Al-Houthi: Matsin lamba bai hana Iran ci gaba da goyon bayan Falasdinu
Published: 18th, October 2025 GMT
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yaman Sayyid Abdul-Malik Badreddin al-Houthi ya yi jawabi a yammacin yau alhamis kan batutuwa daban-daban da suka shafi duniyar musulmi, musamman abubuwan da suka faru a Gaza da Yemen. Ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ba tare da la’akari da duk wani matsin lamba ba, ta yi sadaukarwa ta karshe a kan turbar goyon bayan Falasdinu, kuma ta bayar da dama ga kwamandojin gwagwarmayar ‘yanci, daga cikinsu akwai babban kwamandan shahidi Qassem Soleimani.
Yayin da yake magana kan zagayowar shahadar babban kwamanda Yahya al-Sinwar, Sayyid Abdul-Malik Badreddin ya ce: “Babban darussan da ya bari na tsararraki, da kuma matsayinsa na sadaukar da kai da jihadi, suna wakiltar muhimman dabi’u da kuma babban matakin wayar da kan jama’a, wanda hakan ya samar da wata mazhaba mai karfafa gwiwa ga tsararraki.
Har ila yau jagoran Ansarullah ya mika sakon taya murna da ta’aziyyar shahadar shahidan Ghamari (Babban Hafsan Sojin Yaman) zuwa ga iyalansa, da ‘yan uwansa, da dukkan ‘yan’ yanci. Ya kara da cewa, Shahidai al-Ghamari ya taka rawa sosai wajen tallafawa Gaza, kuma tun bayan shahadarsa ‘yan uwansa suka ci gaba da yin jihadi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Marzieh Jafari Ta Dauki Lambar Yabo Ta Horar Da Mata Wasan Kwallon Kafa Ta Nahiyar Asia October 18, 2025 Iran: Kudurin Kwamitin Tsaro Kan Yarjeniyar JCPOA Ya Kawo Karshe A Yau October 18, 2025 Iran: Kauyuka 3 Sun Shiga Cikin Wuraren Bude Ido Na Duniya October 18, 2025 Aref: Kofar Tattaunawa A Bude Take, Amma Ba Zamu Amince Da Bukatun Da Basa Da Ma’an Ba October 18, 2025 Kenya Ta Yiwa Raila Odinga Jana’iza Ta Musamman October 18, 2025 Kwamandan Rundunar Kudancin Amurka ya sanar da murabus kan batun ayyukan soji a yankin Caribbean October 18, 2025 Janar Sulaimani: A Yayin Yakin Kwanaki 12 Iran Ta Tarwatsa Wasu Muhimman Wurare 21 Na Isra’ila October 17, 2025 Abokan Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya Sun Ce: Sake Dawo Da Takunkumin Da Aka Kakaba Kan Iran Baya Kan Doka October 17, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Wuce Gona Da Irin Isra’ila Kan Kudancin Kasar Lebanon October 17, 2025 Kungiyar Hamas Ta Yi Kira Da Matsa Wa Isra’ila Lamba Da Ta Cika Sharuddan Yarjejeniyar Gaza October 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Akwai yiwuwar matsin lamba ya sa Tinubu cire sunayen wasu da ya yi wa afuwa saboda cece-kuce
Rahotanni na nuna cewa akwai yiwuwar Shugaban Kasa Bola Tinubu ya cire wasu sunaye daga jerin wadanda ya yi wa afuwa bayan cece-kucen da hakan ya jawo.
Hakan dai ya biyo bayan ci gaba sukar lamirin hakan da jama’a ke yi, musammam kan saka wasu rikakkun masu laifi da kotu ta yanke wa hukunci daban-daban.
Saudiyya ta zaftare wa Najeriya guraban Aikin Hajji da sama da kujeru 28,000 ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 8 a harin kwanton ɓauna a ZamfaraAfuwar shugaban kasa da ake bayarwa a lokutan bukukuwan ƙasa, ana yin ta ne don rage cunkoso a gidajen yari da kuma ƙarfafa sulhu da haɗin kai.
Sanarwar fadar shugaban kasa ta ce an yanke shawarar ne bisa shawarwarin Kwamitin Shawara na Shugaban Ƙasa kan Afuwa, wanda Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi ke jagoranta.
Sai dai wannan lamari ya sake tayar da cece-kuce kan gaskiya da sahihancin tsarin afuwar Najeriya.
Amma a ranar Alhamis, Ministan na shari’a ya ce afuwar da shugaban kasa ya sanar ba a kammala tantance ta ba, kuma har yanzu akwai sauran matakan da ba a kammala cikawa ba.
Cece-kuce na ci gaba da tasowa kan wasu sunaye da aka haɗa a ciki, inda hukumar EFCC, ICPC da NDLEA da sauran hukumomin tsaro suka fara kokarin dakatar da sakin wasu daga cikin waɗanda ke cikin sunayen.
A taron Majalisar Koli da aka gudanar a ranar 9 ga Oktoba, 2025, fadar shugaban kasa ta shelanta sunayen mutum 175 da aka yi wa afuwar, ciki har da masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, masu laifukan ofis, masu laifukan miyagun ƙwayoyi, Manjo-Janar Mamman Vatsa, Farfesa Magaji Garba, Ken Saro-Wiwa, mutanen Ogoni, Maryam Sanda da ma wasu da dama.
Yayin da sunayen wasu ’yan siyasa kamar Herbert Macaulay da Farouk Lawan ba su haifar da cece-kuce ba, haɗa sunayen masu laifukan tashin hankali da karya doka ya jawo fushi daga jama’a.
Daya daga cikin sunayen da suka jawo cece-kuce shi ne Maryam Sanda, wacce aka yanke wa hukuncin kisa a 2017 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello.
Yayin da wasu daga cikin iyalan marigayin suka ƙi amincewa da afuwar, Alhaji Bello Isa (mahaifin mamacin) da Alhaji Garba Sanda (mahaifin Maryam) sun gudanar da taron manema labarai don karɓar afuwar ta shugaban kasa.
Shugaban kasa ya kuma yi wa Major S. Alabi Akubo afuwa, wanda aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai kan mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, da kuma Kelvin Prosper Oniarah, wanda aka danganta da hare-haren garkuwa da mutane a jihohin Delta, Edo, Ribas, Abia, Binuwai da Oyo, inda aka gano sansanoninsa na tsare mutane a Warri, Kokori, Ugbokolo, Benin City da Aba.
Kazalika, sunayen waɗanda aka yanke wa hukunci kan kashe jami’an tsaro, safarar miyagun ƙwayoyi, da satar kuɗi, da sauransu, sun jawo tambaya daga jama’a.
Rahotanni sun nuna cewa wannan cece-kuce ya sa fadar shugaban kasa ta fara nazarin sake duba tsarin afuwa, tare da yiwuwar cire sunayen da suka jawo suka daga jama’a.