HausaTv:
2025-09-17@23:08:34 GMT

Sheikh Kassim: Mayakan Hizbullah Mazajen Fagen Daga Ne

Published: 6th, July 2025 GMT

Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’ima Kassim ya bayyana cewa; Dakarun Hizbullah mazajen fagen daga ne da ba su karbar kankanci.

Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a wurin babban taron Ashura a ungiyar Dhahiya dake birnin Beirut, ya bayyana cew; Yaki na tsaron kasa zai ci gaba saboda mun yi Imani da ‘yanto da kasa, kuma wajibi ne akansu, ko da kuwa an dauki lokaci mai tsawo sannan kuma sadaukar da kai ya yawaita.

Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Isra’ila abokiyar gaba tana ci gaba da mamaye yankuna 5 na Lebanon, don haka babu yadda za a yi mu mika kai.” Haka nan kuma ya yi tambayar cewa; Ta yaya za a tsammaci za mu ki tsayuwar daka a gaban wannan abokin gfabar wanda yake ci gaba da mamaye kasa da kuma kisa?

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma kara da cewa; gwagwarmaya za ta ci gaba, kuma zuriya mai zuwa za su dora daga inda aka tsaya.”

Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce:  Za mu kare gwagwarmayar da mutane masu yawa su ka sadaukar da kawunansu akanta, domin wannan gwagwarmaya ce ta Imam Musa Assadar, kuma ta Sayyid Hassan Nasrallah shugaban shahidan wannan al’umma.”

Da yake Magana akan yadda HKI take keta wutar yaki, Sheikh Na’im Kassim ya ce; yawan keta wutar yakin Isra’ila ya kai dubban gomomi, ya kuma kara da cewa; Batun da ake yi na wata sabuwar yarjejeniya ba zai sa mu mika wuya ba, abinda ya kamata shi ne a fada wa abokan gaba cewa; Su daina keta wutar yaki, sannan kuma gwgawarmaya tana cikin hanyoyin magance matsalar da ake fuskanta.”

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe

Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Yobe (ALGON) ta karrama Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, da lambar yabo ta karramawa bisa himmar ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ke gudanarwa a faɗin jihar.

Karramawar, wacce aka bayyana a matsayin irinta ta farko a tarihin Jihar Yobe, shugabannin ƙananan hukumomi 17 na jihar suka ba da ita ga gwamna.

Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno

Da yake jawabi, shugaban ƙungiyar ALGON a Jihar Yobe, kuma shugaban ƙaramar hukumar Damaturu, Alhaji Bukar Adamu, ya yaba da yadda Gwamna Buni yake gudanar da harkokin mulki na bai ɗaya. Ya ce nasarorin da aka samu sun haɗa da fannoni na ilimi, noma, kiwon lafiya, kasuwanci, da samar da ababen more rayuwa.

“Babu wani sashe a jihar da aka bari a baya a cikin ayyukan ci gaban da Gwamna Mai Mala Buni ke aiwatarwa,” in ji Adamu.

A nasa martanin, Gwamna Buni, wanda mataimakinsa, Alhaji Idi Barde Gubana, ya wakilta, ya karɓi karramawar a matsayin “hanyar mayar da martani mai ƙarfi” da ke tabbatar da tasirin gwamnatinsa a matakin farko.

Ya kuma yi alƙawarin ci gaba da ƙoƙarin kai Yobe matsayin jiha da za ta iya gogayya da takwarorinta a fagen ci gaban ƙasa.

Wakilinmu ya ruwaito cewa taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, ’yan siyasa daga ciki da wajen jihar, da kuma sarakunan gargajiya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • Chadi:  Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa  damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa
  • ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
  • Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
  • ’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote
  • Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila
  • Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 
  • ’Yan sanda sun sasanta rikicin asibitin AKTH da KEDCO
  • Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta
  • Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki