamman ta hanyar fitar da darussa, ta hanyar kyautata mu’amala tsakamnin bangarorin biyu. Babban misali shi ne yadda ake samun bunkasar dangantakar mata tsakanin kasashen Kenya da Sin, wadda aka inganta yayin ziyarar...
    Farfesa Jeffrey Sachs na jami’ar Columbia, ya yaba wa nasarorin da Sin ta samu, inda ya ce, “shawarar ‘ziri daya da hanya daya’, wani shiri ne mai ban mamaki kuma na musamman.”   Farfesa Sachs ya fadi hakan ne a kwanan nan, yayin da wakiliyar rukunin gidan rediyo da talibijin kasar Sin wato CMG ta...
    Rundunar sojin Najeriya, ta bayyana cewa dakarunta sun kashe ’yan ta’adda biyar a wani samame da suka kai yankin Magumeri da Gajiram, a Jihar Borno. Kakakin rundunar Operation Haɗin Kai, Kanar Sani Uba, ya ce dakarun sun yi arangama da wasu ’yan ta’adda 24 da ke tafe a ƙafa a ranar Juma’a. Mutane 2 sun...
      Rundunar ‘yansanda ta tabbatar da cewa ana gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwarta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tsaro Sojoji Sun Ƙaryata Rahoton Cewa Ƴan Bindiga Sun Mamaye Sansaninsu A Kwara October 5, 2025 Tsaro Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 450, Sun Ceto Mutane 180 A Satumba — DHQ October 4,...
    Shugabannin Faransa, Jamus, da Biritaniya: Sun kuduri aniyar farfado da tattaunawa da Iran Kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya sun bayyana aniyarsu ta farfado da shawarwari da Iran da Amurka dangane da shirin makamashin nukiliyar Iran da nufin cimma cikakkiyar yarjejeniya mai dorewa. A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, kasashen uku sun yi la’akari...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya October 10, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa October 10, 2025 Daga Birnin Sin Sin...
    Aƙalla mutum takwas ’yan Ƙungiyar tsaro ta Civilian JTF ko ’yan ƙato da gora aka sanar an kashe a ƙauyen Dan Loto da ke Ƙaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara. Harin dai na zuwa ne makonni biyu kacal bayan da wasu ’yan bindiga suka kai hari a wani masallaci tare da kashe wasu masallata biyar...
    Majalisar dokokin tarayyar Turai ta amince wa kasashen nahiyar su kakkabo jiragen yakin kasar Rasha wadanda suke keta sararin samaniyar wasu daga cikin kasashen Nahiyar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa majalisar ta dauki wannan matakin ne bayan da ta sami rahotanni daga wasu daga cikin kasashen gabacin turai kan cewa...
    Bugu da kari, an rufe shafukan hakar ma’adanai haramtacce 98 a fadin kasar.   “An kiyasta cewa Nijeriya na asarar kusan Dala biliyan 9 a kowace shekara sakamakon haramtacciyar hakar ma’adanai. Wannan sata ta albarkatunmu da ya kamata ta bunkasa kasarmu ta wuce kima, kuma lokaci ya yi da za a kawo karshensa,” in ji...
    Hukumar Kwastam shiyyar bodar Najeriya ta Seme da ke jihar Legas ta ce ta cafke motoci biyar da ke maƙare da buhuna 10,000 na lalatacciyar fulawa da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.2. Rundunar ta kuma ce ta tara jimillar kuɗin shigar da ya kai Naira biliyan daya da rabi a watan Satumba, wanda hakan...
    Yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin Gaza ta fara aiki da safiyar yau, kamar yadda rundunar sojin Isra’ila ta sanar. A cikin sa’o’i 72 ne ake sa ran sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a musayar fursunonin Falasdinu. Tunda farko dama gwamnatin Isra’ila ta sanarda amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da Hamas, wadda...
    Hukumar Bunkasa Ma’aikata ta Jihar Jigawa ta shirya taron karawa juna sani na kwana daya ga jami’an kula da dakunan karatu  a wani bangare na aikinta na daga darajar ma’aikata da ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu.   A jawabinsa na bude taron, Darakta Janar na MDI, Umar Farouk Wada, ya ce makasudin shirya taron...
    A cewar kungiyar, wadannan kalubalen sun hada da takurawar dokoki daga hukumomin gwamnati, karancin isar da danyen mai daga Kamfanin Man Kasa na Nijeriya (NNPC), matsalolin da suka shafi farashin kayayyaki, da kuma tsoma bakin kungiyoyin ma’aikata da na dillalan man fetur.   ACF ta fi mayar da hankali ne kan rawar da Kungiyar ’Yan...
    Cibiyar Kula da Harkokin kasuwanci ta kasa ta bayyana kafa Cibiyar Gudanar da taron Kasuwanci na Najeriya a wani bangare na ganin ba a samarda cibiyoyi da ke da aiki iri ɗaya ba.   Babban magatakardar Cibiyar Mista Victor Olannye, ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da takardar a yayin taron jin...
    Shugaban kungiyar Hamas a Zirin Gaza kuma shugaban tawagar Falasdinawa Khalil al-Hayya ya sanar da cimma yarjejeniyar kawo karshen yaki da cin zarafin al’ummar Palasdinu, da fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin a zirin Gaza, gami da janye sojojin mamaya, shigar da kayan agaji, bude mashigar Rafah ta bangarori biyu, da musayar fursunoni....
    Gwamnatin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da tsare tsare da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar a hukumance, kamar yadda ofishin Firayim Ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar a yau Juma’a. Wannan dai na zuwa ne bayan ci gaba da tsaikon da aka samu  na tsawon kwana daya biyo bayan...
    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci dukkanin bangarorin da su yi aiki da kuma mutunta yarjejeniyar da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da kuma yin amfani da wannan  damar. Da yake jawabi a wurin taron Majalisar Dinkin Duniya, Guterres ya bayyana cewa, “Ina kira ga dukkan bangarorin da su mutunta...
    “Jami’an ‘yansanda na SIS, suka fara bincike kan rahoton, ta hanyar amfani da kaifin basira da fasaha, a hanyar filin jirgin sama, karamar hukumar Nassarawa, jihar Kano, jami’an sun kama wata mata mai suna Adama Hassan, ‘yar shekara 35 da ke da zama a karamar hukumar Deba, jihar Gombe, a ranar 6 ga Oktoba, 2025,...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI October 9, 2025 Labarai Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA  October 9, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan...
    Gwamnatin tarayya ta yi asarar jimillar gangar danyen mai miliyan 13.5 wanda kudinsa ya kai dala biliyan 3.3 sakamakon sata da fasa bututun mai tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024, in ji wata kungiya mai fafutukar kare masana’antu ta Nijeriya (NEITI). Sakataren zartarwa na NEITI, Dokta Ogbonanya Orji, ne ya bayyana hakan a Legas a taron...
    Ayatullah Sayyid Ali Khamnei  wanda ya aike da sako zuwa wurin taron kas ana raya salla karo na 32, ya yi ishara da rawar da sallolin farilla suke takawa wajen ayyana makomar mutum a duniya da kuma lahira. Haka nan kuma ya ce; Nauyi ne da ya rataya a wuyan cibiyoyin addini, da malamai da...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko October 8, 2025 Daga Birnin Sin Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan October 8, 2025 Daga Birnin Sin Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai...
    Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, sun kama mutum 12 da ake zargi da hannu a kisan ma’aikaciyar Arise TV, Somtochukwu Christella Maduagwu, a unguwar Katampe da ke Abuja. Rahotanni sun nuna cewa Somtochukwu, ta rasu bayan faɗowa daga bene mai hawa uku, yayin da ta ke ƙoƙarin tserewa daga hannun ’yan fashin, yayin da...
    Jami’an Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) a Jihar Jigawa, sun kama wani matashi da ake zargi da sato motar asibiti daga Jamhuriyar Nijar, yayin da yake ƙoƙarin shigowa da ita Najeriya. Kwanturolan hukumar a jihar, Tahir Abdullahi Musa ne, ya tabbatar wa manema labarai hakan a Dutse. Falasdinawa na murna da tsagaita wutar...
    Kungiyar Hamas ta sanar da yarjejeniyar kawo karshen hare-haren wuce gona da irin gwamnatin mamayar Isra’ila kan Gaza Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta sanar a yau Alhamis cewa, ta cimma yarjejeniyar kawo karshen hare-haren da gwamnatin mamayar Isra’ila ke kai wa Gaza, da janyewar sojojin mamaya daga cikinta, da shigar da kayan agaji da...
    Kungiyar Jihadul-Islami ta Falasdinu ta bayyana cewa: Abin da aka cimma na yarjejeniyar dakatar da bude wuta ba kyauta ce daga kowa ba Kungiyar Jihadul-Islami ta Falastinu ta bayyana cewa: Yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni da makiya yahudawan sahayoniyya ba kyauta ce daga kowa ba. A cikin wata sanarwar manema labarai da ta...
    Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kaddamar da sabuwar cibiyar taro ta Ahmadu Bello da aka gina a Bauchi, inda ya bayyana ta a matsayin alamar ci gaba a gwamnatin Gwamna Bala Mohammed.   Da yake jawabi a wajen taron, Obasanjo ya jaddada muhimmancin dunkulewar duniya, inda ya ce babu wata al’umma da za ta...
    Falasdinawan da ke Gaza da Isra’ila ta shafe sama da shekara biyu tana kai wa hare-hare sun nuna jin dadi da farin ciki bayan sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta da nufin kawo karshen yakin. Yayinda labarin yarjejeniyar ya yadu a cikin yankin da aka kewaye, mazauna Khan Younis a kudancin Gaza sun fito tituna suna...
    Ya kuma sanar da cewa an saka wa cibiyar sunan marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, domin girmama jajircewarsa da hangen nesansa a shugabanci.Gwamnan ya ƙara da cewa Bauchi na da ɗimbin albarkatun ƙasa, kuma gwamnatinsa tana ɗaukar matakai don inganta yanayin kasuwanci domin jawo hankalin ‘yan kasuwa daga cikin gida da wajen ƙasa.Taron, wanda...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa Isra’ila da Hamas sun amince da matakin farko na yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya. A wani sako da ya wallafa a kafarsa ta sada zumunta ya ce hakan na nufin nan ba da jimawa ba za a saki dukkanin wadanda ake garkuwa da...
    Ƙungiyar Ma’aikatan Manyan Makarantun Najeriya (SSANU) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ilimi (NASU), sun shirya gudanar da zanga-zangar gargaɗi ta rana ɗaya a yau Alhamis saboda Gwamnatin Tarayya ta gaza cika musu alƙawuran da ta ɗauka. Ƙungiyoyin, ƙarƙashin jagoranci Joint Action Committee (JAC), sun gudanar da taron gaggawa a ranar Laraba don shirya zanga-zangar. 2027: Atiku, Jonathan...
    Kasashen Iran, Rasha, Azerbaijan, da kuma Kazakistan sun rattaba hannu kan yarjeniyar samar da tsaro a ruwayen tekun Caspian wadanda suke tarayya a mallakarsu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kwamandojin sojojin ruwa na wadannan kasashe sun rattaba hannu a kan yarjeniyar a yau Laraba a birnin St. Petersburg na kasar...
    Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne, sun tare hanyar Gusau zuwa Gummi a Jihar Zamfara, inda suka sace mutane da dama. Wata majiya ta bayyana cewa, maharan sun tare motoci sannan suka yi awon gava da fasinjojin da ke ciki. Yadda Obasanjo ya ƙaddamar da cibiyar taron ƙasa da ƙasa a Bauchi Ban yi...
    Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ƙaddamar da sabon ginin Cibiyar Taron Ƙasa da Ƙasa, wadda aka sanya wa sunan Sir Ahmadu Bello a Jihar Bauchi. An ƙaddamar da cibiyar ne kafin babban taron zuba jari da nufin bunkasa kasuwanci da masana’antu a jihar. Ban yi murabus don ina da laifi ba — Nnaji Kamfanonin...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bai wa wata ma’aikaciyar lafiya ’yar ƙabilar Igbo kuma ‘yar asalin jihar Anambra, Marbel Ijeoma Duaka, kyautar gida mai dakuna biyu. Gwamnan ya kuma ba ɗan ma’aikaciyar aikin yi na dinidindin saboda jajircewarta da sadaukarwa wajen hidimtawa jihar na sama da shekara 20. Matar aure mai ’ya’ya huɗu...
    Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata daina samar da magungunan da take yi ta hanyar fasahar makamashin nukiliya ba Kakakin Kwamitin Tsaro da Harkokin Waje na Majalisar Shawarar Musulunci (wato Majalisar Dokoki) Ibrahim Reza’ei, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da samar da magungunan ta hanyar fasahar makamashin...
    Dakarun bangaren sojin kungiyar Jihadul Islama ta Falasdinu Sarayal-Quds ta bayyana cewa: Fursunonin mamaya ba za su ga hasken rana ba har sai an sharuddan Falasdinawa Dakarun bangaren sojin kungiyar Jihadul Islama ta Falasdinu, sun jaddada cewa: Fursunonin mamayar Isra’ila ba za su ga hasken rana ba, sai dai ta hanyar tattaunawa da musayar ra’ayi...
    Haka kuma ya buƙaci a aiwatar da gyare-gyare don farfaɗo da tattalin arziƙi, inganta ilimi da kiwon lafiya, tare da samar da damammaki ga matasa.Ya ƙara da cewa majalisar za ta sake duba Kundin Tsarin Mulki na 1999 domin bunƙasa dimokuraɗiyya da inganta mulki a Nijeriya.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC...
     Geng Shuang ya jaddada cewa, kasar Sin kasa ce da ta’addanci ya yi wa illa. Ya ce kungiyar ETIM wadda kwamitin sulhu na MDD ya ayyana a matsayin ta ta’addanci, ta taba tada rikice-rikicen ta’addanci da dama a cikin kasar Sin, kana ta gudanar da ayyukanta a kasar Syria, da Afghanistan da sauransu. Ya jaddada...
      Shugaban Kwamitin Amintattu na Ƙungiyar Tuntuba ta Arewa, Alhaji Bashir M. Dalhatu, Wazirin Dutse, ya yi kira ga mambobin ƙungiyar da su ƙara haɓaka ɗa’a, bin ƙa’ida da ƙulla zumunci yayin da ƙungiyar ke shirin gudanar da bikin cika shekaru 25 da kafuwa a watan Nuwamba 2025.   Yayin jawabin sa a taron Kwamitin...