Aminiya:
2025-12-09@02:47:18 GMT

Ƙungiya ta tallafa wa ɗaliban makarantar masu buƙata ta musamman a Gombe

Published: 24th, October 2025 GMT

Ƙungiyar Arewa Unity Women in Media, ta kai tallafi Makarantar Masu Buƙata ta Musamman da ke Gombe, domin taimaka wa gwamnati wajen kula da rayuwar ɗaliban da ke da buƙata ta musamman.

Tallafin ya ƙunshi gidajen sauro, bargo da tabarmi, wanda aka raba wa ɗaliban a lokacin bikin miƙa kayan tallafin.

’Yan sanda sun kama ɗalibi da ya soki Gwamnan Neja ’Yan sanda sun sake kama Sowore bayan kotu ta bayar da belinsa

Shugabar ƙungiyar, Lois Hassan daga GMTV Gombe, tallafin na da nuna kulawa da ƙauna ga ɗaliban, tare da tabbatar musu cewa al’umma ba ta manta da su ba.

Ta ƙara da cewa ƙungiyar Arewa Unity Women in Media ƙungiya ce mai zaman kanta da ke gudanar da ayyukan jin-ƙai domin tallafa wa marasa galihu da ƙarfafa zumunci a tsakanin al’umma.

Malaman makarantar, Joy Samuel da Maimuna Manager, sun yaba da wannan tallafi, inda suka roƙi gwamnati ta samar da magunguna a cibiyar lafiya ta makarantar.

Haka kuma, sun buƙaci ƙungiyoyi da masu hannu da shuni su yi koyi da irin wannan aiki na alheri.

Wasu daga cikin ɗaliban da suka amfana da tallafin, Comfort Ephraim da Barisasa David, sun bayyana farin cikinsu, inda suka bayyana cewa tallafin ya zo a lokacin da suke buƙata sosai.

Sun kuma roƙi gwamnati da ta gyara wutar lantarki a makarantar domin inganta tsaro da yanayin karatu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ɗalibai Ƙungiya

এছাড়াও পড়ুন:

Dorinar Ruwa ta Yi Ajalin Mutane Biyu, ta Raunata Shida a Gombe

Mutanen garin Dadin-Kowa da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, sun shiga damuwa kan yadda wata Dorinar ruwa ta addabi yankin, ta hanyar kashe mutane da kuma lalata gonaki.

Cikin watanni biyu, Dorinar ta kashe mutum biyu, ta karya wasu biyu, sannan ta jikkata wasu huɗu, waɗanda yawanci manoma da masunta ne a Dam ɗin Dadin-Kowa.

Matsalar ta sa ɗan Majalisar Tarayya na Yamaltu Deba, Inuwa Garba, ya kai koke gaban Majalisar Wakilai, inda ya nemi gwamnati ta hanzarta kawo wa mazauna yankin ɗauki.

Ya ce, “Ta’addancin Dorinar ya yi yawa. Idan ba a taimaka mana ba, za ta ci gaba da kashe mutane da lalata amfanin gona.”

A makon da ya gabata, Dorinar ta farmaki wani matashi mai suna Sama’ila Garba (Mai Lasa), bayan ya faɗa cikin ruwa.

Shaidu, sun ce dabbar ta yi ƙoƙarin kashe matashin, ta yadda hanjin cikinsa sai da ya fito, kafin a ceto shi.

Garba Zafi, ɗan uwansa, ya ce Sama’ila ya je bakin ruwa ne kawai sai ya ji ya faɗa, daga nan Dorinar ta afka masa.

Wani mazaunin garin, Akilu Gyara Sa’a, ya roƙi gwamnati ta kai musu agaji duba da yadda rayuwar mutane ke da muhimmanci.

Ya ce: “Dorinar tana lalata gonaki, tana kashe mutane. Gwamnati ta hanzarta magance matsalar kafin abin ya ta’azzara.”

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce zai bincika domin samun cikakken bayani kan lamarin.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto bai yi ƙarin haske kan lamarin ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnonin Arewa Za Su Zuba Biliyoyin Naira Don Yaki da Matsalar Tsaro
  • Kungiyar AU Ta yi Tir Da Harin Da RSF  Takai A Makarantar Kananan Yara Da Ya Kashe Mutane 80
  • Mutum 5 sun rasu sanadin gobara da faɗa wa rijiya a Kano
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 168
  • Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 167
  • Rwanda Da Amurka Sun Rattaba Hannu Kan Tallafin Dalar Amurka Miliyon $228 Na Kiwon Lafiya
  • Sojoji sun yi juyin mulki a Jamhuriyar Benin
  • Ranar Sabuwar Shekara za mu rufe duk na’urar POS mara rajista —Gwamnati
  • ’Yan sanda sun ceto yara 2 da aka yi garkuwa da su a Borno
  • Dorinar Ruwa ta Yi Ajalin Mutane Biyu, ta Raunata Shida a Gombe