2025-11-28@13:46:16 GMT
إجمالي نتائج البحث: 12033
«Basshar Asad»:
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nahiyyar Afrika (CAF) ta fitar da jerin alƙalan wasa da masu kula da na’urar VAR a gasar cin kofin Nahiyyar Afrika ta 2025, amma babu ɗan Najeriya ko ɗaya. A sanarwar da hukumar ta fitar, ta ayyana alƙalan wasa 28 da masu kula da VAR 14 daga ƙasashe daban-daban. Ƙasar Japan ta fara sayar da injin da ke yi wa mutane wanka Hamɓararren Shugaban Guinea-Bissau ya gudu Senegal Hukumar ta zaɓo alƙalan wasa biyu daga ƙasashen Maroko, Aljeriya, Masar, da kuma Mauritaniya. Masana harkokin wasanni dai na ganin cewa matsalar cin hanci da rashawa ne dalilin yin shagulacin ɓangaro ga alƙalan wasan Najeriya, saboda karɓar na goro musamman a gasar Firimiya. Kawo yanzu an shafe shekaru...
An fara sayar da wani inji da ke yi wa mutum wanka bayan ya burge baƙi a lokacin bajekolin duniya a Japan, in ji wata mai magana da yawun kamfanin da ya ƙera injin, a ranar Juma’a. Masu amfani za su kwanta su rufe kansu a cikin injin da wani murfi, sannan ya wanke su kamar yadda ake wanke kaya a injin wanki, amma ba tare da ya jujjuya su ba, yayin da kiɗa ke tashi a ciki. An gabatar da samfurin na’urar, mai suna “injin wankin ɗan adam”, kuma an sami dogayen layuka a baje kolin watanni shida da aka kammala a Osaka a watan Oktoba bayan ya sami halartar fiye da mutum miliyan 27. Kamfanin Japan mai suna...
Rahotanni sun bayyana cewa kasar Yamen ta yi tir da matakin da kasashen birtaniya da Amurka suka dauka na sukar hukumcin kisa da aka yanke wa wasu yan leken asiri bayan kama su da laifi, tace bata amince da wannan mataki ba kuma tsoma baki ne a harkokin cikin gidanta. Ma’aikatar harkokin wajen kasar yamen ta bayyana cewa ma’aikatar sharia ta kasar tana da cikakken yanci kuma tuni ta yanke hukumcin kisa kan wadanda aka kama da yi wa kasashen waje leken asiri a kasar Haka zalika ta ce duk wata kasa da tace za ta dauki mataki kan wannan hukumci Amurka ce ko birntaniya to za ta dauke shi matsayin shiga shugalarta ne, kuma ba za ta amince da...
Rahotanni sun bayyana cewa Isra’ila ta kai hari ne a garin beit Jin dake gefen birnin damaskas da ya kai ga mutuwar mutane 10 yayin da wasu da dama kuma suka jikkata, wannan ya faru ne bayan rikici da ya barke tsakanin mazauna yankin da kuma sojojin Isra’ila da ya kai ga jikkata sojoji 6 . yawan kai hare-hare da Isra’ila ke yi yana nuna irin zaman dar-dar da ake ciki a kudancin kasar siriya musamman a damaskas da Qunaitara, kuma wannan hari wani bangare ne na mataken da sojojin isra’ila ke dauka wuraren sojojin kasar siriya da hakan kara jefa farare hula cikin fargaba da rashin kwanciyar hankali. Rahotanni sun bayyana cewa sojojin Isra’ila suna ci gaba da tunkarar...
Jagoran juyin musulunci na kar iran Ayatullah sayyid Ali Khamna’i ya bayyana cewa kasar Amurka bata ji da dadi ba a yakin kwanaki 12 da ta kaddamar a kan kasar iran a watan yuni, duk da amafani da ta yi da manyan makaman yaki na zamani da suka hada da jiragen yaki da kuma makaman kariya . Har ila yau jagoran yace Amurka da isra’ila sun sha kashi a yakin kwanaki 12 da suka kaddamar kan kasar iran, sun kai harin ne don su ci blus, sai suka koma da borin kunya, basu iya tabuka komai ba, wannan babban shan kashi ne a garesu, Yace wasu rahotanni sun nuna cewa gwamnatin sahyuniya ta shirya yakin shekaru 20, ta shirya tunzura...
Gammayar ministocin harokin wajen kungiyar tarayyar Turai sun fitar da wata sanarwa da aciki suka soki hare haren da yahudawa yan share wuri zauna suke kai wa falasdinawa a gabar yammacin kogin Jodan da isra’ila ta mamaye kuma yake kara ci gaba fiye da kowanne lokaci a baya, Sanarwar ta fito ne daga minsitocin kasashen birtaniya, jamus , faransa da kuma italiya inda manyan jami’an diplomsiyarsu suka bayyana hare-haren a matsayin mataki ne na tada fitina da kuma ta’addanci. Haka zalika sun yi kira ga fira ministan isra’ila Benjamin na tanyaho da yayi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansa karakshin dokokin kasa da kasa, kuma ya kiyaye hakkin falasdinwa dake zaune a bangarorin da aka mamaye. Daga karshe...
An rantsar da Gen Horta N’tam a matsayin sabon shugaban mulkin sojan kasar Gunea-Bissau bayan juyin mulkin da sojoji suka yi. Gen Horta N’Tam ya zamo shugaban da zai mika mulki ga shugabannin farar hula inda zai kasance a kargar mulki na tsawon shekara guda. An dai rantsar da shugaban ne a wani takaitacce kuma gajeren bikin da aka yi ranar Alhamis. Wasu kungiyoyin farar hula a Guinea-Bissau sun soki shugaban da aka hambare, Umaro Sissoco Embalo da kitsa juyin mulki na wasan kwaikwayo a kansa, bisa taimakon sojoji, inda suke cewa ya shirya wasan kwaikwayon ne domin hana sakamakon zaben da aka yi ranar Lahadi fitowa idan bai yi nasara ba. Sun ce sun kwace ikon ne domin dakile...
Hamɓararren Shugaban Ƙasar Guinea-Bissau, Umaro Sissoco Embaló, ya isa ƙasar Senegal bayan da sojoji da suka kifar da gwamnatinsa a wannan makon suka sake shi. Wannan ya biyo bayan tattaunawar ƙungiyar ECOWAS yayin da tashin hankali ke ƙaruwa a ƙasar sakamakon juyin mulkin. Jonathan ya dawo Najeriya bayan juyin mulki ya ritsa da shi a Guinea-Bissau Ya kamata ’yan majalisar Najeriya su koma zaman wucin gadi – Ndume Ma’aikatar harkokin wajen Senegal a cikin wata sanarwa ta ce Embaló ya sauka a cikin ƙasar “lafiya kalau” a jirgin sojoji da aka ɗauka a haya da yammacin Alhamis.
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya dawo Najeriya bayan juyin mulkin sojoji ya ritsa da shi a ƙasar Guinea-Bissau inda ya je sa ido kan zaben ƙasar. Jonathan ya isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da yammacin Alhamis, kusan kwana biyu bayan sojoji sun karɓi mulki a ƙasar da ke yammacin Afirka. Ya kamata ’yan majalisar Najeriya su koma zaman wucin gadi – Ndume An janye ’yan sanda 11,566 daga yi wa manyan mutane rakiya – Egbetokun Ya isa filin jirgin sama na Abuja a cikin jirgin gwamnatin Guinea-Bissau, inda tawagar magoya baya da jami’an gwamnati suka tarbe shi. Tsohon shugaban kasar ya je Guinea-Bissau ne don sa ido kan zaben shugaban kasa da na majalisar...
Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya ce Najeriya na iya ajiye biliyoyin naira a duk shekara idan aka rungumi tsarin majalisa ta wucin gadi. Yayin da yake magana a gidan talabijin na Channels ranar Alhamis, Ndume ya ce kuɗin da ake kashewa wajen kula da Majalisar Dokoki a tsarin zama kodayaushe ba zai dore ba, musamman a wannan lokaci da ƙasar ke fama da matsalolin kuɗi da tsaro. An janye ’yan sanda 11,566 daga yi wa manyan mutane rakiya – Egbetokun An gano gawawwakin mata uku ’yan Kamaru da aka sace a Anambra “Kudin gudanar da gwamnati ya yi yawa sosai. Idan ’yan majalisa suka zauna na wucin gadi, gwamnati za ta ajiye biliyoyi,” in ji shi. Ya ce...
Babban Sufeton ’yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya ce sun janye ’yan sanda 11,566 da ke rakiyar manyan mutane kamar yadda Shugaban Ƙasa ya ba da umarni a kwanakin baya. Ya kuma ce an sake tura waɗannan jami’an zuwa muhimman wuraren da aka fi buƙatars su don kare al’ummomi masu rauni a fadin ƙasa. NAJERIYA A YAU:Waiwaye Kan Irin Gudunmawar Da Sheikh Dahiru Bauci Ya Bayar Ga Cigaban Addini An gano gawawwakin mata uku ’yan Kamaru da aka sace a Anambra Aminiya ta rawaito cewa Shugaba Bola Tinubu, a ranar Lahadi, ya bayar da umarnin janye jami’an ‘yan sanda daga aikin tsaron manyan mutane tare da umartar a sake tura su zuwa ayyukan tsaro na asali. Umarnin ya biyo bayan...
Ministan yakin Isra’ila ya yi barazanar kai wa kasar Lebanon hari gadan-gadan, inda ya bukaci kungiyar Hizbullah ta kwace damarar makamai. Ministan yakin Isra’ila, Isra’ila Katz, ya yi gargadin cewa Tel Aviv a shirye take ta kaddamar da wani sabon yaki kan kasar Labanon matukar kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta ki mika makamanta zuwa karshen shekarar 2025. Da yake jawabi ga Knesset na Isra’ila, Katz ya yi ikirarin cewa Washington ta ba Beirut wa’adin kwance damarar Hezbollah zuwa karshen shekara, amma ya ce ba ya tsammanin kungiyar za ta mika makamanta. “Ban yi imani cewa Hizbullah za ta mika makamanta bisa radin kanta ba,” kamar yadda ya shaida wa ‘yan majalisar. “Idan Hezbollah ba ta yi watsi da makamanta a karshen...
Yayin da ayyukan sojin Amurka ke karuwa a yankin Caribbean da Pasifik, shugaban kasar Colombia Gustavo Petro ya zargi gwamnatin Trump da yin amfani da matsin lamba kan kasar Venezuela da sunan yaki da fataucin muggan kwayoyi a matsayin hujjar samun damar shiga kasar don mamaye albarkatun man fetur da Allah ya huwace wa kasar. Man fetur shine tushen al’amarin, Petro ya fadawa CNN a cikin wata hira ta musamman, yana mai cewa Venezuela ita ce kasar da tafi kowace kasa yawan danyen ma a duniya. “Saboda haka, wannan batun baki dayansa a kan man fetur ne. Na yi imani cewa (Shugaban Amurka Donald Trump) na tunanin yadda zai samu mai a kasar Venezuela ne ba batun dimokiradiyya ko yaki...
Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Mahmoud Ali Youssouf, ya yi Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a Guinea-Bissau a ranar Alhamis, inda ya yi kira da a gaggauta sakin hambararren shugaban kasar Umaro Sissoco Embaló da sauran jami’an da ake tsare da su. A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta sake nanata cewa kungiyar Tarayyar Afirka ba za ta amince da duk wani sauyi na gwamnati da ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar ba. Ya jaddada muhimmancin mutunta tsarin zabe da ake gudanarwa da kuma tabbatar da tsarin mulkin kasar, kamar yadda hukumar zabe ta kasar ta tanada. Youssouf ya yi kira ga dukkan bangarorin da su yi taka tsantsan don hana ci gaba da...
Rundunar ’yan sandan Jihar Anambra ta gano gawar wasu mata uku ’yan ƙasar Kamaru da ake zargin waɗanda suka yi garkuwa da su domin neman kuɗin fansa sun kashe su. Haka kuma, rundunar ta ce ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a lamarin, Nonso Augustine Akpeh da Kingsley Akpeh, waɗanda ake zargin suna cikin gungun masu garkuwar da suka sace matan. Wata mata ta kashe ’yar shekara 7 a Ribas El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADC Tun dai a ranar Litinin, 10 ga watan Nuwamban nan ne aka sace matan a garin Anam da ke Jihar Anambra, inda suka saba zuwa sayen kayayyakin kasuwanci. Jami’an rundunar na sashen yaki da masu garkuwa da mutane da...
Ana fargabar cewa wata mata mai suna Success ta kashe wata yarinya mai shekaru bakwai, Alicia Olajumoke, a unguwar Rumueme da ke birnin Fatakwal na Jihar Ribas. Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa matar da ake zargin tana da kusanci da dangin mahaifiyar yarinyar, wacce ita kaɗai ce a wurin iyayenta. El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADC An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya Bayanai sun ce ita ma matar ta caka wa kanta wuƙa a wuya bayan kashe yarinyar, kuma bayan an garzaya da duk su biyun asibiti, likitoci suka tabbatar da cewa sun riga mu gidan gaskiya. Lamarin wanda ya faru a ranar Talata ya ɗimauta mazauna yankin, la’akari da zargin...
Sufeto Janar na ’Yan sandan Nijeriya, Olukayode Egbetokun, ya sanar da cewa sun aiwatar da umarnin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na janye dakarunsu daga gadin ɗaiɗaikun mutane da ake kira VIP. IG Egbetokun ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a yau Alhamis, yana mai cewa zuwa yanzu sun janye dakaru 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya. Mbappe ya ci ƙwallaye 4 rigis a wasan Madrid da Olympiacos An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji “Wannan karon za mu aiwatar da umarnin da kyau saboda umarnin shugaban ƙasa ne,” in ji shi. “Babu wani gwamna, ko minista, ko abokaina da za su kira su takura min saboda sun san cewa umarnin...
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana jimaminsa kan rasuwar babban malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi, lamarin da ya ce ya kaɗu matuƙa da ya samu labarin. Tinubu ya ce jagoran na ɗarikar Tijjaniya mutum ne mai daraja da ƙima, sannan ya bayyana shi a matsayin madubi wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa. Rasuwarsa za ta ba babban giɓi a Najeriya,” in ji shugaban. Shi ma Tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana rasuwar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi a matsayin rashi babba ga al’ummar Musulmi na Najeriya da ma Afirka baki ɗaya. A wata sanarwa da Atiku ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, ya bayyana marigayin da babban malami wanda ya koyar da addini...
Iran ta yi Allah wadai da matakin gwamnatin Ostiraliya na ayyana Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) a matsayin “mai tallafawa ta’addanci,” “Matakin da gwamnatin Ostiraliya ta dauka wani abu ne mai laifi ne mai hadari, wanda aka tsara a karkashin gwamnatin Sahayoniya don karkatar da hankalin jama’a daga kisan kare dangi da aka yi a Gaza,” in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran a cikin wata sanarwa da aka fitar a yau Alhamis. Gwamnatin Ostiraliya ta sanya IRGC a matsayin “mai tallafawa ta’addanci” bisa zarge-zargen da ba su da tushe na cewa IRGC ta shirya kai hare-hare kan Al’ummar Yahudawa na Ostiraliya. Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da wannan shawarar da babbar murya, tana mai Allah...
Shugaban Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa ya soki kalaman takwaransa na Amurka Donald Trump na cewa ba zai gayyace shi taron kasashen gungun G20 mafiya karfin tattalin arziki na duniya a shekara mai zuwa a Florida. Ramaphosa ya ce abin takaici ne yadda Trump ke ci gaba da daukar matakai bisa labaran da ba na gaskiya ba ko kuma aka yi musu kwaskwarima. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba zai gayyaci Afirka ta kudu taron na badi ba, da Amurka zata karbi bakunci, kuma ya nanata sukar da yake yi wa Afirka ta kudun, kan zargin cewa an aikata kisan kiyashi a Afirka ta Kudu a kan tsirarun fararen fata. Amurka ta...
Kungiyar raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta yi Allah wadai da juyin mulkin da ya faru a ranar Alhamis a kasar Guniea Bissau, kwanaki uku bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu, inda ta kira shi da “barazana kai tsaye ga zaman lafiyar kasar da yankin.” Wannan “juyin mulkin soja” ya zama “mummunan keta tsarin mulki” kuma “barazana kai tsaye ne ga zaman lafiyar kasar da yankin baki daya,” in ji ECOWAS a cikin wata sanarwa da ta fitar. Dama kafin hakan Shugabannin tawagar masu sa ido kan zaben na Guinea Bissau na kungiyar Tarayyar Afirka da ECOWAS, sun bayyana ” matukar damuwa game da sanarwar da sojoji suka yi na yin juyin mulki a kasar.” A...
Kasashen Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi Allah wadai da “karuwar yawan tashin hankalin” da yahudawa ‘yan gudun kama wuri zaman ke yi wa fararen hular Falasdinawa, tare da yin kira ga Isra’ila da ta kare al’ummar Yammacin Kogin Jordan. “Wadannan hare-haren dole ne a daina su. Suna kawo cikas ga kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya da kuma tabbatar da tsaron Isra’ila mai dorewa,” in ji ministocin harkokin waje na kasashen hudu a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa. Sun kuma yi maraba da ” bayyanannar adawar” da shugaban Amurka Donald Trump ya nuna kan yunkurin mamaye Yammacin Kogin Jordan kuma sun sake nanata adawarsu “ga duk wani nau’in mamayewa, ko na bangare, ko na...
An sake tabbatar wa ma’aikatan Gwamnatin Tarayya FG da suka yi ritaya cewa za a biya su wani bangare na kudaden ariyas a cikin wannan watan, kamar yadda hukumomin da abin ya shafa suka yi alkawari. Mataimakin Sakataren ƙungiyar masu karɓar fansho ta ƙasa, Alhaji Ahmed Gazali, ya bayar da wannan tabbaci yayin da ake tattaunawa da shi ta wayar tarho daga Abuja. Alh. Ahmed Gazali, ya yi bayanin cewas daraktan dake kula da kudade na ofishin akanta janar na tarayya ya tabbatar da daukan matakin hakan na biyan kudaden. Ya bayyana fatan ganin kudirin FG na gaggauta biyan kudade, domin dakatar da duk wata zanga zanga wanda hakan bai dace ba ga ma’aikatan da suka yi ritaya domin...
Ɗan wasan gaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid, Kyalian Mbappe ya samu nasarar zura kwallaye huɗu rigis a ragar Olympiacos a wasan mako na biyar na kofin zakarun nahiyyar turai da suka buga a yammacin jiya Laraba. Real Madrid dai caskara Olympiacos 4-3 ne a wasan, lamarin da ya ba ta damar haɗa maki 12 cikin fafatawa biyar. Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban gibi a Najeriya – Tinubu An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji Kawo yanzu dai Mbappe ya shiga gaban Victor Osimhen na Galatasaray wajen yawan zura ƙwallaye a raga a gasar ta kakar nan, inda Mbappe ya ke da 9, yayin da Osimhen wanda ke fama da rauni...
Daga Usman Muhammad Zaria Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, Dr. Builder Muhammad Uba, ya aiwatar da wani aiki na da naira miliyan biyar domin tallafa wa aiwatar da Shirin Tallafawa Yara Mata (AGILE) a yankin. Aikin ya hada da gyaran ajujuwa biyu da samar da muhimman kayan aiki, ciki har da injunan dinki, injin yin surfani wato (monogram) da shirin AGILE ya bayar kyauta wanda Dr. Uba ya shirya, ya taimaka wajen ganin an fara amfani da shi, tare da samar da janareta da tabarmi domin inganta koyarwa da horo. Wannan ci gaban ya biyo bayan wani bincike da tawagar AGILE ta jihar Jigawa ta gudanar a baya, inda ta bayyana cewa wuraren koyon sana’o’in na...
Sojojin Guinea-Bissau sun naɗa Janar Horta Nta Na Man a matsayin sabon shugaban ƙasar na rikon kwarya, kwana ɗaya bayan sun yi juyin mulki tare da kama shugaban ƙasar, Umaro Sissico Embalo. Sojojin dai sun kwace mulkin ne yayin da ake shirin bayyana sakamakon zaɓen kasar mai cike da takaddama. Majalisar Wakilai ta nemi gwamnati ta gaggauta dauko Jonathan daga Guinea Bissau Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi “Na rantsar da kaina a matsayin shugaban Babban Kwamandan Soja,” in ji Janar Horta bayan ya karbi rantsuwar aiki a wani biki da aka gudanar a hedkwatar sojoji a ranar Alhamis, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito. Daruruwan sojoji dauke da makamai sun...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kaduwa da rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Fitaccen malamin ya rasu a Bauchi ranar Alhamis yana da shekaru 101. Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka A cikin wata sanarwa da Kakakin shugaban, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin jagoran da ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa, wa’azi da jagorantar al’ummar Musulmi. Tinubu ya ce rasuwar malamin ba wai asara ce ga iyalansa da almajiransa kawai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya. “Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba ne kuma murya ce ta daidaito...
Majalisar Wakilai a ranar Alhamis, ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta yi amfani da diflomasiyya da duk wasu hanyoyi don tabbatar da dawowar tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan lafiya daga Guinea Bissau, bayan juyin mulkin sojoji a ƙasar. Wannan kuduri ya biyo bayan amincewa da kudurin gaggawa da Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere, ya gabatar. Ihonvbere ya shaida wa Majalisar cewa Jonathan, wanda ya je ƙasar domin sa ido kan zaɓe, ya makale bayan juyin mulkin, yana mai cewa gwamnati ta nemo hanyoyin da za su tabbatar da dawowarsa lafiya. Muna tafe da karin bayani…
Daga Sani Sulaiman Gwamnan Jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas, ya yi jimami kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2025, yana da shekaru 102. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Mista Emmanuel Bello, ya sanyawa hannu. Gwamnan ya ce rasuwar wannan babban malami babban rashi ne ga kasa, yana mai nuna cewa a wannan lokaci ne ake matuƙar bukatar irin gudummawar da yake bayarwa, duba da kalubalen da kasar ke fusfuskanta. Ya kara da cewa marigayi Sheikh ya koyar da ilimi da zai ci gaba da jagorantar kasa kan...
Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta sanar da karbar gawawwakin shahidai 15 a jiya Laraba a karkashin yarjejeniyar musayar fursunoni, da kungiyar agaji ta “Red Cross” ta shiga tsakani. Sanarwar ma’aikatar kiwon lafiyar ta Palasdinu ta kuma ce, daga lokacin da aka fara musayar zuwa yanzu,adadin gawawwakin shahidan da su ka karba sun kai 345, kuma an riga an gudanar da gwaje-gwaje akan 9 daga cikinsu domin tantancewa. Mai magana da kungiyoyin agaji Mahmud Basal ne ya tabbatar da karbar gawawwakin na shahidai da mika su ga asibitin Nasar da yake a Khan-Yunus a kudancin Gaza. Tun da fari, ‘yan gwgawarmaya a Gaza sun mika gawar wani sojan mamaya da marecen shekaran jiya Talata. A gefe daya kakakin kungiyar Hamas,...
A ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamban 2025 ce Allah ya yi wa fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma jigo a Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi rasuwa. Ya rasu yana da sama da shekaru 100 a duniya. Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa Sheikh Dahiru Bauchi: Malamin da zuri’arsa ta fi kowacce yawan mahaddata Alkur’ani Baya ga tarin iliminsa da yawan shekaru, akwai wasu tarin baiwa da Allah Ya ba malamin, wadanda ba kowa ne ya san da su ba. Aminiya ta yi nazari a kansu, inda ta zakulo muku abubuwa 18 da ya kamata ku sani a kansa. Ga wasu daga ciki: Ya fi kowa yawan zuri’ar da ta haddace Alkur’ani a duniya, inda...
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya kafa tarihin zama mutumin da ya fi kowa yawan zuri’ar da ta haddace Alkur’ani a tarihin duniya. Alkaluma sun nuna cewa shehin malamin, wanda a kwanan nan ya cika shekara 100 a duniya, yana da ’ya’ya da jikoki da ma tattaba-kunne kusan 300 da suka haddace Alkur’ani. Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa Sheikh Dahiru Bauchi ya cika shekara 101 a duniya A cewar kundin tattara bayanai na Cholan Book Of World Records, wadanda suka karrama malamin da lambar yabo, Sheikh Dahiru Bauchi shi ne mutum na farko da ya taba samun irin wannan baiwar. Bayanai sun nuna fitaccen malamin yana da ’ya’ya 95 da jikoki 406 da tattaba-kunne...
Kwamandan rundunar soja ta “Sayyidush-shuhada” dake Tehran Janar Qurbani Muhammad Wali Zadeh ya bayyana cewa; makamai masu linzami da Iran take da su ne, da kuma jiragen sama marasa matuki suke takawa makiya birki.” Janar Qurbani Muhammad Wali Zadeh ya kuma ce; Albarkacin sadaukar da jinanai da shahidai su ka yi ne da kuma kwazon kwararrun masana, su ka sa Iran samun wannan karfin da take da shi. Wali Zadeh wanda ya halarci taron girmama rundunar sa-kai ta Basiji da kudancin birnin Tehran, ya kara da cewa, Iran ta samu matsayin da take da shi ne a wannan lokacin daga jihadin shahidai da tsayin dakar al’ummar Iran, sannan kuma ya kara da cewa; A halin yanzu karfin Iran a fagen...
Daya daga cikin ‘ya’yan babban malamin addinin musulunci a Najeriya Sayyid Ali Dhahiru Usman Bauchi ne ya tabbatar wa da jaridar “Daily Trust” rasuwar malamin. Sayyadi Ali ya furta cewa: ” Tabbas Shehi ya koma ga mahaliccinsa, mu duka daga Allah muke, kuma zuwa gare shi za mu koma.” Haka nan kuma ya kara da cewa, Lokaci ya yi da shehun malamin zai huta,kuma mun gode wa Allah da ya yi mana komai, ya tsawaita rayuwar shehi har zuwa wannan lokacin. Shi dai Shehu Dhariu Usman Bauchi an haife shi ne a 29 ga watan Yuni na 1927, ya kuma rasu yana dan shekaru 97 a wannan Alhamis din 27/ ga watan Nuwamba 2025. Gabanin rasuwarsa ya kasance daya daga...
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi, a matsayin babban rashi ga al’umma. Gwamnan ya bayyana malamin a matsayin jagoran haɗin kai, zaman lafiya, da fahimtar juna tsakanin Musulmi da mabiya addinai daban-daban. ’Yan sanda sun gano harsasai 210 a kan titin Zariya-Funtuwa Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa A cikin saƙon ta’aziyya da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya sanya wa hannu, gwamnan ya ce Gwamnatin Jihar Bauchi tana alhinin rasuwar malamin. Dahiru Bauchi, ya rasu da safiyar ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamba, 2025 a Bauchi, yana da shekara 102. Gwamnan, ya ce Sheikh Dahiru Bauchi babban malami ne na addinin...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta gano harsasai 210 da aka jefar a kan babbar hanyar Zariya zuwa Funtuwa, a unguwar Dogo Itace da ke Samaru, Zariya. Lamarin ya faru ne lokacin da DPO na Samaru tare da tawagarsa suke sintiri a kan hanyar. Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau Jama’ar yankin ne suka kira rundunar cewar fasinjojin wata mota ƙirar Volkswagen Golf mai launin baƙi sun jefar da wata jaka, sannan suka tsere. Da jami’an rundunar suka isa, sun tarar da jakar da aka jefar. Bayan gudanar da bincike, sun gano harsasai 210 na ɗangon 7.56mm. DPO ɗin yankin ya sanar da sauran jami’an rundunar da ke kan hanyar...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A cikin shekarun nan, matsalolin tsaro a Najeriya—kamar ta’addanci, da garkuwa da mutane, da rikicin manoma da makiyaya, da kuma ayyukan ’yan bindiga—suna kara ta’azzara, lamarin da ya sanya al’umma da masana tsaro ke tambayar wace hanya ta fi dacewa gwamatani ta yi amfani da shi wajen kawo karshen wadannan matsaloli da suka ki ci suka ki cinyewa tsawon shekaru. Yayin da wasu ke ganin amfani da karfin soji ne kadai hanyar da zai kawo karshen wannan matsala, wasu na ganin tattaunawa ne kadai mafita, wasu har ila yau na ganin idan aka yi amfani da gaurayen biyun zai fi dacewa. NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke...
Bayan an zabi kasar Iran a matsayin mamba a kwamitin zartarwa na hukumar yaki da makaman guba ta duniya, wato ‘ the Chemical Weapons Convention (CWC)’ da kuriun jimillar yan majalisar, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa Iran zata yi amfani da damar da ta samu na bin hakkin mutanen kasar Iran dangane da makaman guba wadanda Sadam Husain ya yi amfani da su a kan mutanen kasar a yakin shekaru 8 (1980-88). Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a taron CWC a birnin Hague a ranar Talatan da ta gabata. Ya kuma kara da cewa Iran zata bukaci a hukunta kasashen da suka taimakawa Sadam Husain a wajen...
Wata cibiyar bincike mai suna “Frensic Architecture’ ta bada sanarwan cewa, HKI tana fakewa da tsagaita budewa juna wuta a Gaza a matsayin dama ta sake shata kan iyakoki a zirin gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto cibiyar tana cewa a halin yanzu HKI ta maida ‘koren layin da Trump ya shata a shwarar tsagaita wuta da ya gabata na tsaida yaki a Gaza a matsayin sabon taswirar Gaza. Labarin ya kara da cewa an Trump ya gabatar gabatar da wannan shawarar ce don sake tsuge fadin gaza, wanda kuma a halin yanzi sojojin hki suna hana Falasdinawa a gaza zuwa kusa da layin da suka shata, kuma duk wanda ya matso kusa da shi suka...
Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta bada sanarwan cewa yawan Falasdinawa wadanda sojojin HKI suke kashewa a Gaza yana karuwa duk tare da abinda suka kira tsagaiya budewa Juna wuta. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto ma’aikatar na cewa a cikin sa’oii 24 da suka gabata sojojin HKI sun kashe Falasdinawa 2 sannan masu bincike sun gano gawakin mutanen 8 a karkashin burbushin gine-ginen da aka rusa a cikin shekaru 2 da suka gabata. Labarin ya kara da cewa daga ranar 11 ga watan Octoban shekara ta 2025 ya zuwa yanzu sojojin HKI sun kashe falasdinawa 347 sannan sun raunata wasu 889 wanda ya kara yawan Falasdinawa da suka yi shahada tun fara yakin tufanul aksa a...
Tsohon shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan a halin yanzu yana birnin Bissau babban birnin kasar Gunea Bissau bayan da sojoji suka kwace mulki suka kuma hana shiga da fita daga kasar. Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar da daruruwan masu sanya ido a zaben da aka gudanar a kasar a makon da ya gabata sun kasa ficewa daga kasar bayan juyin mulkin. Labarin ya kara da cewa sojojin da suka yi juyin mulkin sun kwace iko da kasar ne a dai-dai lokacinda ake irga kuri’un da aka kada a zaben da aka gudanar a cikin yan kwanakin da suka gabata. Kafin juyin mulkin dai yan takaran shugaban kasa a zaben shugaba Umaro Sissoco da kuma...
Ma’aikatar Ma’adinai da wutan lantarki a yankin Kurdistan na kasar Iraki ta bada sanarwan cewa an dakatar da tura iskar gas zuwa cibiyoyin samar da wutan lantarki a yankin saboda hare-haren da aka kai kan wata cibiyar hakar iskar gas a yankin. Tashar talabijan ta Almayadeentv ta kasar Lebanon ta bayyana cewa wani jirgin yaki wanda ake sarrafashi daga nesa ne ya fada kan cibiyar hakar iskar gas ta Kurmur, ta kuma jawo dakatar da tura iskar gas din. Labarin ya kara da cewa jirgin ya fada kan cibiyar hakar iskar gas ta kurmur a bangaren Chemchel na lardin Sulaimaniyya ne, ya kuma haddasa barna mai yawa, wanda mai yuwa har da rasa rai ko rayuka. A halin yanzu dai...
Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya maƙale a Guinea-Bissau bayan da sojoji suka yi juyin mulki tare da karɓe ragamar mulkin ƙasar. Jonathan da sauran baƙi baƙi masu sanya ido kan zaɓen da aka gudanar, ba za su iya barin ƙasar ba domin sojoji sun rufe iyakokin ƙasar baki ɗaya, tare da dakatar da zaɓen gaba ɗaya. Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniya Lamarin ya samo asali ne bayan manyan ’yan takara biyu sun yi iƙirarin samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana. Ba jimawa wasu dakarun sojin ƙasar suka hamɓarar da gwamnatin farar hula ta ƙasar. Sun kuma sanar da dokar hana fita da...
An kulle Fadar Shugaban Kasar Amurka ta White House tare da wasu gine-ginen gwamnati da dama, sakamakon harbin ɗan bindigar da ya raunata sojoji biyu a kusa da fadar. A yayin, an harbe masu tsaron fadar biyu har lahira. Gwamna Patrick Morrisey da farko ya ce an kashe sojojin, amma daga baya ya ce yana samun “rahotanni masu karo da juna” game da halin da suke ciki, yana mai da cewa za a fitar da ƙarin bayani idan an tabbatar. A cikin wani rubutu a shafin X, ya ce, “Yanzu muna samun rahotanni masu cin karo da juna game da halin sojojin biyu, kuma za mu bayar da ƙarin bayani idan mun samu cikakken rahoto. “Addu’o’inmu suna tare da waɗannan...
Daga Isma’il Adamu Gwamna Dikko Radda na Jihar Katsina ya sanya hannu kan kudirin kasafin kudin jihar na 2026 na Naira Biliyan 897, makonni uku bayan gabatar da shi a gaban majalisar dokokin jihar. Yayin rattaba hannu a Fadar Gwamnati da ke Katsina, a gaban ‘yan majalisar dokokin jihar, gwamnan ya jinjinawa majalisar bisa gaggawar amincewa da kasafin, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da shi yadda ya dace. Ya bayyana cewa kashi 82 cikin ɗari na kasafin an ware shi ne ga manyon ayyuka(capital expenditure), yayin da kashi 18 cikin ɗari aka ware ga ayyukan yau da kullum(recurrent expenditure), rabo wanda ya ce ya fi abin da doka ta baya ta tanada, wadda ke bukatar kada kudaden gudanarwa...
Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta bukaci maniyyatan aikin hajjin 2026 da su gaggauta biyan kudin kujerun su kafin ranar 24 ga watan gobe. Darekta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taro da shugabannin sassa na hukumar da shugabannin shiyya da sauran ma’aikatan hukumar a Dutse babban birnin jihar. Yana mai cewar, hukumar aikin hajji ta kasa wato NAHCON ta bayyana ranar 5 ga watan Disamba da ta kayyade a matsayin ranar rufe biyan kudin kujerun aikin Hajjin 2026 a fadin kasar nan. Ya bayyana cewar ranar itace ranar karshe da hukumar aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta kayyade na biyan kudin kujerun...
An naɗa Andrea Thompson, ’yar ƙasar Birtaniya, a matsayin mace mafi ƙarfi a duniya. Wannan na zuwa ne bayan tabbatar da cewa wanda aka bayyana a matsayin zakara — Jammy Booker — tun da farko namiji ne da aka sauya masa halitta zuwa mace, lamarin da ya sa aka soke nasararsa bisa saɓawa dokokin gasar. Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro Real Madrid za ta yi karon-batta da Olympiacos a Gasar Zakarun Turai Thompson mai shekaru 43, ta karɓi lambar yabon ne daga masu shirya gasar nunin ƙarfi ta duniya, kwanaki biyu bayan kammala bikin a Arlington da ke birnin Texas na Amurka, wanda aka gudanar a daga 20 zuwa 23 ga watan Nuwamba. Gasar nuna ƙarfin ta...
Daga Bello Wakili Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkar tsaro a duk fadin kasar, sakamakon karuwar kalubalen tsaro da ake fuskanta. Shugaban ya ce za a dauki sabbin jami’an tsaro nan ba da jimawa ba, wadanda suka hada da na sojiin, ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro — domin karfafa matakan tsaron kasa. A karkashin sabon umarnin, an bai wa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ikon daukar karin jami’aaidubu ashirin, wanda hakan zai kawo yawan sabbin jami’an da za a dauka bana zuwa dubu hamsin. Shugaban kasar ya kuma amince a yi amfani da sansanonin horas da matasa masu yi wa kasa NYSC a matsayin wuraren horaswa na wucin gadi, sakamakon gyare-gyaren da ake yi a...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya. Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan. Shugaban ya bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an ’yan sanda 20,000, lamarin da zai ƙara adadin jami’an da za a ɗauka zuwa 50,000, bayan umarnin da ya bayar a ranar Lahadi na ɗaukar jami’an tsaro 30,000. Real Madrid za ta yi karon-batta da Olympiacos a Gasar Zakarun Turai Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu Haka kuma, Tinubu...
Rahotanni sun bayyana cewa kididdigar da ma’aikatar harkokin wajen yankin falasdinu ta fitar ya nuna cewa sojojin Isra’ila sun kashe akalla yan mata 33000 a ci gaba da yakin kare dangi da take yi kan alummar Gaza. Ma’aikatar fa fitar da wannan sanarwar ce a wajen taron ranar kawo karshen hare-hare kan mata ta duniya . kuma tayi kaca-kaca da gwamnatin sahayuniya game da irin muggan laifukan yaki da ta tafka, inda ta rika amfani da makamai na zamani kan alummar falasdinu Kididdigar ta nuna cewa sama da mata 12500 da kuma yara 20,000 ne Isra’ila ta kashe a harin da ta kai tun daga watan oktoban shekara ta 2023. Har ila yau ma’aikatar ta bayyana cewa lallai a kwai...
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya dawo Abuja daga birnin Luanda na Angola, inda ya halarci taron AU–EU karo na 7 a madadin Shugaba Bola Tinubu. Ya wakilci shugaban kasa a taron G20 na 2025 da aka yi a Johannesburg, Afirka Ta Kudu. A Angola, Shettima ya karanta sakon Shugaba Tinubu wanda ya sake jaddada bukatar Afrika na samun kujerun dindindin da ikon zartarwa a Majalisar Dinkin Duniya. Ya kuma bukaci Tarayyar Turai su hada kai da Afrika wajen samar da tsare-tsaren zaman lafiya da tsaro. Shugaba Tinubu ya tabbatar da kudirin Nijeriya na ci gaba da inganta zaman lafiya, tsaro da mulki na gari a Afrika, tare da yin aiki da Tarayyar Turai domin samun daidaito da kwanciyar...
A yammacin nan ne ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid za ta kece raini da Olympiacos a ci gaba da Gasar Zakarun Turai, duk da rashin wasu manyan ’yan wasanta biyu. Babban mai tsaron ragar Madrid, Thibaut Courtois, da ɗan wasan baya Dean Huijsen, na fama da jinya, lamarin da zai hana su buga wannan muhimmin wasa. Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu Yanzu haka jerin ’yan wasan Madrid da ke jinya sun haɗa da: Thibaut Courtois, Dean Huijsen, Antonio Rüdiger, David Alaba, Franco Mastantuono, da Éder Militão. Tun bayan zuwan sabon kocin Real Madrid, Xabi Alonso, Courtois ya riƙe ragamar tsaron raga a dukkan wasanni 17 da suka buga a...
Jakadan kasar Aljeriya a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya yayi tir da abin da ya kira zalunci isra’ila da kuma ci gaba da kai hare-hare kan mutane kasashen labanon, Syria, da Gaza da kuma gabar yammacin kogin jodan , yayi kira ga majalisar dinkin duniya da ta dauki mataken gaggawa wajen dakatar da wadannan hare haren, kuma akwai dubban laifuffukan da Isra’ila ta aikata da ba’a manta ba kuma ba’a dauki wani mataki a kai ba. Aljeriya ta yi wannan bayanin ne bayan karuwar sukar da ake yi a kwamitin tsaro game da mataken da isra’ila ke dauka a daidai lokacin da ake cikin matsala game da isar da taimakon agaji ga alummar gaza. A taron da kwamitin tsaro...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya. Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan. Shugaban ya bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an ’yan sanda 20,000, lamarin da zai ƙara adadin jami’an zuwa 50,000. Haka kuma, Tinubu ya bai wa rundunar sojin ƙasa da sauran hukumomin tsaro umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai. Sanarwar ta ce za a yi amfani da sansanonin masu yi wa ƙasa hidima NYSC a matsayin wuraren horas da sabbin ’yan sandan....
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya. Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan. Shugaban ya bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an ’yan sanda 20,000, lamarin da zai ƙara adadin jami’an zuwa 50,000. Haka kuma, Tinubu ya bai wa rundunar sojin ƙasa da sauran hukumomin tsaro umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai. Sanarwar ta ce za a yi amfani da sansanonin masu yi wa ƙasa hidima NYSC a matsayin wuraren horas da sabbin ’yan sandan....
Rahotanni sun bayyana cewa wasu masu dauke da makamai sun kama shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Sissoco Embalo a yau Laraba, kwanaki uku bayan da aka yi zaben shugaban kasa. Rahotannin sun ce an yi ta harbe harbe a babban birnin kasar, a yayin da Alummar kasar ke zaman jiran sakamako zagaye na farko na zaben shugaban kasa da aka yi a ranar Lahadi. Zuwa yanzu ba a tabbatar da ko su wane ne suka yi harbin ba. Rahotannin sun kuma ce an yi ta harbe harben a kusa da fadar shugaban kasar da ofishin hukumar zabe a yau Laraba, inda mutane suka tarwatse suna neman mafaka. A jiya Talata ne dai shugaban mai ci Umaro Sissoco Embalo, da babban...
Babban sakataren tsaron kasar Iran Dr Ali Larijani a shafinsa na X ya soki siyasar Amurka a lokacin ziyararsa a kasar Pakistan kuma ya jaddada cewa Tehran tana son ayi gaskiya a duk tattaunawa da za’a yi. Kalaman na larijani yana nuna matsayar iran ne kan diplomasiyar iyakoki, yace yanci da mallaka wasu abubuwa ne da babu sulhu a kansu, don haka duk wata tattaunawa da Amurka dole ne ta zama cikin yanci da daidaito, za’a iya tattaunawa amma ta gudana ba tare da nuna fifiko ba. Amurka tana kokarin nuna kanta a matsayin wadda za ta kawo sauyi a kowanne lamari na duniya, amma wannan wani nau’i ne na yaudarar kai, don haka mun yarda da tattaunawa ta gaskiya...
Shugaba Bola Tinubu ya aike da sunan mutum uku zuwa Majalisar Dattawa, domin tantance su a matsayin sabbin jakadan Najeriya. Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne, ya sanar da haka a zaman majalisar na ranar Laraba. Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna Waɗanda aka zaɓa su haɗa da Kayode Are daga Jihar Ogun, Aminu Dalhatu daga Jihar Jigawa da kuma Ayodele Oke. Bayan karanta takardar Tinubu, Akpabio ya ce, “Sunaye uku ne zuwa yanzu, tabbas sauran za su biyo baya.” Tun bayan ɗarewarsa kan mulki a 2023, Tinubu bai naɗa jakadu ba har yanzu. Mutane da dama sun daɗe suna ƙorafin kan jinkirin naɗa jakadun. Amma wasu na...
Sojoji a Guinea-Bissau sun ce sun yi juyin mulki tare da karɓe ragamar mulkin ƙasar. Sun kuma sanar da dakatar da zaɓukan ƙasar tare da rufe iyakokinta nan take. ’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS Wannan na zuwa ne kwana uku bayan ƙasar ta gudanar da zaɓen ’yan majalisa da na shugaban ƙasa. A yau ne aka wayi gari ana ji. harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa, lamarin da ya tashi hankalin mutane. Daga bisani kuma dakarun soji suka rufe babban titin da ke zuwa fadar shugaban ƙasar. A cewar majiyar AFP, sojojin sun karanta sanarwar ƙwace mulkin ƙasar a hedikwatar rundunar...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta bayyana sabbin nasarorin da ta samu wajen yaƙi da laifuka a jihar, ta hanyar holen mutum 34 da ta kama da aikata laifuka daban-daban. Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Rabi’u Muhammad, ya ce wannan ci gaba ya samu ne saboda sabbin dabarun aiki da kuma bayanan sirri da aka samu daga al’umma da hukumomin tsaro. Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000 A Anguwar Barnawa da wasu wurare a Kaduna, rundunar Operation Fushin Kada ta kama mutane 13 da ake zargi da aikata fashi da makami da satar wayoyi a otel-otel da gidaje. An ruwaito sun taɓa kashe...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta bayyana sabbin nasarorin da ta samu wajen yaƙi da laifuka a jihar, ta hanyar holen mutum 34 da ta kama da aikata laifuka daban-daban. Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Rabi’u Muhammad, ya ce wannan ci gaba ya samu ne saboda sabbin dabarun aiki da kuma bayanan sirri da aka samu daga al’umma da hukumomin tsaro. Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000 A Anguwar Barnawa da wasu wurare a Kaduna, rundunar Operation Fushin Kada ta kama mutane 13 da ake zargi da aikata fashi da makami da satar wayoyi a otel-otel da gidaje. An ruwaito sun taɓa kashe...
Daga Salihu Tsibiri Tsohon shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana tabarbarewar tsaro da ake fuskanta, wato ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma hare-haren ’yan bindiga, a matsayin barazana ga siyasar ƙasar nan gabanin zaɓen 2027. Ya yi wannan tsokacin ne a jawabinsa yayin bude zaman taron musamman na yini biyu da Majalisar Wakilai ta shirya kan halin tsaro da ƙasar ke ciki. Alhassan Ado Doguwa, wanda ya yaba da ayyukan da hukumomin tsaro ke ci gaba da gudanarwa, ya ce halin da Arewa ke ciki abin takaici ne ƙwarai, la’akari da yawan mutanen da ke hannun masu garkuwa da kuma waɗanda ke rayuwa cikin tsananin rashin tabbas. Tsohon shugaban ya jaddada cewa duk da cewa...
Jami’an tsaro a Jihar Kaduna, sun fara gudanar da babban samame domin kawar da ’yan ta’adda da ’yan bindiga a wasu ƙananan hukumomin jihar. A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce an gudanar da aikin tare haɗin gwiwar sojoji, DSS, NSCDC, KADVS, da kuma ƙungiyoyin sa-kai da mafarauta. Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000 Aikin ya shafi ƙananan hukumomin Makarfi, Hunkuyi da Ikara. Rundunar ta ce manufar wannan samame shi ne “share dukkanin maɓoyar miyagu, rushe sansanonin da suka kafa, da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankunan...
Hukumar tsaro ta DSS ta zargi dan jarida kuma mai shiga tsakani da ’yan ta’addar da suka sace fasinjojin jrigin kasan Kaduna-Abuja a shekarar 2022, Tukur Mamu, da karbar Naira miliyan 50 daga kudin fansar fasinjojin. Ana zargin Tukur Mamu da karbar kudin ne daga jagoran ’yan bindigar da ake kira da “Shugaba”. Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000 Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi Mamu na fuskantar tuhumar laifukan ta’addanci, ciki har da karɓar kuɗin fansa daga iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su a harin jirgin Kaduna na ranar 28 ga Maris, 2022, hulɗa da kuɗaɗen ’yan ta’adda, hana...
Da safiyar Yau Laraba ne sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila su ka kai hare-hare a yankuna daban-daban na zirin Gaza, tare da rushe gidaje da dama. Sojojin mamayar sun yi amfani da jiragen sama marasa matuki da kuma tankokin yaki domin rushe gidajen. A arewacin Gaza da gabashin Jabaliya sojojin na mamaya sun yi amfani da manyan bindigogi akan gidajen fararen hular. A unguwar “Tuffah” ma an ga yadda sojojin mamayar su ka aike da jiragen yaki marasa matuki. A can kudancin Gaza kuwa jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ne su ka kai hare-hare akan barin Bani-Suhaila a gabashin Khan-Yunus,a lokaci daya kuma manyan bingigoginsu su ka bude wuta akan iyaka. Tun bayan da aka tsagaita wutar yaki a cikin...
Majiyar ‘yan hamayyar siyasar kasar Uganda sun sanar da cewa, jami’an tsaron kasar sun kama magoya bayan Bobi Wine dake takarar shugabancin kasar 300 a tsawon yakin neman zabe. Mai magana da yawun Bobi Wine dan takarar shugabancin kasar ya fada a jiya Talata cewa; jami’an tsaron kasar sun kama fiye da mutane 300 da suke goyon bayansa tun da aka fara yakin neman zabe daga watan Janairu zuwa yanzu. Bob Wine wanda shahararren mawaki ne ya juye zuwa dan siyasa, yana yin takara a karo na biyu da shugaban kasar mai ci, Uweri Musaveni. A zaben 2021 Bob Wine wanda sunansa na yanke shi ne Robert Kyagulanyi,, ya zo na biyu. Kakakin jam’iyyarsa ta NUP,ya ce, a cikin wannan...
Reuters: Kungiyar Likitoci Ba Da Iyaka Ba Ta Fice Daga Asibitin Darfur Bayan Bude Wa Ma’aikatanta Wuta
Kungiyar ta kasa da kasa mai gudanar da a ayyukan agaji, ta sanar da janye ma’aikatanta daga asibitin Darfur, bayan da aka bude musu wuta, ya kuma kai ga kashe daya daga cikin masu aikin agaji. Kungiyar ta yi kira ga rundunar kai daukin gaggawa RSF da ta tabbatar da tsaro da kuma kiyaye lafiyar ma’aikatan agaji. Bugu da kari kungiyar ta ce mutumin da aka kashe a ranar 18 ga watan nan na Nuwamba ma’aikaci ne a ma’aikatar kiwon lafiya ta Sudan. Asibitin Zalnagi yana a jihar Darfur ta tsakiya ne da a halin yanzu ke karkashin ikon rundunar “RSF. A nata gefen, jami’a mai kula da tafiyar da ayyukan kungiyar ta “ Likitoci Ba Tare Da Iyaka Ba.” ...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Litinin ya ziyarci ɗaliban jihar da ke karatu a ƙasar Indiya, inda ya ba kowannen su tallafin Naira 500,000. Gwamnan, wanda ke ziyarar aiki a Indiya, ya fara ganawa da waɗanda suka ci gajiyar shirin tallafin karatu na jihar a Jami’ar Sharda da ke Noida. Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai Ya tabbatar musu da jajircewar gwamnatinsa wajen kula da walwalarsu domin samun nasarar karatunsu, sannan ya gargade su da su mai da hankali kan karatun nasu. Ya ce, “Na zo nan yau saboda dalili ɗaya,...
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya ce ko sisi gwamnati ba ta biya waɗanda suka yi garkuwa da ɗalibai mata 25 na sakandaren gwamnati ta Maga da ke jihar ba. Ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar a ranar Talata, inda ya tabbatar da kubutar da ɗaliban da aka sace a farkon makon nan. Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi Ya ce, “An karɓo ɗalibanmu da aka yi garkuwa da su a Maga. Shugaban ƙasa ya ba jami’an tsaro umarni su gano inda yaran suke, kuma su kubutar da su. Muna tabbatar wa...
Shugaban Iran ya sanar da cewa gwamnati na aiki don inganta juriya da ingancin tattalin arzikin kasar. Masoud Pezeshkian, Shugaban Iran, ya yi jawabi a taron Kasuwar Jarin Iran na shekara-shekara mai taken “Juriya, Kirkire-kirkire, Ci gaba,” yana mai jaddada gyare-gyaren manufofin tattalin arziki, kula da albarkatu, da kuma tallafawa masu zuba jari. Ya bayyana cewa gwamnati na aiki don rage cikas ga samar da kayayyaki da ciniki. Pezeshkian ya nuna muhimmancin yin tarurruka na wata-wata tare da masu zuba jari da masu samar da kayayyaki don nemo hanyoyin magance matsalolin da ake fuskanta. Ya kara da cewa, “Tanadin kashi 10% na iya adana ganga 800,000 zuwa 900,000 na mai a kowace rana.” Ya kuma nuna cewa samar da wutar...
Pars Today – Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, yana mai jaddada muhimmancin Pakistan a yankin, ya ce haɗin gwiwa tsakanin Tehran da Islamabad a fannoni daban-daban yana taimakawa wajen kawo kwanciyar hankali da zaman lafiya a yankin Ali Larijani, Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, ya ce da sanyin safiyar Talata da ya isa Islamabad cewa Pakistan muhimmiyar ƙasa ce a yankin kuma tana da matsayi mai kyau wajen tasiri ga yanayin tsaro na yankin. A cewar Pars Today, ya ƙara da cewa a matsayinta na maƙwabciyar gabas ta Iran, Pakistan ma tana taka rawa a al’adu, kuma dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu ta daɗe tana da zurfi kuma ta tarihi. Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Jamhuriyar Musulunci...
Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr Ali Larijan wanda ya ke ziyarar aiki na kwanaki uku a kasar Pakistan ya yabawa kasar saboda goyon bayan da ta bawa kasarsa a lokacin yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka dorawa kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Dr Ali Larijana yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Talata. Sannan yace ya isar da sakon gaisuwa na Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khami’ae ga mutanen kasar Pakistan. Banda haka ya gana da Firai ministan kasar Shehbaz Sharif da shugaban kasa Asif Ali Zardari da kuma kakakin majalisar dokokin kasar kasar Sardar Avaz Saadik. A ganawar Larijani da Sharif sun tattauna kan...
Jami’an tsaro na kasar Siriya karkashin gwamnatin rikon kwarya ta HKI sun budewa masu zanga zangar lumana wuta a yankunan bakin ruwa na kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a jiya Talata ce, a garuruwan Tartus, Lazikiyya da lardin Lantakiya mutane suka fito zanga zanga ta lumana inda suke neman adlci ga Alawiyawa da sauran kananan addinin da mazhabobi a yankin. Har’ila yau da sakin wadanda gwamnati take tsare da su. Amma jawabin gwamnatin Jolani ga masu zanga-zangar shi ne aman wutan bindigogi da hayaki mai sa hawaye a kama masu zanga-zangar da dukan wasu daga cikinsu. Labarin ya kara da cewa matsalolin tsaro sun tarbarbare a yankin bakin ruwa na kasar Siriya sosai, tare...
Shugaban kungiyar Ansar Allah a Yemen, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya aika da sakon ta’aziyya ga Sakatare Janar na Hezbollah, Sheikh Naim Qassem, kan shahadar babban kwamandan dakarun kungiyar Haitham Ali al-Tabtabai da abokansa. Huthi ya jaddada cewa laifin da aka aikata a kansu, tare da hare-haren da ake kai wa Lebanon da Zirin Gaza, yana nuna irin girman kai da Isra’ila ke da shi ne. Sayyed al-Houthi ya kara da cewa shahid al-Tabtabai ya yi kokari matuka wajen cimma manyan-manyan nasarori, kuma ya ba da gudummawa ga hanyar gwagwarmaya don taimakon gaskiya da wadanda aka zalunta, ya kara da cewa tasirin rawar da ya taka a cikin gwagwarmaya zai ci gaba da wanzuwa a cikin lamirin gwagwarmaya da zaluncin Isra’ila...
Wani mai magana da yawun rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (UNIFIL) ya tabbatar da cewa Isra’ila ta gina katanga kan iyakar da ta ratsa zuwa cikin yankin kasar Lebanon kusa da garin Yaroun, abin da tawagar ta bayyana a matsayin keta kudurin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701. “Isra’ila ta shafe shekaru da dama tana gina katanga a gefen Layin da aka Shata da ya raba yankunan Falastinu da Isra’ila ta mamaye da Lebanon, amma a cikin wannan yanayi katangar Isra’ila ta ratsa layin da ya raba bangarorin biyu,” in ji mai magana da yawun UNIFIL. “Don haka muna nuna rashin amincewa da wannan mataki, Wannan, a bayyane ya keta kuduri mai lamba 1701...
Jami’an tsaro na kasar Siriya karkashin gwamnatin rikon kwarya ta HKI sun budewa masu zanga zangar lumana wuta a yankunan bakin ruwa na kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a jiya Talata ce, a garuruwan Tartus, Lazikiyya da lardin Lantakiya mutane suka fito zanga zanga ta lumana inda suke neman adlci ga Alawiyawa da sauran kananan addinin da mazhabobi a yankin. Har’ila yau da sakin wadanda gwamnati take tsare da su. Amma jawabin gwamnatin Jolani ga masu zanga-zangar shi ne aman wutan bindigogi da hayaki mai sa hawaye a kama masu zanga-zangar da dukan wasu daga cikinsu. Labarin ya kara da cewa matsalolin tsaro sun tarbarbare a yankin bakin ruwa na kasar Siriya sosai, tare...
Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu
Jakadan kasar Aljeriya a MDD ya gabatar da jawabi a kwamitin tsaro na majalisar a jiya Talata, inda ya yi tir da hare-haren da HKI take ci gaba da kaiwa kan Gaza, da Lebanon duk tare da yarjeniyar da ta cimma na tsagaita wuta da kungiyoyin Hizbullah da Hamas. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Ammar Ben Jamaa jakadan kasar Aljeriya a MDD yana cewa HKI ba ta mutunta yarjeniyoyin da ta cimma da kasashen Larabawa a yankin, sannan masu shiga tsakanita da wadannan kungiyoyin sun kasa tabuka wani abu na ganin bangarorin biyu sun mutanen hakkin ko wani banagare. Jamaa ya kara da cewa a halin yanzu HKI tana kai hare-hare a kan kasashen larabawa da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A cikin ‘yan shekarun nan, batun garkuwa da mutane ya zama babban kalubale ga tsaro a Najeriya da wasu ƙasashen duniya. Lokacin da mutane suka fada hannun masu garkuwa, iyaye da ‘yan uwa sau da yawa suna fuskantar babban zabi mai wahala: biyan kudin fansa don sakin wanda aka sace ko tsayawa da kafafun tsaro har zuwa samun taimakon hukumomi. Shin ko ya kamata alumma su cigaba da biyan kudin fansa idan an yi garkuwa da ‘yan uwansu? NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Wannan shine batun da shirin Najriya A Yau...
’Yan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla mutum 11 mazauna garin Isapa da ke kusa da Eruku a Ƙaramar Hukumar Ekiti ta Jihar Kwara. Harin ya faru ne sa’o’i kadan bayan sakin wasu masu ibada da aka yi garkuwa da su suna tsaka da ibada a coci. An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi A cocin CAC da ke Ekuru, ana gudanar da bikin godiya domin murnar ’yantar da mambobi 18 da aka yi garkuwa da su kusan wata guda da ya gabata, sai ’yan bindiga suka kutsa suka yi garkuwa da mutum 38 bayan sun harbe uku har lahira. Sabon harin, wanda ya faru da misalin...
Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr Ali Larijan wanda ya ke ziyarar aiki na kwanaki uku a kasar Pakistan ya yabawa kasar saboda goyon bayan da ta bawa kasarsa a lokacin yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka dorawa kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Dr Ali Larijana yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Talata. Sannan yace ya isar da sakon gaisuwa na Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khami’ae ga mutanen kasar Pakistan. Banda haka ya gana da Firai ministan kasar Shehbaz Sharif da shugaban kasa Asif Ali Zardari da kuma kakakin majalisar dokokin kasar kasar Sardar Avaz Saadik. A ganawar Larijani da Sharif sun tattauna kan...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta kammala shirye-shiryen yi wa yara sama da miliyan daya da rabi ‘yan ƙasa da shekaru biyar allurar rigakafin shan inna zuwa karshen watan Nuwamba a jihar. Shugaban Hukumar Kula Lafiya a Matakin Farko ta Jihar (JSPHCDA), Dakta Shehu Sambo, ya bayyana haka a taron tattaunawa da manema labarai na yini guda da aka shirya, tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, a Dutse, babban birnin jihar. Dakta Sambo, wanda Mataimakin Mai wayar da kan jama’a na hukumar, Malam Nura Ado ya wakilta, ya ce ana sa ran adadin yara 1,516,244 ne za a yi wa rigakafin a wannan watan. Ya ƙara da cewa rigakafin...
An ceto ’yan matan nan 24 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Makarantar sakandaren Gwamnati ta GGCSS da ke yankin Maga da ke Jihar Kebbi. Gwamnan jihar Kebbi Nasiru Idiris a taron manema labarai a ranar Talata fadar gwamnatin jihar ya tabbatar da an karɓo ɗalibban da aka sace a farkon makon nan. Ya ce “an karɓo ɗiyanmu ’yan makaranta waɗanda aka yi garkuwa da su a Maga. Shugaban ƙasa ya baiwa jami’an tsaro umarni a tafi a gano inda yaran suke kuma a karɓo su muna tabbatar wa uwayen yara da al’ummar Kebbi yara sun dawo. “Muna godiya ga shugaban ƙasa da jami’an tsaro musamman sojoji da ’yan sanda da Sibil difens da sauransu da suka...
Daga Bello Wakili Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa dawowar ’yan mata 24 da ’yan ta’adda suka sace a Maga, Jihar Kebbi. ’Yan ta’addan sun kai hari makarantar ranar 17 ga wantan Nuwamban 2026, inda suka yi awon gaba da ’yan matan, jim kaɗan bayan wata rundunar soji ta bar harabar makarantar. Lamarin Kebbi ya haifar da wasu sace-sace makamanta a Eruku da ke Jihar Kwara da kuma Papiri a Jihar Neja. An sako dukkan mutune 38 da aka sace a Eruku ranar Lahadi, inda a wannan ranar ce shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Jihar Neja ya ce an samu yara 50 daga cikin ɗaliban makarantar Katolika da suka ɓace a gidajen iyayensu. Shugaba Tinubu ya...
Babbar Mai Shari’ar ta kasa , Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta jaddada cewa alkalai suna da nauyin tabbatar da adalci cikin gaskiya da daidaito a lokacin da matsalolin tattalin arziki ke kara tsananta wa al’umma. Ta bayyana haka ne a Taron Alkalai na Shekara-shekara Karo na 26, wanda Cibiyar Nazarin Shari’ar Musulunci ta Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) ta shirya tare da haɗin gwiwar Cibiyar Koyar da Ayyukan Shari’a ta Kasa (NJI), a harabar Jami’ar da ke Kongo, Zariya. Mai Shari’a Kekere-Ekun, wadda Sakatare na NJI, Barista Abdulazeez Aluwo ya wakilta, ta ce dole ne kotuna su yi hukunci da ke la’akari da yanayin tattalin arziki da kuma hakkokin masu nema da wadanda ake binsu hukunci. Ta ce hakan ne kadai...
Mahukunta a Jakarta, babban birnin Indonesia, sun haramta sayarwa da cin naman karnuka, kyanwa da jemagu, a wani yunƙuri na daƙile yaɗuwar cutar nan ta Mahaukacin Kare da a Turance ake kira rabies. Da yake jawabi a wannan Talatar, Gwamnan Jakarta, Pramono Anung, ya sanar da rattaba hannu kan dokar da ke hana duk wani nau’in kasuwanci ko mu’amala da waɗannan dabbobi a matsayin abinci. An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara ba Dokar wadda za ta fara aiki bayan wa’adin watanni shida, ta ayyana cewa duk wanda ya karya ta zai iya fuskantar hukunci daga kan gargaɗi na rubuce har zuwa janye lasisin kasuwanci...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2026 na sama da naira biliyan 900 ga Majalisar Dokokin jihar. Yayin gabatar da kasafin da aka lakaba wa suna “Kasafin Kirkire-kirkire da Sauyi Don Cigaban Jigawa II,” Gwamna Namadi ya ce za a ware sama da naira biliyan 693.4, wanda ya kai kimanin kashi 76 cikin 100, don ayyukan raya kasa. Gwamnan ya kuma ce sama da naira biliyan 208 za su tafi ne ga ayyukan yau da kullum. A cewarsa, an ware sama da naira biliyan 310 ga bangaren ilimi da lafiya, yayin da kimanin naira biliyan 186 za su tafi ga hanyoyi da sufuri. Malam Umar Namadi ya ƙara...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta samu nasara a wasan mako na 14 na Nigeria Premier Football League (NPFL), bayan da ta doke Ikorodu City da ci 2–1 a filin wasa na Muhammad Dikko, da ke birnin Katsina. Wannan ita ce nasara ta uku da Pillars ta samu a kakar bana, cikin wasanninta 14, inda ta yi kunnen doki uku, sannan ta sha kashi shida. ’Yan bindiga sun yi yi garkuwa da mutane 11 a Kwara Chelsea za ta kece raini da Barcelona a Gasar Zakarun Turai Kafin wannan wasan, Kano Pillars ta yi wasanni takwas a jere ba tare da samun nasara ba. Pillars ta zura kwallayenta ne ta hannun Rabiu Ali, wanda ya zura ta farko a...
Taron koli karo na 7 na tarrayar Turai da tarayyar Afrika, wanda aka bude a Luanda, na maida hankali kan batun diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi a karon farko. A cewar ajandar taron, daya daga cikin manyan jigogi zai mayar da hankali kan diyya ta kudi da siyasa da ta shafi zaluncin mulkin mallaka da cinikin bayi, gami da lalacewar tattalin arziki, da al’adu da aka tara tsawon shekaru da dama. Wannan lokaci ne da ba a taba ganin irinsa ba a wannan matakin siyasa: ba a taba sanya irin wannan batu a cikin ajandar taron da ya hada shugabannin kasashen Turai da Afirka ba. Kungiyar Tarayyar Afirka ta ware shekarar 2025 a matsayin shekarar “Adalci...
Hizbullah: Isra’ila na kuskure idan ta na tunanin kashe-kashen kwamandodinmu zai kawo karshen kungiyar
Kungiyar Hizbollah ta kasar Lebanon ta bayyana cewa Isra’ila na yin kuskure idan ta na tunanin kashe-kashe da kisan gillar da ake wa mambobi da kwamandojinta zai kawo karshen kungiyar. Wannan na zuwa ne bayan kisan gillar da Isra’ila ta yi wa babban kwamandan sojin kungiyar da wasu makusantansa a ranar Lahadi, a wani hari da ta kai a kudancin babban birnin Lebanon. Haitham Ali Al-tabataba’i da aka fi sani da Abu Ali, ya yi shahada ne tare da wasu dakarun hizbullah guda 4 a wani mummunan hari da Isara’ila ta kai a heret hareik dake kudancin birnin beirut. Tabataba’I yana daya daga cikin jajircaccen dakarun kungiyar hizbullah , kuma ya taka rawa sosai wajen tsarin tsaron kungiyar tun shekarun...
Tashar Talabijin ta Press TV ta Iran ta kaddamar da sabon sashenta na harshen Hebrew don isa ga masu sauraro na Yaren Hebrew na duniya. Yanzu ana iya samun wannan sashen ta hanyar asusun X (@PresstvHebrew) da kuma tashar Telegram (@PresstvHebrew), kuma Za a kaddamar da cikakken shafin Intanet na tashar nan ba da jimawa ba. Sashen na Hebrew zai rika bayar da labarai, binciken kwakwaf, da sharhi kan abubuwan da suke faruwa a yankin da ma duniya baki daya. A cewar Ahmad Norouzi, darektan sashen watsa labarai a bangaren harsunan ketare na Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRIB), ya bayyana cewa babban aikin tashar shi ne fallasa gaskiyar duk abinda jami’an Isra’ila ke neman boyewa, gami da takunkumin da aka...
Adadin Falasdinawan da aka kashe a yakin kisan kare dangi na Isra’ila a Gaza na iya zama mafi girma fiye da yadda aka kiyasta a baya, in ji rahoton jaridar Die Zeit ta Jamus ta mako-mako. A bisa ga kiyasin masu binciken, tsakanin Falasdinawa 99,997 da 125,915 ne aka kashe a Gaza a cikin shekaru biyu na farko na yakin. Masana kimiyya a Cibiyar Max Planck sun tattara bayanai daga majiyoyi da yawa kafin su bayyana kididdigar. Baya ga alkaluman da Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta fitar, sun hada wani bincike mai zaman kansa na gida da rahotannin mace-mace da aka buga a shafukan sada zumunta. Duk da haka, asibitoci da yawa sun daina aiki yadda ya kamata a lokacin...
Hukumar kula da makarantun firamare da sakandare ta Jihar Katsina ta sanar da sake buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarabawar zangon farko na shekarar karatu. A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Sani Danjuma Suleman, ya fitar a madadin Shugaban hukumar, ta ce makarantun firamare, sakandiren je-ka-ka-dawo da kuma makarantu masu zaman kansu za su buɗe daga yau Talata domin ci gaba da jarabawar zangon farko. Sanarwar ta ƙara da cewa, sauran makarantun kwana za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai lokacin da hali ya ba da dama. Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne Gwamnatin Katsina ta rufe makarantun bayan ƙaruwar hare-haren sace ɗalibai da masu garkuwa da mutane suka...
’Yan Majalisar Tarayya daga yankin Kudu sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, afuwa bayan da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai. Kungiyar ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu maso Gabas ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi, wajen yi wa Nnamdi Kanu afuwa wanda kotu ta same shi da laifin ta’addanci. Alƙali James Omotosho na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ne ya yanke hukuncin, inda ya same shi da laifi a kan tuhumar da ake masa guda bakwai, sannan ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Tuni aka tura Nnamdi Kanu...
Rahotanni na cewa ’yan bindiga sun sace wasu mutum takwas a garin Biresawa da ke Karamar Hukumar Tsanyawa ta Jihar Kano a daren jiya na Litinin. Wata majiyar da ta tabbatar da lamarin ta shaida wa Aminiya cewa maharan sun shiga garin tsakanin 11 na dare zuwa 12 na tsakar dare, inda suka yi awon gaba da maza biyu da mata shida. ’Yan bindiga sun yi yi garkuwa da mutane 11 a Kwara Chelsea za ta kece raini da Barcelona a Gasar Zakarun Turai Wani ɗan uwa ga waɗanda aka sace, Kabiru Usman, ya ce maharan sun zo ne a ƙafa ɗauke da makamai, suka kuma yi garkuwa da matarsa Umma, ɗiyarsa mai shekara 17, da matar ɗan’uwansa da wasu...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea za ta karɓi baƙuncin Barcelona a wasan mako na biyar na gasar cin Kofin Zakarun Turai (Champions League) da ke ci gaba da gudana a kakar nan. Wasan da za a buga a filin Stamford Bridge, yana zuwa ne bayan da ’yan wasan Barcelona suka ƙauracewa atisayi a bainar jama’a domin ɓoye salon horon su. Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina Matsalar Tsaro: Gwamnonin Arewa sun shirya taron gaggawa Chelsea da Barcelona sun haɗu sau 14 a gasar Zakarun Turai, inda kowacce ƙungiyar ta yi nasara huɗu, sannan aka yi kunnen doki shida. Wannan shi ne karo na farko da ƙungiyoyin za su kara tun kakar 2017/18...
Daga Musa kutama , kalaba Hasana Aminu matashiyar jaruma ce a Masana’antar Kannywood, wacce ta fito a finafina da dama ciki har da fim xin A Duniya da wasu fitattun finafunan Hausa. A zantawarta da Aminiya, Hasana Aminu wadda aka fi sani da suna Nabila ta ce, a halin yanzu tana tauna taura biyu ne a baka Ga yadda girar su ta kasan ce: Sunan Jarumar? Sunana Hasana Aminu, amma an fi sani na da suna Nabila a Masana’antar Kannywood da ke Kano Ta yaya kike gwama karatu da kuma kasuwanci da harkar fim? Eh, to farko ko da na shigo Masana’antar Kannywood sai na ga ai ashe ma ina da damar da zan iya yin karatu yayin da kuma...
’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 11, ciki har da wat mai juna biyu da ƙananan yara Jihar Kwara. Maharan sun kai farmaki tare da sace mutanen ne a yankin Eruku da ke Ƙaramar Hukumar Ekiti da ke jihar. Ƙarin bayani na tafe…
Gwamnonin jihohin Arewa 19 za su gudanar da muhimmin taro a ranar Asabar, 29 ga Nuwamba, domin tattauna matsalolin tsaro da suka addabi yankin. Mai bai wa Gwamnan Nasarawa shawara na musamman kan harkokin jama’a, Peter Ahemba, ne ya sanar cewa, taron gwamnonin Arewa da aka shirya a Kaduna zai samu halartar manyan sarakunan gargajiya. “Manufar taron ita ce samar da matsaya ɗaya wajen fuskantar matsalolin tsaro da ke damun yankin, tare da tsara hanyar magance su,” in ji shi. Ya ƙara da cewa, za a yanke muhimman shawarwari a taron domin tabbatar da tsaron yankin. ’Yan Majalisar Kudu sun roƙi Tinubu ya yi wa Nnamdi Kanu Afuwa Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu...
Hukumar da take kula da harkokin watsa labaru a kasar Mali ta sanar da dakatar da ayyukan wasu kafafen watsa labarun kasar Faransa biyu a cikin kasar. Wadannan kafafen watsa labarun dai su ne LCI da TF1 saboda zarginu da watsa gubatattun labaru akan matsalar makamashi da ake fama da ita. TF1 dai tashar talabijin din Faransa ce mai zaman kanta da take watsa shirye-shiryenta a kasashe mabanbanta. Ita kuwa LCI ( La Chaine Info) tashar labarai ce wacce take a karkashin TF1. Hukumar dake kula da sanarwa a cikin kasar ta Mali ( HAC) ta rubuta wata wasika zuwa ga kafafen watsa labaru a ranar 13 ga watan Nuwamba wacce kuma a wannan makon mai karewa ne aka fito...