Ja’afari: Iran Tana Da Isassun Makamai Masu Linzami Masu Cin Zangogi Daban-Daban
Published: 26th, October 2025 GMT
Tsohon kwamandan rundunar kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) ya bayyana cewa: Suna da isassun makamai masu linzami masu cin zango daban-daban
Tsohon kwamandan rundunar kare juyin juya halin Musulunci (IRGC), Manjo Janar Mohammad Ali Ja’afari, ya bayyana cewa: Iran ba ta da wani takunkumi kan adadin makamai masu linzami, kuma wannan karfin ya hada da nau’ikan makamai masu linzami daban-daban masu cin iyakoki daban-daban.
A wata hira da manema labarai da aka watsa jiya, Asabar, Manjo Janar Ja’afari ya yi magana kan batutuwan yanki, na kasa da kasa, da na cikin gida, ciki har da ci gaba kan bangaren ‘yan gwagwarmaya da kuma halin da ake ciki a Lebanon da Hezbollah, yana mai cewa: “Kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce, gwagwarmaya ba wani abu ne na zahiri da za a iya kayar da shi ba. Da ace gwagwarmaya wata abu ce na zahiri, da Hezbullah ba za ta wanzu har zuwa yau ba.”
Ya kara da cewa: “Duk da mummunan matsin lamba da Hezbullah ta sha, gami da hasarar manyan shugabanninta, har yanzu tana kan tafarkin gwagwarmaya. Makiya za su iya kai hari kusan kashi 30% na karfin Hezbullah, amma kashi 70% na wadannan karfin sun kasance a shirye, kuma wannan a cikin kansa shaida ce ta zurfin da karfin gwagwarmaya.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Dan Majalisar Dokokin Tarayyar Turai Ya Ce: Dole Ne A Hakunta Isra’ila Kan Laifukan Da Ta Aikata October 26, 2025 Mayakan Kungiyar Kurdawa Ta PKK Sun Fice Daga Turkiyya Zuwa Iraki October 26, 2025 Iran Za Ta Karbi Bakuncin Taron Kungiyar Tattalin Arziki TA “Eco” A Gobe Litinin October 26, 2025 Bahrain: Fursunoni 90 Suna Yajin Cin Abinci Saboda Neman ‘Yanci October 26, 2025 Shugaban Kasar Nigeria Ya Yi Sauye-sauye A Rundunonin Sojan Kasar October 26, 2025 Iran Ta Ki Zuwa Taron Sherme-Sheikh Ne Saboda Kar Ta Zama Mai Shaidar Zur Akan Kisan Kiyashin Gaza October 26, 2025 Jami’ar ABU Ta Karyata Zargin Da Ake yi Na Kera Makamin Nukiliya A Asirce October 25, 2025 M D D Ta ce Akalla Mutane miliyan 1.5 Ne Ke Bukatar Taimakon Gaggawa A Gaza October 25, 2025 Tony Balai Na Fuskantar Turjiyar Kasashen Larabawa Game Da Rawar Da Zai Taka A Gaza. October 25, 2025 Yau Ne Ake Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Ivory Coast October 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Ce: Shugaban Amurka Zai Ci Gaba Da Kasancewa Cikin Rudu
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya fadawa shugaban Amurka Trump cewa ya ci gaba da rayuwar cikin mafarkinsa!
A jawabin da ya gabatar a gaban Majalisar Dokokin Isra’ila ta “Knesset”, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa ya lalata cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya, amma kalmomi biyu kacal da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci a Iran, Ayatollah Sayyed Ali Khamenei, ya furta sun isa su zame a matsayinsa mayar da martani.
Ya zo cikin Shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa: Alfaharin Shugaban Amurka cewa: “Hakika sun yi luguden wuta kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran tare da ruguza su, tabbas wannan da’awa ce kawai, amma Amurkawa su ci gaba da rayuwa cikin wannan ruɗunsu!”
Martani mai ƙarfi da Iran ta kai kan haramtacciyar kasar Isra’ila da sansanin Amurka da ke kasar Qatar ya rusa ruɗanin Trump da Isra’ila. Abin da Trump ya faɗa ba komai ba ne illa ƙoƙarin ɓoye gazawarsa da kuma ƙarfafa ƙarfin gwiwar mazauna yankin.
Amma gaskiyar magana a ƙasa abin mamaki ne: makamai masu linzami na Iran sun shiga cikin Isra’ila, sun barnata wurare masu mahimmanci kuma sun mayar da su toka.
Bayan kwanaki 12 kacal, mamayar ba ta da wani zaɓi illa ta ɗaga tuta fari ta nemi a tsagaita wuta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ya Ce: Iran, Rasha Da China Sun Aike Da Sako Mai Muhimmanci October 26, 2025 Ja’afari: Iran Tana Da Isassun Makamai Masu Linzami Masu Cin Zangogi Daban-Daban October 26, 2025 Dan Majalisar Dokokin Tarayyar Turai Ya Ce: Dole Ne A Hakunta Isra’ila Kan Laifukan Da Ta Aikata October 26, 2025 Mayakan Kungiyar Kurdawa Ta PKK Sun Fice Daga Turkiyya Zuwa Iraki October 26, 2025 Iran Za Ta Karbi Bakuncin Taron Kungiyar Tattalin Arziki TA “Eco” A Gobe Litinin October 26, 2025 Bahrain: Fursunoni 90 Suna Yajin Cin Abinci Saboda Neman ‘Yanci October 26, 2025 Shugaban Kasar Nigeria Ya Yi Sauye-sauye A Rundunonin Sojan Kasar October 26, 2025 Iran Ta Ki Zuwa Taron Sherme-Sheikh Ne Saboda Kar Ta Zama Mai Shaidar Zur Akan Kisan Kiyashin Gaza October 26, 2025 Jami’ar ABU Ta Karyata Zargin Da Ake yi Na Kera Makamin Nukiliya A Asirce October 25, 2025 M D D Ta ce Akalla Mutane miliyan 1.5 Ne Ke Bukatar Taimakon Gaggawa A Gaza October 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci