Aminiya:
2025-10-24@10:30:19 GMT

Messi ya tsawaita kwantiraginsa da Inter Miami

Published: 23rd, October 2025 GMT

Fitaccen ɗan wasan tamaula, Lionel Messi, ya tsawaita kwantiraginsa da ƙungiyar Inter Miami har zuwa shekarar 2028, kamar yadda kulob ɗin ya sanar a ranar Alhamis, 23 ga Oktoba, 2025.

Wannan sabon kwantiragin zai bai wa kulob ɗin da ma gasar MLS ta Amurka damar ci gaba da kasancewa tare da ɗaya daga cikin fitattun ’yan wasan da duniya ta taɓa gani har zuwa ƙarshen kakar wasa ta 2028.

An kashe manoma uku da suke girbin amfanin gona a Filato Boko Haram sun kai sabbin hare-hare a wasu yankunan Borno da Yobe

A ƙarshen wannan kakar ce kwataragin ɗan wasan na ƙasar Argentina zai ƙare, inda ya bayyana farin cikin sabunta shi kamar yadda wani saƙo da kulob ɗin ya wallafa a shafin X ya tabbatar.

Messi, mai shekara 38, ya koma Inter Miami ne a 2023, bayan wani lokaci mara daɗi da ya ce ya yi a ƙungiyar Paris Saint-Germain (PSG) da ke Faransa.

Da wannan sabon kwantaragin, Messi zai ci gaba da murza leda har bayan Gasar Kofin Duniya ta 2026, wadda Amurka da Kanada da kuma Mexico za su yi tarayya wajen karɓar bakuncinta.

Messi dai ya shafe mafi rinjayen shekarunsa na tamaula a Barcelona, daga shekarar 2004 har zuwa 2021, inda ya ɗauki kofin La Liga 10 da na Zakarun Turai a tsawon lokacin.

Haka kuma, a shekarar 2022 ce ya jagoranci ƙasarsa ta Argentina wadda ta lashe gasar Kofin Duniya da aka gudanar a Qatar.

A yanzu, zaƙaƙurin dan wasan ya ci ƙwallaye 114 a matakin ƙasa tare da Argentina, sannan ya dauki Copa America har sau biyu a shekarar 2021 da kuma 2024.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Argentina

এছাড়াও পড়ুন:

MTN zai rufe ofisoshi 101 a Kano, Borno da Adamawa saboda gyare-gyare

Kamfanin sadarwa na MTN ya sanar da shirin gudanar da aikin gyare-gyare a cibiyoyin sadarwa a ranar Asabar, 25 ga watan Oktoba mai zuwa.

Ana sa ran aikin zai kawo tsaiko na ɗan lokaci ga sadarwa a wasu sassan jihohin Adamawa, Borno da Kano.

Labarin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya ƙarya ne – Sarkin Musulmi Masu kwacen waya sun kashe ma’aikaciyar lafiya a Zariya

MTN ya ce aikin zai ɗauki tsawon sa’o’i biyu, daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa 8:00 na safe, inda zai shafi ofisoshi 101 na cibiyar sadarwa a cikin ƙananan hukumomi 15 a jihohi ukun.

Kamfanin ya ce aikin yana cikin wani dogon shiri na inganta ayyuka da ƙarfafa tsarin sadarwa a Arewacin Najeriya.

Aikin zai haɗa da sauya wayoyin sadarwa na cable a wani ɓangare da aka matsar daga AFCOT zuwa kauyen Bawo, inda za a maye gurbin ɓangarorin wayoyin da suka lalace.

Yankunan da gyaran zai shafa

MTN ya ce yankunan da gyaran zai shafa sun haɗa da Karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano; Girei, Song, Mubi North, Hong, Gombi, Fufore, Mubi South, Madagali, Michika, Maiha, Chibok da Yola ta Arewa a jihar Adamawa; da kuma Askira/Uba da Shani a jihar Borno.

Kamfanin ya ce sabis din 2G da 3G da 4G ba za su yi aiki ba a lokacin aikin.

MTN ta ce wannan mataki yana gina kan aikin dawo da cibiyar sadarwa da aka gudanar a watan Agusta 2025 a kan hanyar igiyar sadarwa ta AFCOT–Bawo.

Kamfanin ya ce abokan huldarsa na iya fuskantar tsaiko na ɗan lokaci, kuma ya ba da hakuri kan duk wata matsala da hakan zai iya haifarwa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gaza Tasirin Rashin Abinci Mai Gina Jiki Da Magani  Zai Ci Gaba  Akan Yara Da Matan Har Zuriya Mai Zuwa
  • Gwarzuwar Shekarar 2025 Sanata Oluremi Tinubu
  • Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi
  • An Sake Saka Sunan Osimhen A Cikin ‘Yan Takarar Kyautar Gwarzon Dan Wasan CAF Na Bana
  • Jerin ’yan wasan da ke takarar lashe kyautar gwarzon Afirka na bana
  • Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Ta Sanar Da Wa’adin Biyan Kafin Alkalami Na Shekarar 2026
  • MTN zai rufe ofisoshi 101 a Kano, Borno da Adamawa saboda gyare-gyare
  • Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025 Na Jaridar Leadership: Dauda Lawal
  • Masu kwacen waya sun kashe ma’aikaciyar lafiya a Zariya