2025-12-03@23:36:31 GMT
إجمالي نتائج البحث: 9411
«Hadimin Gwamna»:
Gwamnonin Arewaci, na shirin dakatar da haƙar ma’adinai a wasu yankuna da ake fama da matsalar tsaro, domin daƙile ayyukan ’yan bindiga da sauran ƙungiyoyin ta’addanci. Wannan batu ya fito ne daga taron haɗin gwiwa na Gwamnonin Arewa da Majalisar Sarakunan Gargajiya da aka yi a Kaduna daga 1 zuwa 2 ga watan Disamba, 2025....
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta ce ta samu rahoton laifuka 25 na cin zarafin mata da ƙananan yara a Ƙananan Hukumomin Jakusko, Fika, Potiskum da Tarmuwa, inda aka kama mutum 28 da ake zargi da aikata laifukan. Kakakin rundunar, SP Abdulkarim Dungus, ya ce an kama masu laifin ne cikin watanni uku da suka...
Tsohon Ministan Tsaro, Abubakar Badaru, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya san dalilin da ya sa ya yi murabus. Badaru, ya ajiye aiki ne a ranar Litinin, inda ya ce matsar rashin lafiya ce ta sa ya yi murabus. Ƙudirin dokar hukuncin kisa ga masu satar mutane ya tsallake karatu na biyu Tsaro: Gwamnatin Kano...
Majalisar Dattawa ta amince da wani sabon ƙudiri da ke neman a gyara dokar yaƙi da ta’addanci, domin a ɗauki garkuwa da mutane a matsayin babban laifi na ta’addanci. Ƙudirin, wanda Sanata Opeyemi Bamidele ya gabatar, ya tanadi hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin satar mutane, ba tare da wata zaɓin tara...
Babban zauren MDD ta amince da kudurori guda biyu wadanda suka yi tir da HKI a jiya talata dangane da mamayar da take yiwa kasar Falasdinu tun shekara 1967 da kuma tuddan golan na kasar Siriya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa HKI ta mamaye tuddan golan na kasar Siriya ne...
An ga jiragen ruwan yaki da kuma jiragen sana na yaki na Amurka Ponce, da kuma Puerto rico a jiya talata, wanda yake kara tabbatar da Shirin Amurka na mamayar tada rikici a yankin Caribian musamman kuma a kasar Venezuela. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar iran ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Trump tana kara...
Daga Bello Wakili Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) da kwamishinoni biyu na hukumar, tare da sabbin manyan sakatarori guda biyar da aka nada a gwamnatin tarayya. Daga nan ya jagoranci taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Bayan karanta takardar tarihin rayuwarsu,...
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa na shirin sayen jirage marasa matuƙa da wasu kayan aiki domin kare yankunan da ke iyakar Kano da Katsina. Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba. Gobara ta ƙone kasuwar katako a Abuja CBN ya...
Wata gobara ta tashi a ranar Laraba ta ƙone kasuwar katako da ke kusa da Jabi Masallaci a Abuja. Gobarar ta lalata kaya da kayan gini na miliyoyin kuɗi, amma ba a yi asarar rai ba. CBN ya kara yawan kudin da mutum zai iya cirewa a mako zuwa N500,000 Gobara ta kashe mata da...
Daga Ali Muhammad Rabi’u An samu mummunan rikici tsakanin mambobin ƙungiyoyin asiri wanda ya shafi tsofaffin daliban kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kwara da ke Ilorin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya. Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa dalibin mai suna Oyelade Olawale wanda ya karanci aikin Injiniya a fannin Gine-gine, ya rasu ne...
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya soke iyakance adadin kuɗin da mutum ko kamfani za su iya ajiyewa a banki sannan ya ƙara yawan kudin da za a iya fitarwa a mako da ₦100,000 zuwa ₦500,000. Wannan na cikin wata sanarwa da Daraktar Sashen Tsarin Kuɗi da Dokoki ta bankin, Dr. Rita Sike, ta sanya wa...
Wata gobara da ta tashi da safiyar Litinin ta kashe magidanci da matarsa da ’ya’yansa uku a unguwar Kofar Sauri da ke cikin garin Katsina. Wadanda gobarar ta rutsa da su sun haɗa da Muhammad Habibu mai shekara 35, matarsa Fatima Muhammad, da ’ya’yansu uku; Khadija, Abubakar, da Aliyu, wadanda dukkansu suka ƙone har lahira....
Daga Aliyu Muraki Hukumar Ilimi Matakin Farko ta Jihar Nasarawa (NSUBEB) ta yi barazanar kamawa tare da gurfanar da iyayen da ‘ya’yansu ba sa zuwa makaranta a jihar. Shugaban Hukumar, Dr. Kasim Mohammed Kasim ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a matsayin wani bangare na ayyukan babban taron inganta ilimi da hukumar...
Wani ya yi shigar mahaifiyarsa da ta mutu ya je karvar kuxin fanshonta Ana binciken wani tsohon ma’aikacin jinya a qasar Italiya bisa zargin ya yi shigar mahaifiyarsa da ta mutu kuma ya je ma’aikatar fansho a matsayin mahaifiyarsa don neman fanshonta. Haka kuma an gano ya voye gawarta a cikin gidansa har tsawon shekaru...
Har yanzu ban bar yin waqa ba-Yusuf Lazio Daga Musa Kutama, Kalaba Yusuf Muhammad Abdullahi da aka fi sani da Yusuf Lazio, fitaccen jarumi ne a Masana’antar Finafinan Hausa, wato Kannywood. Jarumin ya yi shura a fim xin Na-Ladidi, inda ya ce, haxa waqa da fim a lokaci xaya, a wurinsa ba wani abu ba...
Majalisar Dokokin Jihar Akwa Ibom ta ƙi amincewa da wani kudiri da ya nemi haramta ci da sayar da naman kare a jihar. Kudirin, wanda ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Etinan, Uduak Ekpoufot ya gabatar ranar Talata, bai samu ko da dan majalisa daya da ya mara masa baya ba. Yau Majalisar Dattawa za ta...
Majalisar Dattawan Najeriya za ta tantance wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a matsayin Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, a zamanta na yau Laraba. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga ofishin Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Opeyemi Bamidele. Mako mai Majalisa za ta kada ƙuri’a kan ƙudurin ƙirƙirar sabbin jihohi...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na ‘Sharhin bayan labarai, wand ani tahar amin zan karanta. A cikin shirimmu na yau zamu yi Magana dangane cewa, shin gaskiyar ne ‘HKI tana fama da karancin sojojin a dukkan rassan sojojin kasar’. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran...
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa tsohon babban hafsan tsaron, Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaron Nijeriya Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ranar Talata. An yi garkuwa da manoma 11 a Kudancin Kaduna Mutane 9,854 na ɗauke da cutar AIDS a Yobe Sanarwar...
Majalisar Dattawa ta sanar da aiwatar da sauye-sauye a wasu muhimman kwamitocinta waɗanda suka haɗa har da na tsaro da na tattara bayanan sirri, sakamakon ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta. Shugaban Majalisar Dattawan, kuma shugaban kwamitin majalisar kan harkokin zaɓe, Sanata Godswill Akpabio ne ya sanar da hakan yayin zaman na yau Talata. Mutane...
Daga Bello Wakili Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro. A wata wasika da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Shugaba Tinubu ya mika sunan Janar Musa domin ya maye gurbin Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya yi murabus a ranar Litinin. Janar Musa,...
Gwamnatin Yobe ta bayyana cewa aƙalla mutane 9,854 ne ke ɗauke da cutar AIDS a jihar, kuma dukkaninsu na karɓar maganin ceton rai. Hukumar ta tabbatar da cewa waɗannan marasa lafiya suna rayuwa cikin ƙoshin lafiya, tare da rage yiwuwar yaɗa cutar ga wasu. Babban Daraktan Hukumar Kula da Cutar AIDS ta Jihar Yobe (YOSACA),...
Fargaba ta lulluɓe al’ummar Ungwan Nungu da ke gundumar Bokana a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna, bayan wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mazauna yankin 11 a ranar Asabar yayin da suke dawowa daga gonakinsu. Mazauna yankin sun ce an tare mutanen ne a wata hanyar daji da ke kusa da unguwar da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar kansar mama na ɗaya daga cikin manyan cututtukan da ke addabar mata a Najeriya da ma duniya baki ɗaya. An kiyasta cewa mata sama da dubu ɗari biyu na kamuwa da cutar a kowace shekara a Najeriya, yayin da miliyoyin mata a duniya ke fama da...
Wakilan kasashen Afirka da suka hallara a birnin Algiers sun sabunta wani yunkuri don amincewa da laifukan ‘yan mulkin mallaka a hukumance, tare da ayyana mulkin mallaka a matsayin laifi kan bil’adama, da kuma tabbatar da an biya diyya bisa ga barna da cin zarafi da aka yi wa al’ummomin Afirka. Taron, wanda aka gudanar...
Jagoran ‘Yan Jam’iyyar Democrat na Majalisar Dattawa Chuck Schumer ya zargi Shugaban Amurka Donald Trump da shirya yaƙi a ɓoye a kan kasar Venezuela, yana mai jaddada cewa ikon ayyana yaƙi ya rataya ne kawai a kan Majalisa, kuma dan majalisar ya bayyana cewa zai gabatar da kuduri don hana tura sojojin Amurka yaki a...
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Shugaban Amurka Donald Trump na cire Pretoria daga taron G20 na shekara mai zuwa, yana mai sake tabbatar da matsayin Afirka ta Kudu na memba da aka kafa wannan dandali na kasa da kasa tare da ita. Trump ya sanar a ranar Laraba da...
Daga Bello Wakili Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa nan take. Sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce wasikar da Badaru ya aika wa Shugaba Bola Tinubu mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Disambar 2025, ta yi bayanin...
Daga Bello Wakili Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa nan take. Sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce wasikar da Badaru ya aika wa Shugaba Bola Tinubu mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Disambar 2025, ta yi bayanin...
165-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku, kissoshi wadanda suka zo cikin Alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Mrtada Muttahari, ko kuma cikin littafan Mathnawa na maulana Jalaluddeen Rumi....
Daga Shamsuddeen Mannir Atiku Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta karɓi daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026 da ya zarce naira miliyan dubu dari tara da tamanin da biyar daga bangaren zartarwa jihar. Da yake gabatar da kasafin kudin a zauren majalisar, Gwamna Malam Uba Sani ya bayyana kasafin a matsayin na sauye-sauye da ci-gaba wanda aka...
164-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku, kissoshi wadanda suka zo cikin Alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Mrtada Muttahari, ko kuma cikin littafan Mathnawa na maulana Jalaluddeen Rumi....
Paparoma Leo 14 wanda yake ziyarar aiki na kwanaki uku a kasar Lebanon ya gana da shugaban kasar Lebanon Josept Aun da kuma manya-manyan malamai da shuwagabannin kungiyoyin yan siyasa a kasar Lebanon. A jawabin da ya gabatar a gaban wadannan shuwagabannin kasar Lebanon Lio na 14 ya bukaci, su rungumi zaman tare da kuma...
Anicen Ekane dan adawa na jam’iyyar African Movement for New Independence yana daga cikin fitattun yan siyasa a kasar Kamaru, kuma yana goyon bayan Issa Chiroma a zaben shugaba kasa wanda aka gudanar a kasar a cikin watan Octoban da ya gabata. Issa Chiroma dai ya shelanta cewa shi ya lashe zaben shugaban kasa wanda...
An kama wasu mutum huɗu da ake zargin ’yan bindiga ne ɗauke da makamai da ake zaton bindigogi ne a tashar mota ta Ƙofar Ruwa da ke Jihar Kano. Tashar motar, wadda ke kusa da kasuwar kayan gini ta Ƙofar Ruwa a Ƙaramar Hukumar Dala. MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai...
Hukumar kididdiga ta HKI ta basa sanarwan cewa yawan yahudawa da suke ficewa daga haramtacciyar kasar . Tashar talabijin ta Almayadeen na kasar Lebanon ta nakalto hukumar na bada labarin cewa a shekara ta 2010 yawan masana wadanda suke da shahadar Jami’a ya karu ha rya kai kashi 46% sannan wannan adadin ya cilla sama...
Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya shawarci gwamnonin jihohin Arewa 19 su riƙa sauraron masu sukarsu tare da amfani da shawarwarin da ake ba su domin inganta salon mulkinsu. Ya bayar da wannan shawara ne a ranar Litinin, yayin taron haɗin gwiwar Gwamnonin Arewa da Sarakunan Gargajiya a Kaduna. ’Yan sanda sun gano zinaren N23m...
’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 13 da suka gabata a Jihar Borno. Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren da suka ɓace...
’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinwu ta kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 12 da suka gabata a Jihar Borno. Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren waɗanda suka haɗa...
Daga Bello Wakili Najeriya ta ƙarfafa ƙoƙarinta na kawar da cutar HIV nan da shekarar 2030, inda Uwargidar Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga ’yan Najeriya, shugabanni da jami’an lafiya su haɗa hannu wajen cimma wannan manufa. Yayin jawabi a bikin ranar Yaki da Cutar AIDS ta Duniya ta 2025 da aka...
Daga Ali Muhammad Rabi’u ’Yan bindiga kimanin guda huɗu dauke da makamai sun kai hari a garin Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a jihar Kwara, inda suka sace wani manomi mai suna Mista Aasaru. Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa wannan hari shi ne na biyu da aka kai wa garin Eruku cikin wata guda,...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma. Mai magana da yawun Hamas, ya bayyana cewa duk da cewa kungiyar ta na girmama yarjejeniyar tsagaita wuta sosai, gwamnatin mamayar Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar, wanda...
Daga Abdullahi Jalaluddeen Gwamnatin Jihar Kano ta sha alwashin daukar mataki kan masu yin haya da babura a fadin jihar. Mai bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Sufuri, Alhaji Danladi Idris Karfi, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Kano. Ya ce gwamnatin ta lura da yadda aka cigaba da yin haya...
Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa za ta sanyar da sinadarin uranium dinta a kasuwar duniya ga wanda ta ga dama bayan da gwamnatin kasar ta mayar da hakar uranium ga kamfanin kasar a watan Yuni. Hakar ma’adinan uranium a Nijar na daga cikin batutuwan da suka fi daukar hankali tsakanin gwamnatin soji data kwace...
’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani fasto da matarsa da mabiyansa a yayin da suke tsaka da ibada a coci da ke a Jihar Kogi. Wani ganau da ke cikin cocin a lokacin da aka kai harin, Adegboyega Ogun, ya ce misalin ƙarfe 9.30 na safe ’yan bindigar suka kai harin suna bude wuta....
Ana ci gaba da ta ƙaddama kan Naira dubu ɗari bakwai da hamsin da Jami’ar Amurka ta Maryam Abacha (MAAUN) da ke Jihar Kano ta wajabta wa ɗalibanta da suka kammala karatu biya a matsayin kuɗin bikin yaye ɗalibai. Jami’ar MAAUN ta sanya wa kowane ɗalibin da ya kammala karatu biyan Naira dubu ɗari bakwai...
Fira ministan HKI Benjamin natanyaho ya bukaci yafiyar shugaban kasa game da shari’a da aka dade ana yi kan zargin da ake masa na cin hancin da rashawa da mutane da sauran yan siyasa ke Allah wadarai da shi. Mazu zanga zanga sun mamaye gidan shugaban gwamnatin isra’ila Isaac Herzog inda suka yi tir da...
Tsohon mai magana da yawun jam’iyyar PDP na ƙasa, Olisa Metuh, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki. Ya ce ya yanke wannan shawara ne saboda PDP ta kasa goyon bayansa lokacin da yake cikin matsaloli. Sojoji sun ceto ’yan mata 12 da ISWAP suka sace a Borno ’Yan bindiga sun sace amarya da...
Sojojin Rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), sun samu nasarar ceto ’yan mata 12 da ’yan ta’addan ISWAP suka sace a gundumar Mussa da ke Ƙaramar Hukumar Askira/Uba a Jihar Borno. An sace su ne ranar 23 ga watan Nuwamba 2025, yayin da suke girbe amfanin gonakin iyayensu. Yaran ’yan shekaru 15 zuwa 20 ne. Wannan...
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu a Gaza ta sanar da cewa; An sami shahidai 3 da aka kai su asibitin a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata. Shi kuwa ofishin gwamnati dake Gaza ya sanar da cewa, daga tsagaita wutar yaki zuwa wannan lokacin, sau 591 Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta keta wutar yaki. Ofishin...
