2025-12-14@00:42:08 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1233
«ƙwarewar fasaha»:
Gidan Talbijin na Jihar Jigawa wato JTV, ya fara gudanar da gyare-gyaren doguwar eriyar yada shirye-shiryen tashar dake garin Andaza. Da yake yiwa shugaban gidan Talabijin na JTV Alhaji Abba Tukur karin bayani kan fara aikin, jagoran tawagar injiniyoyin, Injiniya Obi Onya, ya ce za su gudanar da aikin ta hanyar gano sassan doguwar eriyar da suke da matsala. Injiniya Onya ya bayyana cewar, haka kuma za su gudanar da irin wannan aikin a kananan tashoshin yada shirye-shiryen tashar dake garuruwa 3 na kananan hukumomi a Jihar. Yana mai cewar, garuruwan su ne Gumel da Hadejia da kuma Kazaure. Shugaban gidan talabijin din wanda ya sami wakilcin Manajan Sashin injiniya na JTV, Malam Sha’aban Abubakar Tahir, ya...
Majalisar Jigawa Ta Bukaci Kananan Hukumomi Su Gabatar da Kasafin Kudinsu a Zangon Farko na Sabuwar Shekara
Daga Usman Muhammad Zaria Shugaban kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa, Alhaji Aminu Zakari, ya bukaci ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar tabbatar da ganin cewa kananan hukumonin jihar 27 sun wallafa cikakken kundin kasafin kudadensu cikin zangon farko na sabuwar shekara. Alhaji Aminu Zakari wanda shi ne wakilin mazabar Gwiwa, ya bayyana haka ne lokacin tantance kiyasin kasafin kudin sabuwar shekara na ma’aikatar kananan hukumomi. Ya kuma yi kira ga ma’aikatar da ta duba batun rashin biyan albashi ga wasu daga cikin nadaddun kansiloli, kasancewar yanzu haka akwai nadaddun kansiloli 21 da ba sa samun albashin su. Ya kara da cewar, kwamitin ya samu koke kan tsallake albashin wasu ma’aikatan kananan hukumomi sakamakon aikin tantance ma’aikata na...
Gwamnonin Bauchi, Neja, Kano, Gombe, da wakilan gwamnan Borno da na Yobe da sauran jihohi duk sun halarci jana’izar. Daga karshe dai an kwantar da marigayin a cikin masallacinsa sashin Rauda da ke unguwar Makera a cikin garin Bauchi. Shaikh Dahiru dai an haife sa ne a ranar 28 ga watan June 1927, wanda ya yi daidai da 2nd Al-Muharram 1346 A.H. An samu fadin shekarunsa daban daban wasu su ce shekarunsa 98, wasu su ce 101, wasu kuma su 102. Hakan ya faru ne sakamakon wasu na amfani da ranar haihuwar da aka haifesa na boko yayin da wasu kuma ke lissafi da watan musulunci na hijira. Ya rasu ya bar ‘ya’ya sama da 100 yayin da 18 daga...
Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor) daga Jihar Kano: Laifi ai na iyayenta ne me ya sa basu yi bincike ba kafin azo wannan gabar. Ya kamata ace ana yin buncike kamar yadda a baya al’adar Malam bahushe ce buncike kafin Aure daga bangaren mijin har na matar. Wani yana gudun kar ya fadi aibin dansa ko ‘yarsa a karshe su rasa masu Aurensu, wanda hakan babbar matsala ce. Ka fadi gaskiya idan mutum ya ga zai iya to, shikenan in ba zai iya ba Allah ya kawo wani. Sunana Khadija Auwal Koki, A Jihar Kano: Eh to, gaskiya laifin mijin ne da kuma danginsa tunda an san maganar aure ba wasa bace ya kamata ace an fadawa...
Gwamnatin Jihar Kano ta fitar sanarwar umarnin haramta kafa wa, da ɗaukar aiki da gudanar da duk wata ƙungiyar Hisbah mai zaman kanta a jihar, inda ta dakatar da ƙungiyar Independent Hisbah Fisabilillahi da tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ke shirin Ƙirƙirowa. Kwamishinan yaɗa labarai ne ya sanar da hakan a taron manema labarai a Kano, yana mai cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu kan umarnin ne domin kare zaman lafiya da kuma kare sahihancin Hukumar Hisbah ta Jihar Kano da doka ta kafa. Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano Ƙirƙirar Hisbah Mai Zaman Kanta: Kungiyar Lauyoyi ‘Yan Kano Ta Shigar Da Tinubu Ƙara Umarnin ya bayyana cewa duk wani...
Ya kara da cewa mutanen Batsari sun dade da wannan sana’a ta noman Rogo tun Iyaye da kakanni, wanda ya ce haka ta sanya ya baiwa hukumar bunkasa kanana da matsakaitun sana’o’i umarnin kafa masana’anta ta sarrafa Rogo a Batsari “Abin da muke gani shi ne, samar da wannan masana’anta zai kawo bunkasar tattalin arziki sannan ya rage asarar da manoma ke yi wajen samar da abinci sannan zai samar da ayyukan yi ga matasa tare da karfafa al’umma su kara shiga harkar noman Rogo” inji shi ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tattalin Arziki CBN Ya Tura Dala Miliyan 50 Don Ƙarfafa Kasuwar Musayar Kuɗaɗe November 28, 2025 Tattalin Arziki Masu Baje Koli 1,000 Za Su Baje Hajarsu A Kasuwar...
Daga Usman Muhammad Zaria Aikin rigakafin watan Disamba a karamar hukumar Sule-Tankarkar ta jihar Jigawa ya samu gagarumar nasara, yayin da iyaye suka fito kwansu da kwarkwata domin tabbatar da cewa an yi wa ’ya’yansu cikakken rigakafi. Wasu daga cikin iyayen da suka kawo ’ya’yansu domin karbar rigakafin yau da kullum da na shan inna sun bayyana jin dadinsu kan yadda aka gudanar da aikin cikin kwanciyar hankali. Daya daga cikinsu, Malama Ummahani Danbala, ta ce an wayar da kan jama’a sosai ta hannun mata ’yan sa-kai a unguwarsu, inda aka karfafa gwiwar iyaye mata su kawo ’ya’yansu domin karbar rigakafin yau da kullum da na shan inna. Malam Yunusa, wani mai sa ido a karamar hukumar, ya...
Ɗan wasan gaban Ƙungiyyar Ƙwallon Ƙafa ta Galatasaray ɗan asalin Najeriya, Victor Osimhen ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasa na bana, a bikin bayar da kyaututtuka ta GQ Türkiye na maza na 2025. Ɗan wasan mai shekara 26 ya sami kyautar mafi girma a bikin da aka gudanar mai ban sha’awa. Matatar man Dangote ta rage farashin fetur zuwa N699 Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Binuwai Ya sami kyautar ne saboda rawar da ya taka a Galatasaray a kakar wasa ta bara, inda ya zura ƙwallaye 37 kuma ya taimaka wajen zura ƙwallo sau bakwai a wasanni 41, wanda hakan ya sa Galatasaray ta lashe gasar Turkiya. Osimhen ya karya tarihin Galatasaray na zama ɗan wasan da ya...
A ci gaba da al’adar fiye da shekaru 30, Ministan Harkokin Wajen Sin Wang Yi ya ziyarci kasashen Afirka da dama a tsakanin 5-11 ga watan Janairun 2025 don sake tabbatar da dangantakar diflomasiyya da kuma binciko sabbin hanyoyin hadin gwiwa. Wannan ziyarar ta sake tabbatar da manufar ci gaba da cin moriyar juna a tsakanin bangarorin biyu. Baje kolin tattalin arziki da ciniki na Sin da Afirka na hudu a Changsha An gudanar da wannan taron baje kolin na hudu daga 12 zuwa 15 ga watan Yunin bana a Changsha, babban birnin lardin Hunan. Baje kolin ya tattaro kusan kamfanonin Sin da Afirka 4,700, kuma an baje kolin kayayyakin Afirka sama da 800 daga kasashe da dama....
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Hukuncin Kisa Kan Maryam Sanda December 12, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Yaba Wa Jami’an Tsaro Kan Ceto Dalibai 100 Da Aka Sace A Neja December 12, 2025 Manyan Labarai NLC Ta Shirya Zanga-Zangar Rashin Tsaro A Faɗin Ƙasa Ranar 17 Ga Disamba December 12, 2025
Kotun Kolin Najeriya ta soke afuwar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi wa Maryam Sanda, inda ta ce shugaban ya wuce makadi da rawa ta hanyar yin afuwa ga wacce har yanzu kararta ke gaban kotu. A hukuncin da aka yanke ranar Juma’a, kotun ta yanke hukunci da rinjayen alƙalai huɗu cikin biyar, inda ta tabbatar da hukuncin kisa da Babban Kotun Abuja ta yanke, kuma Kotun Daukaka Kara ta tabbatar. ‘Haduwata da masu garkuwa da ɗan uwana a dajin Zamfara’ Jam’iyyar PDP ta tabbatar da mutuwar mataimakin Gwamnan Bayelsa An yanke wa Sanda hukunci ne a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, a lokacin rikicin cikin gida a gidansu da ke Abuja. Kotun ta yi watsi...
Taron Abuja kan Tattaunawakan Tattalin Arziki Kasa- “Akwai yiyuwar tattalin arzikin kasa zai murmure a shekarar 2026”
Taron Abuja kan Tattaunawakan Tattalin Arziki Kasa- “Akwai yiyuwar tattalin arzikin kasa zai murmure a shekarar 2026” Masana a Taron Abuja na Tattaunawa kan Tattalin Arziki Kasa da ake wa lakabi da Abuja Economic Dialogue 2025 da Kamfanin Ignite Capital ke shiryawa duk shekara da haxin gwiwar Kamfanin Innovision Global Consulting sun yi hasashen cewa, za a samu saukar kayan masarufi da Karuwar samar da ayyukan yi a faxin kasa a shekara mai zuwa ta 2026. Masana tattalin arzikin da suka yi fashin baki kan yadda tattalin arzikin Nijeriya ke tafiya a cikin watanni tara da suka gabata, a taro sun haxa da Dakta Paul Arinze, Shugaban Kamfanin Bincike da Nazari kan harkokin tattalin arziki mai suna Pedestal Africa da Dakta...
A Legas farashin shinkafa ya fadi sosai A kasuwannin Mushin da Daleko, farashin buhun shinkafa kilo 50 da ake sayar da shi a da Naira N75,000 cikin Nuwamba, a yanzu ya dawo Naira 54,000. Jihar Delta A Jihar Delta, musamman a Asaba, farashin kayan abinci ya daidaita a manyan kasuwanni irin su Kasuwar Oko (Hausa), Midwifery Market da Ogbogonogo Market, sai dai a kasuwannin mako-mako na kauyuka. Bincike a babban birnin jihar ya nuna cewa farashin muhimman kayan abinci ya dan daidaita, amma ‘yan kasuwa da masu sayayya sun nuna damuwa kan karancin kudin da ake da shi don sayayya. Kwandon tumatir da ake sayarwa Naira 5,000 a wasu watanni da suka gabata, yanzu ya sakko Naira 4,000....
Hukumar kwallon kafa ta Nigeria (NFF) ta taya Osimhen murnar samun wannan babbar nasarar a kwallon kafa ta hanyar sanya hoton Osimhen a babban shafinsu na Facebook da yake da mabiya fiye da miliyan daya, Osimhen na daga cikin yan wasan da kocin tawagar ta Super Eagles Eric Chelle ya gayyata domin buga gasar kofin kasashen Afirka da za a buga a Morocco a shekara mai zuwa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Salah Ba Ya Cikin ‘Yan Wasan Liverpool Da Za Su Kara Da Inter Milan December 8, 2025 Wasanni Shirye-shiryen Fara Kofin Afirka: Abin Da Ya Kamata Ku Sani December 7, 2025 Wasanni Liverpool Ba Ta Yi Min Adalci Ba – Muhammad Salah December 7, 2025
Jam’iyyar PDP a ranar Alhamis ta tabbatar da mutuwar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo. Jam’iyyar ta tabbatar da rasuwar ce a cikin wata sanarwa da sakatarenta yada labaranta na kasa, Kwamared Ini Ememobong, ya fitar. Rahotanni sun ce Ewhrudjakpo ya yanke jiki ya faɗi a ofishinsa da ke gidan gwamnati, Yenagoa, a ranar Alhamis, inda aka garzaya da shi zuwa Cibiyar Lafiya ta Ƙasa (FMC) da ke Yenagoa. Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis. An haifi Ewhrudjakpo ranar ranar biyar ga watan Satumban 1965, a ƙauyen Ofoni da ke Ƙaramar Hukumar Sagbama, Jihar Bayelsa. Ya rasu yana da shekaru 60. Kodayake ba a san ainihin dalilin faɗuwarsa ba, majiyoyi sun ce ya faɗi ne ba zato ba...
Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar kula da masu bukata ta musamman a jihar Jigawa za ta gudanar da aikin gyaran gidajen gajiyayyu na shiyyar Birnin Kudu da Gumel a sabuwar shekara. Shugaban hukumar, Malam Sale Zakar Kafin Hausa, ya bayyana haka lokacin kare kiyasin kasafin kudin 2026 a gaban kwamatin harkokin mata na majalisar dokokin jihar Jigawa. Ya ce gidan gajiyayyu na shiyyar Birniwa yana cikin kyakkyawan yanayi da kulawa sosai ta fuskar abinci da sutura da kayan wanka da na wanki da sauran bukatun rayuwa, dan haka gwamnati ta kuduri niyyar gyara sauran gidajen gajiyayyun domin kyautata yanayinsu. Malam Sale Zakar ya ce an Kara yawan mata masu juna biyu da masu shayarwa da ke amfana da Shirin kula...
Zuwa karfe 5:41 na daren ranar 7 ga watan Disamba, fim din Amurka “Zootopia 2” wanda aka fara nuna wa kwanaki 12 da suka wuce (tun daga ranar 26 ga Nuwamba), ya samu kudaden shiga a cikin kasar Sin da yawansa ya wuce yuan biliyan 30 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 424.8, adadin da ya zarce kudaden shiga da ya samu a kasashen Arewacin Amurka, har ya sa kasar Sin ta zama kasa mafi taka rawa wajen samar da kudin shiga ga wannan fim a duniya. Hakan kuma ya nuna yadda Sin ke da babbar kasuwar fina-finai. Ibrahim Akopari Ahmed, jami’in kula da harkokin cinikayya a Najeriya, a zantawarsa da dan jarida a baya, ya taba bayyana cewa, “Najeriya na daya...
Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda ta Najeriya, tare da haɗin gwiwar Rundunar ’Yan Sandan Kasar sun buɗe shafin neman aiki domin ɗaukar sabbin ’yan sanda na constables da kuma ma’aikata masu kwarewa ta musamman. A kwanan nan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin ɗaukar sabbin ’yan sanda 50,000 a fadin ƙasar domin ƙarfafa tsaron cikin gida da kuma ƙara yawan jami’an da za su taimaka wajen yaƙi da laifuka da rashin tsaro. Za a buɗe shafin neman aiki daga 15 ga watan Disamba, 2025 zuwa 25 ga Janairu, 2026. Ga yadda yadda za ku cike neman aikin daki-daki: Mataki na 1: Duba cancantarka Dole ne ka kasance ɗan Najeriya ta hanyar haihuwa. Ka kasance lafiyayye a...
Daga Usman Muhammad Zaria Ma’aikatar mata da walwalar jama’a ta jihar Jigawa za ta kashe naira milyan dubu 10 da milyan 599 wajen gudanar da manyan ayyuka da harkokin yau da kullum a sabuwar shekara. Kwamishinar ma’aikatar, Hajiya Hadiza Abdulwahab, ta bayyana hakan lokacin kare kiyasin kasafin kudin ma’aikatar a gaban kwamatin harkokin mata na majalisar dokokin jihar Jigawa. A cewar ta, za su mayar da hankali wajen inganta shirye shiryen bunkasa rayuwar mata da al’amuran da su ka jibinci kananan yara domin bada kariya ga masu rauni a cikin al’umma. Hajiya Hadiza Abdulwahab ta ce ma’aikatar ta samu nasarori wajen aiwatar da tanade tanaden kasafin kudin 2025, yayin da za su ci gaba da daukar matakan da su...
Daga Aminu Dalhatu Uwargidar Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta taya Uwargidar Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, murna bisa nadin ta a matsayin Yeye Asiwaju Gbogbo Ile Oodua a Ile-Ife na Jihar Osun. Nadin ya kasance wani bangare na bukukuwan cikar shekaru 10 na Mai Martaba Ooni Adeyeye Enitan Ogunwusi Ojaja II akan karagar mulki na Ooni Ife, wanda ya jawo sarakunan gargajiya, manyan jami’an gwamnati da fitattun mutane daga sassan kasar nan. A wata sanarwa da sakatariyar yada Labarai ta Uwargidar Gwamnan, Rabi Yusuf, ta fitar, ta bayyana karramawar da aka yi wa Sanata Oluremi a matsayin abin yabawa, inda ta ce karramawar ta yi daidai da jajircewarta wajen ci gaban kasa, tallafawa mata, da kuma gudummawarta...
Saurayi ya kashe budurwarsa sannan ya soya qwaqwalwarta Koda a cikin jerin masu kisan gilla, mai cin naman mutane a Rasha Dmitry Luchin ya ci ya kasance matsayin xaya daga cikin mutune mafi munin xabi’a da rashin tausayi da suke rayuwa a duniya. Xan ina da kisan, yanzu ya kasance sanannen mai laifi a Rasha saboda kashe budurwarsa da ya yi a shekarar 2018. Bayanan da suka fito game da yadda wannan lamari na rashin imani ya auku ya girgiza Gabashin Turai. Budurwarsa mai suna Budunova, wacce take da shekaru 23 kacal a lokacin, ta ziyarci saurayinta Dmitry Luchin mai shekaru 45 don yin shagalin bikin Ranar Mata ta Duniya, amma shi kuwa mugun, ba ta san cewa, yana da wata muguwar voyayyar manufa...
Majalisar Dokokin Amurka ya iso Abuja yayin da ƙasashen biyu ke ƙara matsa ƙaimi wajen tattaunawar diflomasiyya kan haɗin gwiwar tsaro da kuma zargin tauye haƙƙin addini. Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro Nuhu Ribadu, ya ce ya gana da wakilan kuma zuwan tawagar na cikin abubuwan da suka amince da shi a tasu ziyarar da suka kai birnin Washington a watan Nuwamba. “Tawagar ta ƙunshi ‘yanmajalisar wakilai Mario Díaz-Balart, Norma Torres, Scott Franklin, Juan Ciscomani, da Riley M. Moore,” in ji Ribadu cikin wata sanarwa a shafinsa na sada zumunta. Kazalika, Jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills na cikin tawagar. A cewar Ribadu, tattaunawar ta mayar da hankali kan yaƙi da ta’addanci, tabbatar da zaman lafiyar yanki...
Rahotannin da suke fitowa daga DRC sun ce fadan ya barke ne dai bayan kwanaki kadan da gwamatin DRC da ta Rwanda su ka amince da tabbatar da zaman lafiya. A can gabashin kasar an ga dubban mutane maza, mata, da kananan yara suka dauke da kayayyakinsu a lokacin da suke ficewa daga kauyukna da suke gundunar Kivu ta kudu,saboda kaucewa sabon fadan da ya barke a tsakanin sojojin kasar da na ‘yan tawayen kungiyar M23. A jiya Asabar ne sabon fadan ya barke saboda bama-baman da ake amfani da su wajen kai hare-haren a tsakanin bangarorin biyu da suke fada da juna. Wani mutum da yake gudu daga garin Luvungi ya fada wa cibiyar watsa labaru ta “Afirka Today”...
Daga Usman Muhammad Zaria Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri ta Jihar Jigawa ta yi kiyasin kashe kudade miliyan dubu 161 da milyan 336 domin gudanar da ayyukan hanyoyin mota da harkokin yau da kullum a sabuwar shekara ta 2026. Babban sakataren ma’aikatar, Malam Ahmad Isah, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin ma’aikatar a gaban kwamatin ayyuka da sufuri na majalisar dokokin jihar Jigawa. Babban Sakataren ya yi bayanin cewar, za a yi amfani da mafi yawan kudaden ne wajen gudanar da ayyukan hanyoyin mota tsakanin gariruwa da hanyoyin burji da kuma titunan cikin gari. Yana mai cewar, haka kuma za a gudanar da ayyukan hanyoyi a manyan makarantun jihar ciki har Jami’ar Sule Lamido da ke...
Hukumar Kula da Rajistar Kamfanoni (CAC) ta ba wa dukkan masu gudanar da harkar kuɗi ta PoS a fadin Najeriya, wa’adin ranar 1 ga Janairu, 2026, su yi cikakken rajista ko ta rufe su. A ranar Asabar, Hukumar ta sanar cewa yawaitar masu PoS marasa rajista a sassan ƙasar nan ya yawaita. Don haka ta jaddada cewa gudanar da PoS ba tare da rajista ba ya saɓa wa Dokar Kamfanoni ta 2020 da kuma ka’idojin Babban Bankin Najeriya (CBN). Hukumar ta kuma zargi wasu kamfanonin fasahar kudi (fintech) da daukar wakilai ba tare da rajista ba, tana bayyana wannan dabi’a a matsayin da sakaci kulawa da kuma barazana ga daidaiton tsarin kuɗi na ƙasar. Ta ce hakan na jefa miliyoyin ’yan...
Yanzu ƴan Najeriya za su iya cire naira 100,000 ta na’urar cire kuɗi ta ATM a rana, haka ma abin yake a ɓangaren cire kuɗi ta na’urar POS. A ɓangaren ma’aikatu kuma, za su iya cire kuɗi har naira miliyan biyar ne a duk mako. Wannan na ƙunshe ne a cikin sabbin tsare-tsaren da Babban Bankin Najeriya CBN ya fitar bayan garambawul da ya yi kan dokokin cire kuɗi ta na’urar ATM da POS a Najeriya. Bankin ya ce wannan sabuwar dokar za ta fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2026. A cikin wata sanarwa da daraktan tsare-tsare na bankin, Dr Rita Sike ta fitar a ranar Talata 2 ga watan Disamba, ta ce babban bankin...
Rikici kan filin kiwo tsakanin wani makiyayi da wani manomi ya yi sanadin mutuwar wani manomi mai shekaru 32 a kauyen Muva da ke cikin karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno. Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, a ranar 2 ga watan Disamba, 2025, da misalin karfe 4:00 na yamma, Alhaji Usman, wanda ke kiwon shanu, ya samu rashin jituwa da Jauro Ishaya mai shekaru 43, kan rikicin filin kiwo. A cewar majiyar, yayin takaddamar ne aka zargi Jauro Ishaya da harba bindigar gida wadda ta sami Alhaji Usman a ciki, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa. An garzaya da wanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Askira, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarsa nan take. Rundunar ’yan sandan...
Kakakin Majalisar Dokokin jihar Ribas, Martin Amaewhule tare da mambobin majalisar su 15 sun sanar da sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Amaewhule ya bayyana shawarar ’yan majalisar ne a zaman majalisa na ranar Juma’a, inda ya ce akwai abin da ya kira “rarrabuwar kai a fili” a cikin PDP wanda ya sa suka yanke wannan shawara. Muna tafe da karin bayanai…
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ce ba zai bai wa ’yan Najeriya kunya ba, saboda ƙwarin guiwar da suke da shi a kansa. Musa, wanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa ministan tsaro, ya bayyana haka ne a ranar Laraba lokacin da aka tantance shi a Majalisar Dattawa. Tsaro: Gwamnonin Arewa na shirin dakatar da haƙar ma’adinai Ƙudirin dokar hukuncin kisa ga masu satar mutane ya tsallake karatu na biyu Ya gode wa Shugaban Ƙasa saboda zaɓarsa da ya yi a matsayin minista, sannan ya gode wa ’yan Najeriya saboda amincewa da suka yi da shi. Ya yi alƙawarin yin iya bakin ƙoƙarinsa domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar nan. Ya ce: “Da na ga irin martanin...
Wata gobara ta tashi a ranar Laraba ta ƙone kasuwar katako da ke kusa da Jabi Masallaci a Abuja. Gobarar ta lalata kaya da kayan gini na miliyoyin kuɗi, amma ba a yi asarar rai ba. CBN ya kara yawan kudin da mutum zai iya cirewa a mako zuwa N500,000 Gobara ta kashe mata da miji da ’ya’yansu 3 a Katsina Kawo yanzu dak ba a san musababbin tashin gobarar ba. Sai dai wasu rahotanni na cewa gobarar na iya farawa ne sakamakon matsalar wutar lantarki, wanda wani lokacin wayoyin wuta na faɗowa kan rumfunan kasuwa. ’Yan kasuwa da mazauna yankin sun yi ƙoƙarin kashe wutar, amma ta yaɗo cikin sauri saboda katako da sauran kayayyakin gini na da saurin...
Daga Ali Muhammad Rabi’u An samu mummunan rikici tsakanin mambobin ƙungiyoyin asiri wanda ya shafi tsofaffin daliban kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kwara da ke Ilorin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya. Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa dalibin mai suna Oyelade Olawale wanda ya karanci aikin Injiniya a fannin Gine-gine, ya rasu ne a yayin wannan rikici na kungiyoyin asiri. An samu labarin cewa an kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da hannu a tarzomar da ta faru a Kwalejin. A cikin wata sanarwa, Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Kwalejin, Halima Garba, ta tabbatar da mutuwar matashin da kuma kama wasu mutane da ake zargi da hannu a rikicin. Sanarwar ta yi kira ga dalibai da al’umma...
Wata sabuwar badakala ta sake bata sunan kungiyar Tarayyar Turai, inda ‘yan sanda suka farmawa gidan toshuwar shugaban kula da manufofin harkokin wajen na kungiyar Federica Mogherini, tare da tsare ta a ranar Talata, a Belgium. Mogherini wacce ta yi aiki a mukamin tun daga 2014 zuwa 2019, Ita da wasu abokan aikinta biyu ana binciken su kan yadda aka yi amfani da kudaden Tarayyar Turai ba bisa ka’ida ba, cin hanci da rashawa. Federica Mogherini, jami’ar diflomasiyya ‘yar Italiya mai shekaru 52, ana tsare da ita tare da Stefano Sannino, babban jami’i a Hukumar da kuma mataimakin darakta na Kwalejin Turai. An kama su, su ukun a wani bangare na binciken da Ofishin Mai Gabatar da Kara na Tarayyar...
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Shugaban Amurka Donald Trump na cire Pretoria daga taron G20 na shekara mai zuwa, yana mai sake tabbatar da matsayin Afirka ta Kudu na memba da aka kafa wannan dandali na kasa da kasa tare da ita. Trump ya sanar a ranar Laraba da ta gabata cewa ba za a gayyaci Afirka ta Kudu zuwa taron G20 na 2026 a Florida ba, yana mai ambaton zargin da ake yi wa kasar na kin mika shugabancin G20 ga wakilin ofishin jakadancin Amurka a bikin rufe taron da aka yi a kasar a baya. Duk da haka, Pretoria ta dage cewa shugabancin da ake yi nak aba-karba an mika shi ga...
’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 13 da suka gabata a Jihar Borno. Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren da suka ɓace tuna shakarar 2012, waɗanda suka haɗa da sarƙoƙi da sulallan zinariya a yankin Ƙaramar Hukumar Abadam. Jami’an Ƙaramar Hukumar ne suka sanar a ranar Asabar a Malam Fatori cewa tsabar zinaren da aka gano, darajarsu ta kai Naira miliyan 23, mallakin wata uwa ce mai ’ya’ya shida. Matar, wacce ke zaune a gaɓar Tafkin Chadi, ta ce, “A yau ina cike da farin ciki game...
’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinwu ta kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 12 da suka gabata a Jihar Borno. Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren waɗanda suka haɗa da sarƙoƙi da sulallan zinariya a yankin Ƙaramar Hukumar Abadam. Jami’an Ƙaramar Hukumar ne suka sanar a ranar Asabar a Malam Fatori cewa tsabar zinaren da aka gano, darajarsu ta kai Naira miliyan 23, mallakin wata uwa ce mai ’ya’ya shida. Matar, wacce ke zaune a gaɓar Tafkin Chadi, ta ce, “A yau ina cike da farin ciki game da gano tsabar zinare na masu...
An yi gangami a fadin duniya domin nuna goyan baya ga al’ummar Falasdinu a daidai lokacin da aka gudanar da bikin ranar Falasdinu a ranar 29 ga watan Nuwamba da MDD ta kebe. A faransa a gudanar da irin wannan gangamin, inda suka yi Allah wadai da mamayar da gwamnatin Isra’ila ta yi wa Gaza da Yammacin Kogin Jordan, tare da bayyana goyon bayansu ga adawar Falasdinu. Baya ga Faransa, Birtaniya, Jordan, Kuwait, Slovenia, Sweden, da Morocco an shirya zanga-zangar goyon bayan Falasdinu. Masu zanga-zangar sun yi Allah wadai da mamayar Isra’ila, ayyukan matsugunan Yahudawa a Yammacin Kogin Jordan, korarsu, da kuma kisan kiyashin Falasdinawa a Gaza da kuma cin zarafin fararen hula. Daga cikin taken da aka yi da...
Babban Bankin Nijeriya CBN, ya sake bayar da wani dauki a Kasuwar hada-hadar musayar kudade, da nufin samar da sauki wajen samun kudade a cikin kasar. Hakan ya sanya Bankin, ya sayar da dala miliyan hamsin, ga dilolin da aka yarjewa yin hada-hadar musayar kudade a cikin kasar. Kazalika, Bankin ya yi hakan ne, domin samar da daidaito, wajen yin hada-hadar musayar kudaden Naira dai, ta fara fuskantar tarnaki ne, biyo bayan samun raguwarta a kasuwar hada-hadar musayar kudade, inda kuma bukatar dalar, ya kara karuwa. Tun bayan da Naira ta samu farfadowa, Bankin na CBN, ya samu sauki kan hada-hadar musayar kudaden da aka yi. Sai dai, Bankin na CBN ya tura dala miliyan hamsin musamman domin dillalen da...
Dubban mutane sun taru a Jihar Bauchi, don halartar jana’izar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa. Gwamnatin Jihar Bauchi, ta ayyana ranar Juma’a a matsayin ranar hutu domin ba jama’a damar halartar jana’izar malamin. Trump zai haramta wa ’yan Najeriya da wasu ƙasashe zuwa Amurka CAF Tayi Watsi Da Alƙalan Wasan Nijeriya a Kofin Afrika Na 2025 Ɗalibansa da sauran Musulmi daga Bauchi da maƙwabtan jihohi sun isa da wuri domin halartar jana’izar. Huumomi sun tsaurara matakai a jihar don tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali. Maulud Dahiru Bauchi, wanda ya yi magana a madadin iyalan marigayin, ya ce za a yi jana’izar malamin...
Gammayar ministocin harokin wajen kungiyar tarayyar Turai sun fitar da wata sanarwa da aciki suka soki hare haren da yahudawa yan share wuri zauna suke kai wa falasdinawa a gabar yammacin kogin Jodan da isra’ila ta mamaye kuma yake kara ci gaba fiye da kowanne lokaci a baya, Sanarwar ta fito ne daga minsitocin kasashen birtaniya, jamus , faransa da kuma italiya inda manyan jami’an diplomsiyarsu suka bayyana hare-haren a matsayin mataki ne na tada fitina da kuma ta’addanci. Haka zalika sun yi kira ga fira ministan isra’ila Benjamin na tanyaho da yayi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansa karakshin dokokin kasa da kasa, kuma ya kiyaye hakkin falasdinwa dake zaune a bangarorin da aka mamaye. Daga karshe...
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana jimaminsa kan rasuwar babban malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi, lamarin da ya ce ya kaɗu matuƙa da ya samu labarin. Tinubu ya ce jagoran na ɗarikar Tijjaniya mutum ne mai daraja da ƙima, sannan ya bayyana shi a matsayin madubi wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa. Rasuwarsa za ta ba babban giɓi a Najeriya,” in ji shugaban. Shi ma Tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana rasuwar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi a matsayin rashi babba ga al’ummar Musulmi na Najeriya da ma Afirka baki ɗaya. A wata sanarwa da Atiku ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, ya bayyana marigayin da babban malami wanda ya koyar da addini...
Kasashen Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi Allah wadai da “karuwar yawan tashin hankalin” da yahudawa ‘yan gudun kama wuri zaman ke yi wa fararen hular Falasdinawa, tare da yin kira ga Isra’ila da ta kare al’ummar Yammacin Kogin Jordan. “Wadannan hare-haren dole ne a daina su. Suna kawo cikas ga kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya da kuma tabbatar da tsaron Isra’ila mai dorewa,” in ji ministocin harkokin waje na kasashen hudu a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa. Sun kuma yi maraba da ” bayyanannar adawar” da shugaban Amurka Donald Trump ya nuna kan yunkurin mamaye Yammacin Kogin Jordan kuma sun sake nanata adawarsu “ga duk wani nau’in mamayewa, ko na bangare, ko na...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kaduwa da rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Fitaccen malamin ya rasu a Bauchi ranar Alhamis yana da shekaru 101. Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka A cikin wata sanarwa da Kakakin shugaban, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin jagoran da ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa, wa’azi da jagorantar al’ummar Musulmi. Tinubu ya ce rasuwar malamin ba wai asara ce ga iyalansa da almajiransa kawai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya. “Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba ne kuma murya ce ta daidaito...
Daga Bello Wakili Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya karɓi labarin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi cikin alhini da jimami. Fitaccen malamin da ke Bauchi ya rasu ne a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2026, yana da shekaru 101. Shugaban Ƙasan ya yi jimamin rasuwar jagoran Darikar Tijjaniyya, yana bayyana shi a matsayin ginshiƙin ɗabi’a wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa da wa’azi. Shugaba Tinubu ya ce rashinsa babban rashi ne ba ga iyalansa da dimbin mabiyansa kaɗai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya. Shugaban Ƙasa ya tuna da albarka da goyon bayan da ya samu daga marigayi Sheikh Dahiru Bauchi a lokacin yakin zaɓen 2023. “Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba, mai cike da natsuwa da hikima....
Daga Bello Wakili Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya karɓi labarin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi cikin alhini da jimami. Fitaccen malamin da ke Bauchi ya rasu ne a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2026, yana da shekaru 101. Shugaban Ƙasan ya yi jimamin rasuwar jagoran Darikar Tijjaniyya, yana bayyana shi a matsayin ginshiƙin ɗabi’a wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa da wa’azi. Shugaba Tinubu ya ce rashinsa babban rashi ne ba ga iyalansa da dimbin mabiyansa kaɗai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya. Shugaban Ƙasa ya tuna da albarka da goyon bayan da ya samu daga marigayi Sheikh Dahiru Bauchi a lokacin yakin zaɓen 2023. “Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba, mai cike da natsuwa da hikima....
Daga Sani Sulaiman Gwamnan Jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas, ya yi jimami kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2025, yana da shekaru 102. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Mista Emmanuel Bello, ya sanyawa hannu. Gwamnan ya ce rasuwar wannan babban malami babban rashi ne ga kasa, yana mai nuna cewa a wannan lokaci ne ake matuƙar bukatar irin gudummawar da yake bayarwa, duba da kalubalen da kasar ke fusfuskanta. Ya kara da cewa marigayi Sheikh ya koyar da ilimi da zai ci gaba da jagorantar kasa kan...
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi, a matsayin babban rashi ga al’umma. Gwamnan ya bayyana malamin a matsayin jagoran haɗin kai, zaman lafiya, da fahimtar juna tsakanin Musulmi da mabiya addinai daban-daban. ’Yan sanda sun gano harsasai 210 a kan titin Zariya-Funtuwa Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa A cikin saƙon ta’aziyya da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya sanya wa hannu, gwamnan ya ce Gwamnatin Jihar Bauchi tana alhinin rasuwar malamin. Dahiru Bauchi, ya rasu da safiyar ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamba, 2025 a Bauchi, yana da shekara 102. Gwamnan, ya ce Sheikh Dahiru Bauchi babban malami ne na addinin...
Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta bukaci maniyyatan aikin hajjin 2026 da su gaggauta biyan kudin kujerun su kafin ranar 24 ga watan gobe. Darekta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taro da shugabannin sassa na hukumar da shugabannin shiyya da sauran ma’aikatan hukumar a Dutse babban birnin jihar. Yana mai cewar, hukumar aikin hajji ta kasa wato NAHCON ta bayyana ranar 5 ga watan Disamba da ta kayyade a matsayin ranar rufe biyan kudin kujerun aikin Hajjin 2026 a fadin kasar nan. Ya bayyana cewar ranar itace ranar karshe da hukumar aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta kayyade na biyan kudin kujerun...
Daga Salihu Tsibiri Tsohon shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana tabarbarewar tsaro da ake fuskanta, wato ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma hare-haren ’yan bindiga, a matsayin barazana ga siyasar ƙasar nan gabanin zaɓen 2027. Ya yi wannan tsokacin ne a jawabinsa yayin bude zaman taron musamman na yini biyu da Majalisar Wakilai ta shirya kan halin tsaro da ƙasar ke ciki. Alhassan Ado Doguwa, wanda ya yaba da ayyukan da hukumomin tsaro ke ci gaba da gudanarwa, ya ce halin da Arewa ke ciki abin takaici ne ƙwarai, la’akari da yawan mutanen da ke hannun masu garkuwa da kuma waɗanda ke rayuwa cikin tsananin rashin tabbas. Tsohon shugaban ya jaddada cewa duk da cewa...
Shugaban Iran ya sanar da cewa gwamnati na aiki don inganta juriya da ingancin tattalin arzikin kasar. Masoud Pezeshkian, Shugaban Iran, ya yi jawabi a taron Kasuwar Jarin Iran na shekara-shekara mai taken “Juriya, Kirkire-kirkire, Ci gaba,” yana mai jaddada gyare-gyaren manufofin tattalin arziki, kula da albarkatu, da kuma tallafawa masu zuba jari. Ya bayyana cewa gwamnati na aiki don rage cikas ga samar da kayayyaki da ciniki. Pezeshkian ya nuna muhimmancin yin tarurruka na wata-wata tare da masu zuba jari da masu samar da kayayyaki don nemo hanyoyin magance matsalolin da ake fuskanta. Ya kara da cewa, “Tanadin kashi 10% na iya adana ganga 800,000 zuwa 900,000 na mai a kowace rana.” Ya kuma nuna cewa samar da wutar...
Pars Today – Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, yana mai jaddada muhimmancin Pakistan a yankin, ya ce haɗin gwiwa tsakanin Tehran da Islamabad a fannoni daban-daban yana taimakawa wajen kawo kwanciyar hankali da zaman lafiya a yankin Ali Larijani, Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, ya ce da sanyin safiyar Talata da ya isa Islamabad cewa Pakistan muhimmiyar ƙasa ce a yankin kuma tana da matsayi mai kyau wajen tasiri ga yanayin tsaro na yankin. A cewar Pars Today, ya ƙara da cewa a matsayinta na maƙwabciyar gabas ta Iran, Pakistan ma tana taka rawa a al’adu, kuma dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu ta daɗe tana da zurfi kuma ta tarihi. Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Jamhuriyar Musulunci...
Babbar Mai Shari’ar ta kasa , Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta jaddada cewa alkalai suna da nauyin tabbatar da adalci cikin gaskiya da daidaito a lokacin da matsalolin tattalin arziki ke kara tsananta wa al’umma. Ta bayyana haka ne a Taron Alkalai na Shekara-shekara Karo na 26, wanda Cibiyar Nazarin Shari’ar Musulunci ta Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) ta shirya tare da haɗin gwiwar Cibiyar Koyar da Ayyukan Shari’a ta Kasa (NJI), a harabar Jami’ar da ke Kongo, Zariya. Mai Shari’a Kekere-Ekun, wadda Sakatare na NJI, Barista Abdulazeez Aluwo ya wakilta, ta ce dole ne kotuna su yi hukunci da ke la’akari da yanayin tattalin arziki da kuma hakkokin masu nema da wadanda ake binsu hukunci. Ta ce hakan ne kadai...
Kakakin kungiyar Hamas yayi Tir da ci gaba da kai hare haren da Isra’ila ke yi a fadin yankin Gaza, yayi gargadin cewa wadannan matakai suna barazana sosai ga yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma tsakaninta da Isra’ila a kasar masar a watan Jiya. A cikin wani bayani da Hazem qassem yayi gargadin cewa ci gaba da wuce gona da irin Isra’ila zai kai ga rusa yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakaninta da Isra’ila , kungiyar ta jaddada matsayinta na aiki da yarjejeniyar duk da ci gaba da keta ta da isra’ila ke yi. A wani bangare kuma akalla falasdinwa 4 ne suka yi shahada yayin da wasu da dama kuma suka jikkata a yankin Gaza . sakamakon...
Kungiyoyi da kasashe masu gwagwarmaya a yammacin Asiya sun yi allawadai da hare-haren da HKI ta kai unguwar Dhahiya Junubiyya na birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon a jiya Lahadi da yamma wanda ya kai ga shahadar mutane 5 da kuma raunata wasu 28. Daga cikin wadanda suka yi shahada har da babban kwamandan kungiyar Hizbullah Shahid Ali Tabatabai. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyoyi da kasashen da suka yi allawadai da hare-haren kamar haka. Akwain kungiyoyin Falasdinawa masu gwagwarmaya wadanda suka hada da Hamas, Jihadul Islami, PFLP, kungiyar falasdinawa masu gwagwarmaya (PMM), Ansarullah mai gwagwarmaya. Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen JMI da kungiyoyi masu gwagwarmaya a kasar Iraki duk sun yi allawadai da hare-haren sun...
Shuwagabannin kasashen duniya a kungiyar G20 sun gabatar da jawabin bayan taro da kuma matsayin kungiyar a cikin al-amura da dama a duniya, duk tare da kauracewa taron wanda shugaban kasar Amurka Donal Trump yayi. Shafin yanar gizo na labarai AfricaNews ya nakalto shugaban afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa yana gabatar da jawabi bayan taron shuwagabannin na G20 na kwanaki 2. Ramanposa yace kungiyar G20 ba zata taba manta da sauyin yanayi ba, kuma ba zata kyala sauran kasashen duniyaba ba, kuma kungiyar zata yi kokarin ganin ta daga sauran kasashe raunan a duniya zuwa matsayin da ya dace na tattalin arziki. Kakakin Ramanposa ya ce dukkan kasashen da suka halarci taron sun amince da jawabin bayan taron. Amma shugaban...
Wata gobara ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Mafa da Jihar Borno ta lalata matsugunan wucin gadi guda 40 tare da kayan abinci da sauran kayan gida. Kamar yadda rahoton ke nunawa cewar, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:20 na safiyar Laraba. An tuntuɓi hukumar kashe gobara ta tarayya da ta Jiha nan take, yayin da ƙungiyoyin sintiri ƙarƙashin jagorancin DPO na Mafa suka taimaka wajen daƙile cunkoson jama’a da kuma hana satar kayayyaki. Daga ƙarshe rahoton da ke garin na nuna cewar an kashe gobarar ba tare da an samu rahoton raunuka ko asarar rayuka ba. Har yanzu ba a tantance adadin kadarorin da suka lalace ba, kuma ana ci gaba da bincike kan musabbabin...
A ranar Alhamis da ta gabata ce karamin kwamiti mai kula da al-amuran nahiyar afirka a majalisar dokokin kasar Amurka ya bude tattaunawa dangane da zargin da shugaban kasar Donal Trump yake yin a cewa ana kashe kiristoci a tarayyar Najeriya fiye da duk wata kasa a duniya. Wanda hakan ya say a yi barazanar daukar matakan soje idan akwai bukatar haka don kawo karshen kissan. Jaridar Premium times ta nakalto Chris Smith dan majalisan da ya jagoranci taron yana fadar cewa zargin Trump gaskiya ne kuma shi a karan kansa ya kai ziyara tarayyar Najeriya har sau uku a baya inda sakamakon ya tabbatar da hakan. Sannan Bishop Wilfred Anagbe daga jihar Benue wanda ya halarci taron ta kafar...
Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta yaba wa jihohin Kano, Katsina da Jigawa kan manyan ci gaba da suka samu a fannin walwalar yara, tana gargadin cewa har yanzu akwai aikace-aikacen da dama da ya rage a yi. A yayin ƙaddamar da rahoton Nigerian Child 2025 a Kano, Shugaban Ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihhood Mohammed Farah, ya ce jihohin Kano, Katsina da Jigawa sun samu gagarumin ci gaba a fannonin lafiya, abinci mai gina jiki, ilimi da samar da ruwan sha mai tsafta ta hanyar haɗin gwiwar hukumar da gwamnatocin jihohin. Daga cikin nasarorin da Farah ya ambata akwai Masaki Initiative a Jihar Jigawa, wani shiri da al’umma ke jagoranta...
Iyalan Waɗanda Aka Kashe Yayin Zanga-zangar Bangladesh Sun Yi Maraba Da hukuncin Kisan Tsohuwar Firaminstar
Iyalai da ‘yan uwan wadanda aka kashe a lokacin zanga-zangar da ta kawo karshen gwamnatin tsohuwar Firaminstar Bangaledash Sheikh Hasina a bara, sun yi maraba da hukuncin kisa da wata kotun birnin Dhaka ta yanke mata. An samu Sheikh Hasina da laifin cin zarafin bil adama tare da ba ‘yan sanda umurnin kashe masu zanga-zanga, inda aka yanke mata hukuncin a bayan idonta. Gwamnatin Bangaledash ta bukaci Indiya da ta tasa keyar Hasina da ke gudun hijira a can domin ta fuskanci hukuncin. Wakiliyar BBC ta ce Hukumomin Indiya na cewa suna ci gaba da bibiyar lamarin tsakanin Sheikh Hasina da mahukuntan Bangaledash kuma hakan na nufin Indiya na neman wata hanyar diflomasiyya akan lamarin. BBC
Mutum uku da wani yaron babbar motar kaya sun rasa ransu bayan wayar wutar lantarki kashe su a lokacin wani bikin nadin sarauta a unguwar Idimu da ke Ƙaramar Hukumar Alimosho ta jihar Legas, bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne ranar Talata, 11 ga watan Nuwamba, kuma an gano cewa yaron motar, wanda ba a tantance sunansa ba tukuna, ya mutu nan take a wurin. Najeriya ta ɗora alhakin taɓarɓarewar harkokin tsaronta kan Amurka Babu addinin da ake yi wa kisan ƙare dangi a Binuwai — Gwamna Alia Rahotanni sun ce wani mazaunin unguwar da aka karrama da sarauta ne ya shirya taron cashiyar a titin Anjorin domin murnar nadin. Sai dai yayin da ake tsaka da bikin,...
Gwamnatin Tarayya ta ɗora alhakin dawowar hare-haren ta’addanci, ciki har da sace dalibai mata a jihar Kebbi da kai hari a coci a jihar Kwara, kan kalaman da Amurka ta yi kwanan nan a kan Najeriya. Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya ce sakonnin da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa, inda ya zargi Najeriya da “kisan kiyasin Kiristoci” tare da barazanar tura sojojin kasarsa, sun kara wa wasu ƙungiyoyin ’yan ta’adda kaimin kai hare-hare. Babu addinin da ake yi wa kisan ƙare dangi a Binuwai — Gwamna Alia Yadda maganin sauro ya yi ajalin magidanci da iyalinsa a Kano “Kalaman da Amurka ta yi kwanan nan sun kara wa wasu ƙungiyoyin masu tayar da kayar baya da ke son...
a Rahotanni sun nuna cewa kungiyar gwagwarmaya Ta hamas ta yi gargadi game karuwar hadari bayan mutuwar falasdinawa guda 28 sakamakon harin da sojojin HKI suka kai a yankin Gaza, da hakan yake kara lalata yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a tsakani. Akwai yara guda 9 daga cikin wanda harin na isra’ila ya kashe a harin na jiya laraba, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta yankin gaza ta bayyana bayan mutane akalla 77 da suka jikkata, Hamas ta karyata zargin cewa dakarunta ne suka fara bude wa sojojin Isra’ila wuta da ya kai ga sun kai harin, kungiyar ta bayyana zargin a matsayin shaci fadi, kuma isra’ila tana son fakewa da shi ne don kare hare haren da...
An sanar da dan wasan Paris St Germain, Achraf Hakimi a matsayin wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2025, mai tsaron baya da ya lashe kyautar karon farko bayan shekara 52. Dan wasan tawagar Masar Mohamed Salah shi ne na biyu mai taka leda a Liverpool da kuma Victor Osimhen na Super Eagles mai wasa a Galatasaray a mataki na uku. Mai tsaron bayan Morocco ya karbi kyautar sakamakon nasarorin da ya samu a 2025 tare da Paris St Geramin ciki har da lashe Champions League da Ligue 1 da Coupe de France da kuma UEFA Super Cup. Shi ne na farko daga Morocco da ya karbi kyautar tun bayan Mustapha Hadji a 1998, kuma...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mata da dama da aka yi garkuwa da su na shiga wani irin mawuyacin hali yayin da suke hannun wadanda suka sace su, suna fuskantar rayuwar kaskanci, da cin zarafi, da muzgunawa da wasu irin yanayi wanda sai ka tausaya musu. Irin wadannan mata a wasu lokutan basa tsira da rayukansu, a wasu lokutan kuma ko sun tsira, sukan shiga halin ciwon damuwa wanda ke daidaita musu rayuwa, a wasu lokutan ma har sai sun ji kamar su dauki rayuwar su. NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Shirin Najeriya A Yau na...
Tauraron ƙwallon ƙafar ƙungiyar PSG da ƙasar Morocco, Achraf Hakimi, ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana.
Fitaccen ɗan wasan gaba na Najeriya da ke taka leda a ƙungiyar Galatasaray ta Turkiyya, Victor Osimhen, ba zai halarci bikin karrama gwarazan ‘yan wasan Afirka na 2025 ba. Osimhen, wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Afirka a 2023, ya bayyana cewa ya koma Turkiyya ne domin duba lafiyarsa, bayan raunin da ya samu a wasan da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta doke Najeriya. Tankin ruwa ya kashe mutum 4, wasu sun jikkata a Jigawa An yanke wa shugaban ISWAP hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari A yau Laraba ne Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) za ta sanar da sunayen gwarazan ‘yan wasan nahiyar na shekarar 2025, a yayin babban bikin da za a gudanar a Morocco. Za...
An yanke wa abokan aikin ɗan tsohon shugaban kasar Gabon hukuncin ɗauri a gidan kurkuku Kotun Hukunta Laifuka ta Musamman da ke Gabon ta yanke hukuncin ɗauri a gidan kurkuku daga watanni 26 zuwa shekaru 15 ga tawagar abokan Nouruddine Bongo, ɗan tsohon shugaban ƙasa Ali Bongo, a shari’ar da aka fi sani da “Tawagar Matasa”, wacce ke da alaƙa da zarge-zargen cin hanci da rashawa da kuma satar dukiyar gwamnati. Bayan dogayen zaman shari’o’i da aka kammala a safiyar ranar 18 ga Nuwamba, 2025, kotun ta yanke wa Iyan Ghislain Ngolo, tsohon darektan ofishin Nouruddine Bongo, hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan yari, tare da dakatar da shekaru biyar, bisa tuhume-tuhumen da suka haɗa da satar dukiyar jama’a, cin...
Shugaban ƙungiyar masu sayar da tsofaffin ƙarafa a jihar Gombe, A.A. Laja, ya ce gobarar da ta tashi a kasuwar tsofaffin ƙarafa da ke kasuwar katakon jihar ta jawo masa asara da ta kai sama da Naira miliyan 500. Lamarin ya faru ne a daren Laraba, inda wutar ta ƙone shaguna fiye da 30 da ke ɗauke da kayan kasuwancinsa. Sanatan Enugu ya mutu a Birtaniya ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’ A.A Laja, wanda ya yi magana da wakilinmu jim kaɗan bayan aukuwar lamarin, ya ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 10 na dare, ta kuma ci gaba da ci har zuwa karfe 4:00 na Asuba, saboda rashin isowar jami’an kashe gobara cikin...
Wata mummunar gobara ta tashi cikin daren Laraba ta ƙone shaguna a kasuwar Katako da ke Gombe, lamarin da ya yi sanadin salwantar dukiya ta miliyoyin naira. Shaidu sun ce gobarar ta fara ne wajen misalin ƙarfe 1:00 na dare sakamakon zargin matsalar wutar lantarki, inda ake kyautata zato cewa an bar wasu na’urorin lantarki ne a kunne bayan an rufe kasuwar. DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Amurka za ta binciki zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya ranar Alhamis Hakan a cewar shaidun ya haddasa tashin gobarar bayan wutar lantarki ta dawo. Gobarar dai ta ci gaba da ƙone shaguna da kadarori iri-iri, lamarin da ya jefa ’yan...
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa dole ne kudirin Amurka da MDD ta amince da shi ya tabbatar da kare hakki da yancin Falasdinawa a sahun gaba samar da kasar Falasdinu. Jakadan Iran kuma wakilin dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeed Iraqini, ne ya bayyana haka, a matsayin martanin ga amincewar da kwamitin Tsaro ya yi da daftarin kudirin Shugaba Donald Trump na Amurka game da Gaza. Iran ta yi gargadi akan amfani da wannan kuduri a hanyar da za ta keta ko ta wargaza hakkokin al’ummar Falasdinawa ba, musamman ‘yancin cin gashin kai da kuma kafa kasar Falasdinawa mai cin gashin kanta. A Kudurin da aka amince dashi jiya Litinin, Iran ta jaddada damuwar da wasu membobin...
Hukumar ƙwallon ƙafar Afirka CAF, ta bayyana cewa bayan tankade da rairaya da ta yi, a yanzu ’yan wasa uku kacal ne suka rage a takarar gwarzon nahiyyar na bana. A wata sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana Achraf Hakimi da Mohamed Salah da Victor Osimhen, a matsayin sauran ukun da suka rage a takarar gwarzon dan ƙwallon ƙafar Afirka na bana. Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno Hakimi, kyaftin din Morocco, ya lashe kofuna daga ciki har da Champions League a PSG — na farko a tarihin ƙungiyar — da Ligue 1, da European Super Cup, da kuma kai wa zagayen ƙarshe...
A yau ne aka bude taron tattaunawa game da wayewar kai takanin Sin da kasashen Larabawa karo na 11, wanda sashen cudanya da kasashen waje na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin da sakatariyar kawancen kasashen Larabawa suka dauki nauyin shiryawa a Beijing. A gun taron, shugabanni na jam’iyyu da kungiyoyin siyasa, ‘yan majalisa, jami’an gwamnati, da wakilan masana da kafofin watsa labarai daga Sin da kasashen Larabawa guda 22 sun hallara don inganta ilmantarwa da fahimtar juna kan wayewar kai da kuma zurfafa hadin gwiwar abokantaka. A wannan taron kuma, Sin da kasashen Larabawa za su mayar da hankali kan batutuwa kamar “Musayar darussan mulkin kasa da binciken hanyoyin zamanantarwa tsakanin Sin da kasashen Larabawa”, da “Shawarwarin wayewar kan...
Rushewar ramukan hako ma’adinai ta kashe ma’aikata 32 a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Akalla ma’aikatan hakar ma’adinai 32 ne suka mutu a ranar Asabar sakamakon zaftarewar ƙasa a wani ma’adinan cobalt a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, yayin da ake ci gaba da neman waɗanda har yanzu ba a same su ba a yankin. Zaftarewar ƙasa ta faru ne a wurin Kalandu da ke cikin ma’adinan Mulundu kusa da Kolwezi, wani wuri da kamfanin Bajiklem ke gudanar da shi a hukumance. Ministan harkokin cikin gida na lardin, Rui Kawumba Mayondi, ya ce “masu hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba sun kai hari kan wurin duk da haramcin da aka sanya saboda ruwan sama mai ƙarfi da kuma haɗarin zaftarewar ƙasa,” ya...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi November 17, 2025 Manyan Labarai Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka November 17, 2025 Manyan Labarai Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda November 17, 2025
Sheikh Ahmad Gumi ya yi martani kan kiraye-kirayen da ake yi na kama shi, inda ya ce masu yin kiran na yi ne domin kawar da rawar da yake takawa wajen magance matsalar ’yan bindiga a Arewa. Gumi, ya ce duk ganawar da yake yi da ’yan bindiga yana yi ne domin samar da zaman lafiya, kuma hukumomin tsaro sun san da komai. Ɗan Najeriya ya kashe mahaifinsa, ya yanki ƙannensa da wuƙa a Amurka Tsaro: Na kan yi kuka duk lokacin da na ji an kashe wani — Akpabio Maganar ta sake fitowa fili ne bayan da ya sake jaddada cewa tattaunawa hanya ce da za ta iya kawo ƙarshen tashin hankali a karkara. A cikin dogon saƙon da ya...
Da yake magana da manema labarai, Ahmed ya ce ficewar ba za ta raunana jam’iyyar ba, amma dai, ya yi fatan alheri ga ‘yan jam’iyyar da suka fice. Ahmed ya ƙara da cewa, NNPP tana da ƙwarin gwiwar riƙe Kano da kuma lasheh kujera a Jigawa, Kaduna, da sauran jihohi. Ya kuma yi ikirarin cewa, an ƙwace nasarar da jam’iyyar ta samu ne a Taraba a zaben da ya gabata wanda ke nuna yiwuwar samun nasara a shekarar 2027. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Nazari Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna? November 16, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Da Ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Mutane 7 November 15, 2025 Manyan Labarai Sanusi...
Iran ta yi gargadin cewa tsanantar ayyukan sojojin Amurka a yankin Caribbean da Latin Amurka na haifar da babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro na duniya, kuma ta yi kira da a girmama hurumi da cikakken yancin Venezuela. A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghai, ya ce barazanar Amurka na amfani da karfi kan zababiyar gwamnatin Venezuela ya saba wa dokokin kasa da kasa. Ya kuma bayyana cewa irin wadannan ayyuka tamkar keta ka’idojin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, musamman haramta amfani da karfi. A daya bangaren kuma, M. Baghai ya yi Allah wadai da hare-haren da Amurka ke kai wa jiragen kamun kifi na Venezuela a matsayin misalai na kisan gilla ba...
An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Yi Taka-tsantsan Da Batun Yankin Taiwan November 15, 2025 Daga Birnin Sin Jakadan Sin A Japan Ya Bayyana Matukar Adawa Da Kalaman Firaminista Takaichi Dangane Da Kasar Sin November 15, 2025 Daga Birnin Sin Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya November 14, 2025
Kyaftin ɗin tawagar ƴan wasa matan Nijeriya ƴan ƙasa da shekara 17 (Flamingos), Shakirat Moshood, na cikin jerin ƴan wasa uku da suka kai matakin ƙarshe domin lashe ƙyautar Matashiyar Ƴar Wasan CAF ta 2025. Sauran ƴan wasan da ke fafatawa da ita su ne Moha El Madani daga Morocco da Adji Ndiye ta Senegal. Moshood ta yi fice a manyan wasanninta a gasar cin kofin Duniya na mata ƴan ƙasa da shekara 17 ta FIFA a 2025, ko da yake tawagar da Bankole Olowookere ke jagoranta ta tsaya a zagaye na 16. A duk tsawon gasar, ta kasance ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasan da suka yi ƙwazo a tawagar da kyakkyawan salon wasa. Wasu Mahara Sun Kashe Mata...
Kungiyar Editocin Nijeriya (NGE) ta yi gargadi cewa yanayin da tattalin arzikin da kasar nan ke ciki ya jefa kafofin yada labarai cikin wani mawuyacin hali. Kungiyar ta kuma yi kira da a soke dokokin da ke takura ‘yancin ‘yan jarida. Shugaban NGE, Mista Eze Anaba, ya bayyana haka ne a jawabin maraba da ya yi a Taron Editocin Nijeriya Gabadaya (ANEC) mai taken “Dimokuradiyya, Gudanarwa da Hadin Kan Kasa: Rawar da Editoci ke Takawa,” wanda aka gudanar a dakin taro na Tarayya, Abuja. Ya yi nanata cewa halin tattalin arziki a kasar ya tilasta wasu gidajen jarida rufewa, yayin da wasu da ke kokarin ci gaba da aiki ba sa iya biyan albashin ma’aikata. A cewarsa, wannan lamari ne...
A wani sabon yunƙuri na inganta haƙƙin yara da walwalarsu, Hukumar kula da kananan yara ta MDD wato UNICEF tare da haɗin gwiwar Hukumar Wayarda kan jama’a da ta Ƙasa (NOA) da Hukumar kidayar Jama’a ta kasa (NPC), da Hukumar Kula da katin zama dan Ƙasa (NIMC), sun kaddamar da shirin wayar da kai na yini guda kan muhimmancin rijistar haihuwa ga sabbin jarirai a duk faɗin Yankin Gwarzo na Jihar Kano. Wannan wani ɓangare ne na shirye-shiryen gwamnati da UNICEF ke tallafawa, domin ƙarfafa tsarin kare yara da kuma tabbatar da samun damar yin amfani da muhimman aikace-aikacen zamantakewa, musamman a yankunan karkara na jihar. Wakilin NPC, Malam Abubakar Lawal, ya jaddada muhimmancin haddin kan al’umma wajen cimma nasarar...
Wani babban ɗan Kasuwar Singa da ke Jihar Kano, Alhaji Salisu Abdullahi, ya ce ya yi asarar kaya da kuɗinsu ya haura Naira miliyan 120 a gobarar da ta auku da safiyar ranar Alhamis, wadda ƙone shaguna da yawa. “An kira ni da misalin ƙarfe 6 na safe, na garzaya zuwa kasuwa, sai kawai na tarar komai ya ƙone. “Na karɓi kaya bashi a makon da ya gabata domin ci gaba da sayarwa. Yanzu ban san ta yadda zan tunkari masu kayan ba,” in ji shi. Gobarar, wadda ta fara da misalin ƙarfe 5 na Asuba, ta ƙone shaguna 44 da dukiya mai tarin yawa. Hukumar Kashe Gobara Jihar Kano, ta ce gobarar ta samo asali ne daga matsalar wutar...
A kwanakin nan ana samun raguwar kujerun maniyyata aikin Hajji daga Najeriya, abin da ya jawo fargaba ga masu shirin zuwa kasa mai tsarki da kuma masu hidimar su. A da, Najeriya na samun kujeru sama da dubu casa’in daga gwamnatin Saudiyya, amma cikin shekaru kadan da suka gabata adadin ya ragu zuwa kusan dubu sittin da biyar. Kazalika a yanzu gwamnatin na saudiyya ta bayyana cewa idan har maniyyatan Najeriya basu biya cikakken kudaden hajjin bana ba, to akwai alamun sake rage yawan kujerun zuwa dubu hamsin. NAJERIYA A YAU: Dalilan Malaman Jami’oi Masu Zaman Kansu Na Shiga Ƙungiyar ASUU DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’umma Ko yaya...
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta bayyana shirin ta na faɗaɗa gonakin shinkafar Jangwa daga hektar 3,300 zuwa hektar 5,000 a kakar noma mai zuwa, domin haɓaka samar da shinkafa da kuma ƙarfafa tattalin arziki a jihar. Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana haka yayin ziyarar duba girbin shinkafa a garin Jangwa, ƙaramar hukumar Awe. Gwamnan ya ce faɗaɗa gonakin zai ƙara hektar 3,000 daga yawan da ake da shi yanzu, domin inganta ci gaban tattalin arziki ta hanyar aikin gona. Ya kuma nuna yadda jihar ta samu ci gaba a fannin noma, inda gonar ta faɗaɗa daga hektar 2,000 a bara zuwa hektar 3,300 a wannan shekarar. Gwamna Sule ya sanar da haɗin gwiwar gwamnatin jihar da kamfanin Silvex International, babban kamfani...
A wani muhimmin mataki na inganta harkar lafiya a matakin ƙasa, Karamar Hukumar Gwarzo ta kaddamar da sabuwar Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko (PHC) da aka gina a garin Dankado, da ke cikin gundumar Sabon Birni. Taron kaddamarwar, wanda ke nuna wani sabon ci gaba a tsarin raya jama’a, ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, da wakilan al’umma. Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo, Dakta Mani Tsoho Abdullahi, wanda Mataimakinsa, Alhaji Abdulmumin Garba Lakwaya, ya wakilta, ya tabbatar da jajircewar gwamnatin sa wajen tabbatar da cewa kowane yanki a cikin karamar hukumar na da damar samun ingantacciyar kiwon lafiya mai sauƙin samu da araha. Ya yaba wa Kakakin Majalisar Dokoki ta Gwarzo, Ahmad Shehu Sabon Birni, da sauran kansiloli bisa...
Hukumar Tsarawa da Raya Birane ta Jihar Kano (KNUPDA) ta gudanar da horon cikin gida na farko ga ma’aikatanta, wanda ya mayar da hankali kan aiwatar da dokokin aikin gwamnati, kyawawan ɗabi’un aiki da kuma ingancin ayyuka. Wannan horo, wanda ya zama muhimmin mataki a shirin ƙarfafa ƙwarewar ma’aikata na hukumar, an shirya shi ne domin haɓaka inganci a ayyuka da ƙarfafa ƙwararru da tabbatar da bin ƙa’idojin aikin gwamnati yadda ya kamata. A jawabinta, Manajiyar Darakta ta KNUPDA, Arc. Hauwa Hassan Tudun-Wada, ta bayyana horon a matsayin muhimmiyar hanya ta gina al’adar ladabi da biyayya da nagarta a cikin ma’aikatan gwamnati. Ta yaba da jajircewa da himmar ma’aikata wajen halartar shirin, inda ta jaddada cewa fahimta da bin dokokin...
Mun yi imanin cewa a nan gaba, karin kamfanonin Afirka za su ga fa’idar budaddiyyar kasuwar Sin ta CIIE, za su kuma kara zurfafa hadin gwiwa tare da Sin, da yin amfani da damammakin CIIE don samun moriyar juna. (Mai zane da rubutu: MINA) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ra'ayi Riga Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari November 6, 2025 Ra'ayi Riga Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki November 4, 2025 Ra'ayi Riga Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan November 4, 2025
Rahoton hukumar ya nuna cewa gobarar ta samo asali ne daga matsalar wutar lantarki saboda amfani da wuta ba daidai ba. Ba a samu asarar rai ba. Hotuna: ShareTweetSendShare MASU ALAKA Hotuna HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi October 9, 2025 Hotuna HOTUNA: An Tsaurara Tsaro A Gidan Buhari Da Ke Daura July 15, 2025 Hotuna HOTUNA: Yadda Bikin Al’adun Gargajiya A Masarautar Kaltungo Ya Gudana December 28, 2024
Kungiyar tarayyar Afirka ta bayyana matukar damuwarta akan yadda al’amurra suke tabarbarewa a cikin kasar Mali, tana mai yin Ishara da yadda ‘yan ta’adda su ka killace iyakokin kasar da hana shigar da muhimman kayan bukatun rayuwa na yau da kullum. Tarayyar Afirka ta kuma yi tir da yadda ake kashe farafen hula a kasar ta Mali da hakan yake haddasa rashin zaman lafiya da tsaro. Bugu da kari, tarayyar Afirkan ta nuna cikakken goyon bayanta ga al’umma da kuma gwamnatin kasar Mali da iyalan wadanda aka kashe. Kungiyar ta Afirka ta kuma nuna cewa a shirye ta bayar da dukkanin taimakon da ake bukatuwa da shi a kasar ta Mali domin samun zaman lafiya. Kungiyar “Jama’atu Nusratul-Islam Wal Muslimin”...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran ta damu da ci gaba da karuwar zaman tankiya tsakanin Afghanistan da Pakistan bayan karuwar fadan kan iyaka tsakanin makwabtan biyu. A wata tattaunawa ta wayar tarho da Ministan harkokin wajen Afghanistan Mawlawi Amir Khan Muttaqi a wannan Lahadi, Araghchi ya ce Iran a shirye take ta taimaka wajen samar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu na musulmi. Babban jami’in diflomasiyyar Iran ya kuma jaddada muhimmancin inganta hulda da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu don tabbatar da rabon ruwa daga kogin Harirud. Sojojin Pakistan da Afghanistan sun gwabza a watan da ya gabata, inda aka kashe mutane da dama a tashin hankali mafi muni tun bayan da Taliban ta kwace iko...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Da zarar damuna ta fara bankawana, yanayi na sanyi da zafi kan fara sallama, wanda hakan kan zo da rashin lafiya dake yaduwa a cikin alumma. Ko wadanne dalilai ne suka sa ake samun yaduwar rashin lafiya a wannan lokaci? NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Basir DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025 November 9, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa November 9, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032 November 9, 2025
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta yi kira ga hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ta ba da kulawa ta musamman ga yan asalin jihar wajen daukar aiki. Gwamna Umar Namadi ya yi wannan kiran a lokacin da babban likitan asibitin Dr. Salisu Mu’azu Babura da ma’aikatan asibitin suka kai masa ziyarar a gidan gwamnati dake Dutse. Malam Umar Namadi ya bayyana cewar jihar Jigawa tana da kwararru da kuma masana da za su iya cike gibin guraben ayyukan lafiya a asibitin na Rasheed Shekoni. Gwamnan ya kuma bada tabbacin ci gaba da tallafawa asibitin don cimma nasarorin da aka sanya a gaba. Malam Umar Namadi ya kuma bayyana cewar gwamnatin jihar za ta kari...
Gwamna Namadi Ya Bukaci Asibitin Koyarwa Na RSUTH Ya Bada Fifiko Ga ‘Yan Asalin Jihar Yayin Daukar Ma’aikata
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta yi kira ga hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ta ba da kulawa ta musamman ga yan asalin jihar wajen daukar aiki. Gwamna Umar Namadi ya yi wannan kiran a lokacin da babban likitan asibitin Dr. Salisu Mu’azu Babura da ma’aikatan asibitin suka kai masa ziyarar a gidan gwamnati dake Dutse. Malam Umar Namadi ya bayyana cewar jihar Jigawa tana da kwararru da kuma masana da za su iya cike gibin guraben ayyukan lafiya a asibitin na Rasheed Shekoni. Gwamnan ya kuma bada tabbacin ci gaba da tallafawa asibitin don cimma nasarorin da aka sanya a gaba. Malam Umar Namadi ya kuma bayyana cewar gwamnatin jihar za ta kari...
Kazalika, duk dai a jiya Jumma’ar, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da taron, Chen Binhua, mai magana da yawun Ofishin Harkokin Taiwan na Majalisar Gudanarwar Kasar Sin ya ce taron wanda ya gudana shekaru goma da suka gabata ya karfafa muhimmiyar rawar da Yarjejeniyar 1992 ta taka a matsayin ginshikin siyasa ta bunkasa zaman lumana a dangantakar bangarori biyu na mashigin tekun, kana matukar an ci gaba da amincewa da Yarjejeniyar 1992 kuma aka nuna adawa da batun “‘yancin kai na Taiwan”, to dangantakar bangarorin biyu za ta iya bunkasa cikin lumana kuma za a iya kara inganta muradun ‘yan kasa da ke bangarorin biyu na mashigin tekun. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin November 8, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong November 8, 2025 Daga Birnin Sin Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE November 8, 2025
CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin
A bana ne ake cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da Sinawa suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da yakin duniya na kin tafarkin murdiya, gami da kawo karshen mulkin mallakar kasar Japan a yankin Taiwan da dawo da shi kasar Sin. Kwanan nan ne CMG wato babban rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin ya wallafa jerin wasu rahotannin talabijin guda biyar dangane da batun dawowar Taiwan kasar Sin. ’Yan jarida ma’aikatan CMG ne suka dauki rahotanni da bidiyo a yankin Taiwan, inda suka yi amfani da kwararan shaidun tarihi, don mayar da martani ga wasu kalaman karya da ke cewa wai “matsayin Taiwan ba shi da tabbas”, tare kuma da bankado markarkashiyar mahukuntan jam’iyyar DPP...
Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe, Hajiya Asma’u Muhammadu Inuwa Yahaya, ta jagoranci wani yunƙuri na ganin an tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata daga watanni uku zuwa shida. Ta jagoranci manyan jami’an lafiya zuwa majalisar dokokin jihar domin neman goyon bayan doka kan wannan shiri. Barau ya nemi Trump ya janye kalamansa, ya nemi afuwar Najeriya Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu — Tinubu A yayin taron wayar da kai a majalisar, Hajiya Asma’u ta bayyana cewa shayar da jarirai nono har watanni shida yana da matuƙar amfani wajen rage mace-macen jarirai, inganta garkuwar jikinsu, da bunƙasa ƙwaƙwalwarsu. Uwargidan ta roƙi majalisar, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Abubakar Mohammed Luggerewo, da su samar da doka da za ta...
Sunana Abdulhamid Ado (Danbayaro): Inna lillahi wa inna ilaihirraju’un. Na ji ba dadi na ji komai sai da ya tsaya min har tsahon lokaci, abun ba zai musaltuba, sai dai kawai mu ce Allah ya ji kan Mal. Nata’ala. Mutum ne mai barkwanci, ga zumunci na gaske, ba a yin gulma da shi, baya boye wa mutum gaskiya, kuma baya cin hakkin mutum, kuma abun hannusa baya rufe masa ido. Kuma indai ya samu abun duniya ko baka sani ba sai ya kira ka an ci da kai, harkar sa ba bakin ciki yana da hali mai kyan gaske. Wata rigar san yi da ya kawo mana ‘location’ ya raba mana dukkan ‘crew’ sai da ya bamu, ina ganin...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025 November 7, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku November 7, 2025 Daga Birnin Sin An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka November 7, 2025
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Jibrin Barau, ya nemi Shugaban Amurka, Donald Trump, ya janye barazanar da ya yi wa Najeriya kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Trump, ya yi barazanar ɗaukar matakin soji a kan Najeriya saboda zargin ana zaluntar Kiristoci. Barazanar Trump: Ya kamata shugabannin Najeriya su farka daga bacci — Bishop Kukah Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi a Aso Rock Barau ya ce maganar da Trump ya yi ba ta dace ba, kuma ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa. A cikin wani bidiyo da aka fitar a ranar Juma’a, Mataimakin Shugaban Majalisar, ya ce Najeriya, a matsayinta na ƙasa mai cin gashin kanta, ba za ta yadda a ci zarafinta ko a tsangwame...