ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa October 24, 2025 Daga Birnin Sin An Shirya Harba Kumbon Shenzhou-21 A Kwanan Nan October 24, 2025 Daga Birnin Sin Shugaba Xi Ya Jagoranci Zaman Jin Ra’ayoyin Wadanda Ba ‘Yan JKS Ba Game Da Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15  October 24, 2025

.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ko Alassane Ouattara zai samu wa’adi na 4 a mulkin Ivory Coast?

Shugaban ƙasa mai ci, Alassane Ouattara, shi ne wanda aka fi yi wa hasashen nasara a zaɓen da za a gudanar a Ivory Coast ranar Asabar, sakamakon rashin wasu jiga-jigan ’yan adawa da za a fafata da su a zaɓen.

Ouattara, mai shekara 83, yana riƙe da madafun iko tun daga shekarar 2011, lokacin da ƙasar ta fara warwarewa daga rikicin siyasa kuma ta kasance ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ke taka rawa wajen bunƙasar tattalin arzikin yammacin Afirka.

Jerin ’yan wasan da ke takarar lashe kyautar gwarzon Afirka na bana Idan Tinubu ya gaza zai yi wuya a samu shugaban da zai yi nasara — Shehu Sani

A ƙarƙashin mulkinsa, Ivory Coast — wacce ita ce babbar mai fitar da koko a duniya — ta samu ci gaba a fannoni da dama, kodayake masu suka na ganin tsawon lokacin da ya shafe a karagar mulki na iya ƙara raba kawunan ’yan ƙasar.

Alassane Ouattara na da damar samun tazarce, a yayin da manyan abokan hamayyarsa ciki har da tsohon shugaban ƙasa Laurent Gbagbo da tsohon shugaban bankin Credit Suisse, Tidjane Thiam — duka an hana su tsayawa takara.

A halin yanzu dai ‘yan adawa huɗu Majalisar Tsarin Mulki ta sahalewa takara, inda ta cire Gbagbo da Thiam daga jerin ’yan takarar tana mai ba da dalilin cewa an goge sunayensu daga rajistar zaɓe.

Bayanai sun ce an hana Thiam tsayawa takara ne saboda matsalolin shari’a da suka shafi batun ƙasa da ƙasa, musamman kan yadda ya samu shaidar zama ɗan ƙasar Faransa a matsayin ƙasarsa ta biyu.

A gefe guda kuma, Gbagbo an hana shi shiga takara ne saboda hukuncin da aka taɓa yanke masa a kotu.

A ranar Laraba, Gbagbo ya soki zaɓen da ke tafe yana mai bayyana shi a matsayin “juyin mulki na farar hula” da kuma “satar zaɓe.”

Da yake magana da gidan jaridar AFO Media na Pan-Afirka, tsohon shugaban ƙasa Laurent Gbagbo ya bayyana goyon bayansa ga masu zanga-zangar da ke “adawa da wannan satar zaɓen.”

Rashin halartar fitattun shugabannin adawa irin su Gbagbo da Tidjane Thiam ya ƙara tayar da ƙura a harkar siyasar ƙasar, lamarin da ya jawo tashin hankalin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane huɗu ’yan kwanakin nan — ciki har da ɗan sanda ɗaya.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa, a ranar Talatar da ta gabata ce wani mutum ya rasa ransa yayin da yake taimaka wa jami’an tsaro rushe shingayen da aka kafa a kusa da birnin Yamoussoukro, babban birnin mulkin ƙasa, wanda ke zama cibiya mai ƙarfi ga ’yan adawa.

A wannan yankin dai an toshe hanyoyi da dama yayin da yanayin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi gabanin zaɓen da ke tafe.

Haka kuma, a ranar Litinin ce aka ƙone wani ginin hukumar zabe mai zaman kanta ƙurmus, inda tuni mahukunta suka hana ’yan adawa gudanar da gangami ko taruka, suna cewa hakan na iya barazana ga tsaron jama’a.

Haramta Gangami

Aƙalla jami’an tsaron ko ta kwana 44,000 aka jibge a fadin ƙasar domin daƙile yiwuwar ɓarkewar zanga-zanga, musamman a yankunan kudu da yammacin ƙasar da ake ganin su ne cibiyoyin magoya bayan adawa.

A cikin ’yan makonnin nan, sama da mutane 700 aka kama, wasu bisa zargin aikata “ta’addanci,” a cewar lauyan gwamnati Oumar Braman Koné, yayin da kusan mutum 30 aka yanke musu hukuncin shekaru uku a gidan yari saboda ta da zaune tsaye da karya doka.

Hukumomin ƙasar sun bayyana cewa ba za su bari “rikici” ya sake faruwa kamar yadda aka gani a zaɓen shekarar 2020, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 85.

“Gwamnati tana ɗaukar matakan tsaro na kariya don kauce wa tashin hankali a lokacin zaɓe. Amma hanya mafi inganci ta gudanar da zaɓe cikin lumana ita ce a shirya zaɓen da ya haɗa kowa,” in ji masanin siyasa Geoffroy Kouao.

’Yan adawa 4 da za su ƙalubalanci Ouattara

Guda cikin ’yan takarar da ake ganin za su ƙalubalanci Ouattara a zaɓen na ranar 25 ga wata akwai Simone Gbagbo mai shekaru 76, wato tsohuwar matar tsohon shugaba Laurent Gbagbo, wanda ya jagoranci ƙasar a lokacin yaƙin basasar da ya faru tsakanin shekarar 2002 zuwa 2007.

Simone tana tare da Gbagbo lokacin da ya ƙi sauka daga mulkin ƙasar bayan shan kaye a zaɓen 2010, wanda ya kai ga rikicin da ya sabbaba mutuwar mutane aƙalla dubu 3, gabanin kame Simone da Gbagbo cikin watan Afrilun 2011 tare da gurfanar da su gaban kotun hukunta manyan laifuka ta ICC.

Sai dai Simone ta samu sassauci ganin cewa an yi mata shari’a ne a cikin gida ba tare da zuwa Hague ba, saɓanin mijin nata, inda aka yanke mata hukuncin shekaru 20 a gidan yari gabanin afuwar da shugaba Ouattara ya yi mata a shekarar 2018, inda a shekarar 2023 kuma ta kawo ƙarshen aurenta da Gbagbo, tare da jagoranta jam’iyyarta ta daban wanda ƙarƙashinta yanzu haka ta ke takara.

Na biyu a jerin ’yan takarar akwai Jean-Louis Billon mai shekaru 60 da ke wakiltar jam’iyyar Democratic Congress wadda haɗaka ce ta jam’iyyu 18 da suka haɗe waje guda domin ƙalubalantar Ouattara ta hanyar wakilta Billon, wanda tsohon ministan kasuwanci ne kuma na hannun daman madugun adawa Tidjani Thiam da aka haramtawa tsayawa takara a zaɓen na bana.

Na ukun shi ne Ahoua Don Mello mai shekaru 67 kuma tsohon kakakin Laurent Gbagbo yayin rikicin zaɓen 2010 zuwa 2011, kuma yanzu haka yana takara ne a raɗin kansa ba tare da jam’iyya ba, bayan jam’iyyar tsohon shugaba Gbagbo ta kore shi sakamakon aniyar da ya bayyana ta tsayawa takara a wannan zaɓe, kuma ana ganin yana da tasirin da zai iya yiwa Ouattara ɓarna a wannan zaɓe.

Ta ƙarshe a jerin waɗannan ’yan takara, ita ce Henriette Lagou Adjoua, tsohuwar Ministar Mata mai shekaru 66 wadda ta taɓa takara a shekarar 2015 tare da Ouattara amma ta samu ƙasa da kashi 1 na yawan ƙuri’un da aka kaɗa.

Sai dai a wannan karon ana ganin Adjoua ta samu ƙarin magoya baya sakamakon fafutukar da ta ke ci gaba da yi wadda ke tir da matakin ƙyamar mata a madafun iko cikin har da littafin da ta rubuta mai suna Why Not a Woman, wanda kai tsaye ke ƙalubalantar rashin baiwa mata damar shugabanci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnan Neja ya ba dukkan iyalan wadanda suka kone a gobarar tankar mai N1m
  • Ƙarfin Niyyar Manzon Allah (SAW) Da Matakinsa Na Aƙlul A’ala
  • Albanese: Wajibi A Kawo Karshen Gwamnatin Mamaya A Falasdinu
  •   Venezuela Ta Sanar Da Mallakar Makamai Masu Linzami Samfurin “ Igla-s” 5,000 Domi  Kare Kanta
  • Tun da PDP ta bar mulkin Najeriya maguɗin zaɓe ya ragu – Akpabio
  • Ko Alassane Ouattara zai samu wa’adi na 4 a mulkin Ivory Coast?
  • Zimbabwe Ta Jinjinawa Jarin Sin A Matsayin Wanda Ya Bunkasa Masana’atun Samar Da Siminti A Kasar
  • Gwamnatin Borno rufe makarantun jihar saboda rigakafin ƙyanda da Polio
  • Masu kwacen waya sun kashe ma’aikaciyar lafiya a Zariya