HausaTv:
2025-12-11@19:58:41 GMT

Hamas ta sake jaddada wajabcin aiwatar da Shirin tsagaita wuta a Gaza

Published: 27th, October 2025 GMT

Wani babban kusa na Hamas ya jaddada kudirin kungiyar na tabbatar da tsagaita wuta a Gaza, yana mai jaddada cewa Falasdinawa ba sa neman komai illa ‘yancinsu na samun cin gashin kai a duniya.

Khalil Al-Haya, shugaban Hamas a Gaza, ya fadi a wata hira da aka watsa ranar Lahadi cewa bangaren Falasdinawa yana da babban kuduri tare da tabbatar da cewa ba zasu baiwa Israla wata dama ta samun hujjar dawowa da yaki a kan al’ummar Gaza ba.

Ya kara da cewa, “Al’ummar duniya, wadanda suka shahara da kuma wadanda suka yi aiki a hukumance, ba za su bari Isra’ila ta sake halasta mamayarta a kan Gaza ba.

Ya kara da cewa, Hamas ta yi matukar jajircewa kan yarjejeniyoyin da aka rattaba hannu a kansu, inda ta tabbatar da hakan ta hanyar mika fursunoni ba tare da wani bata lokaci ba.

“Mun mika fursunoni 20 daga sojojin mamaya da suke tsare sa’oi  72 bayan fara aiwatar yarjejeniyar tsagaita wuta.

Ya ce zuwa yanzu sun mika gawarwakin fursunoni 17 da suka mutu ga gwamnatin Isra’ila kuma sun kuduri aniyar nemo sauran gawawwakin.

” Za mu yi bincike da gaske kuma alhakin ne mu yin hakan, domin kare hakkokin al’ummarmu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sudan: Dakarun sa kai na Jama’a a Arewacin Darfur sun karyata RSF kan kwace iko da El Fasher October 27, 2025 Araghchi : Iran na maraba da tattaunawar diflomatsiyya da Amurka amma cikin mutunta juna October 26, 2025 Ana Zaman dar-dar gabanin bayyana sakamakon zaben shugaban kasa a Kamaru October 26, 2025 Faransa : An yi Zanga-zangar adawa da isar da makamai zuwa Isra’ila October 26, 2025 Hamas : Ba za mu bari Isra’ila ta sami hujjar ci gaba da yaki a Gaza ba October 26, 2025 ‘Yan Ivory Coast na jiran sakamakon zaben shugaban kasa October 26, 2025 Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Ce: Shugaban Amurka Zai Ci Gaba Da Kasancewa Cikin Rudu October 26, 2025 Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ya Ce: Iran, Rasha Da China Sun Aike Da Sako Mai Muhimmanci October 26, 2025 Ja’afari: Iran Tana Da Isassun Makamai Masu Linzami Masu Cin Zangogi Daban-Daban October 26, 2025 Dan Majalisar Dokokin Tarayyar Turai Ya Ce: Dole Ne A Hakunta Isra’ila Kan Laifukan Da Ta Aikata October 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

An Fito Da Gawawwakin Shahidai 98 Da Aka Binne Cikin Gaggawa A Asibitin “Ash-Shifa”

Masu aikin ceto a Falasdinu, sun fada a ranar Litinin din da ta gabata cewa; An fito da gawawwakin shahidai 98 da aka binne su cikin gaggawa a lokacin yaki, a cikin harabar asibitin al-Shifa a cikin birnin Gaza.

An fito da gawawwakin ne dai domin kai su zuwa sanannun makabartun da ake da su a cikin yankin na Gaza,domin binnewa.

Sanarwar hukumar ceton ta ce; A tsakanin shahidan da akwai wasu 55 da ba iya tantance ko su wanene ba, sai dai an mika su ga kwararrun likitoci domin tantance da gano ko su wanene.

Ma’aikatan agaji suna ci gaba da fito da wasu gawawwakin na shahidai da aka binne a cikin asibitin, domin tantance su, kuma ana yin hakan ne dai a cikin kare hurumin matattun.

A farko-farkon kwanakin yakin Gaza, sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila, sun kai hari akan wannan asibitin, wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane 500 a lokaci daya.

A wani labarin na daban, ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa; A cikin sa’oi 24 da su ka gabata an kai gawawwakin shahidai 5, uku daga cikinsu sun kwanta dama ne sanadiyyar sabbin hare-haren da sojojin mamaya suke kai wa, duk da cewa an tsagaita wutar yaki. Sauran shahidan biyu kuwa wadanda aka fito da su ne daga karkashin baraguzai na gine-ginen da ‘yan sahayoniya su ka rusa gidaje da mutane a cikinsu a tsawon ranakun yaki.

Ma’aikatar kiwon lafiyar ta Gaza ta kuma ce, har yanzu da kawai adadi mai yawa na shahidai da suke a karkashin baraguzai, ana kuma samun jinkirin fito da su ne saboda rashin kayan aiki.

Daga  tsagaita wutar yaki a  ranar 11 ga watan Oktoba 2025 zuwa yanzu  adadin wadanda su ka yi shahada sun kai 376, wadanda su ka jikkata kuwa sun kai 981. Haka nan kuma an tono gawawwakin shahidai 626.

Idan aka koma zuwa Oktoba na 2023 kuwa, to adadin shahidan Falasdinawa ya kai 70,365, wadanda su ka jikkata kuwa sun kai 171,058.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka  Talauci Yana Karuwa A “Isra’ila” Bayan 7 Ga Watan Oktoba December 9, 2025 AU Ta yi Tir Da Harin RSF  A Makarantar Kananan Yara Da Ya Kashe Mutane 80 December 8, 2025 MِِِِDD:  Kisan Kare Dangin Da Isra’ila Ta yi A Gaza Shi Ne Farko Da Yafi Jan Hankalin duniya December 8, 2025 Iran Da Azarbaijan Sun Amince Da Ci Gaba Da Tuntubar Juna Domin Warware Matsaloli December 8, 2025 Iran Da Kasashen Afrika Sun Daura Dammarar Karfafa Alakar Kimiyya Tsakaninsu December 8, 2025 Ecowas Ta Tura Sojoji Zuwa Jamhuriyar Benin Don Dakile Juyin Mulki December 8, 2025 IRGC: Makaman Iran Sun Fada Kan Matatan Man Haifa Har Sau Biyu A Yakin Kwanaki 12 December 8, 2025 Najeriya: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Sanarwan Kubutar Da Yan Makaranta 100 Da Aka Sace December 8, 2025 Iraki Ta Musanta Cewa Ta Tushe Asusun Hizbullah Da Ansarallah December 8, 2025 Sabon Fada Ya Barke A Tsakanin Thailand Da Cambodia December 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hamas : Isra’ila ta gaza cika alkawarin da ta dauka kan yarjejeniyar tsagaita wuta
  • Hamsa: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Bangaren Farko Na Yarjeniyar Tsagaita Bude Wuta A Yankin
  • Amurka ta matsa lamba a kan kotun ICC don janye bincike kan yakin  Gaza da Afghanistan: Reuters
  • Iran Ta yi Tir Da Kisan Karen Dangin Isra’ila A Gaza A Ranar Yaki Da Kisan Kiyashi Ta MDD
  • Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye
  • Iran da Saudiyya sun sake jaddada fadada dangantakarsu
  • RSF : Rabin ‘Yan jarida 67 da aka kashe a bana, a Zirin Gaza ne
  • An cire Tony Blair daga jerin wadanda zasu jagoranci Gaza
  • Isra’ila ta sake kai hare-haren a kudancin Lebanon
  • An Fito Da Gawawwakin Shahidai 98 Da Aka Binne Cikin Gaggawa A Asibitin “Ash-Shifa”