Ya ce Hukumar Binciken Ƙasa ta Nijeriya (NGSA) za ta jagoranci kwamitin, domin ita ce ke da ikon tattara bayanan ma’adinai na ƙasa baki ɗaya.

 “NGSA ta yaba da ƙoƙarin gwamnatin Jihar Kaduna bisa gaskiya da bayyana bayanai, tare da yin kira da a gudanar da binciken tabbatarwa mai zaman kansa,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa wannan haɗin gwiwar zai ƙara goyon bayan masu zuba jari a sashen ma’adinai na Nijeriya, tare da faɗaɗa bayanan kimiyyar ƙasa, wanda zai taimaka wajen haɓɓaka tattalin arzikin ƙasa ta hanyar albarkatun ma’adananta.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Yayansa A Matsayin Sabon Sarkin Duguri October 24, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya October 24, 2025 Manyan Labarai Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa October 24, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Tarayya ta yi jimami kan mutuwar mutanen da suka rasu a fashewar motar mai a Jihar Neja

Gwamnatin Tarayya ta bayyana alhinin ta kan mummunar haɗarin fashewar motar mai da ta faru a ƙauyen Essa, cikin Karamar Hukumar Katcha ta Jihar Neja, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da yawa.

 

A cikin wata sanarwa da Ministan Yada Labarai da Tsarin Ƙasa, Mohammed Idris, ya sanya wa hannu, Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyya ga Gwamnatin Jihar Neja da al’ummar jihar bisa wannan babban rashi, tana mai bayyana lamarin a matsayin abin tunawa da illar da ke tattare da haɗarin motocin mai a ƙasar.

 

Sanarwar ta nuna damuwa kan yadda, duk da wayar da kai da gargadin da ake yi a kai a kai, wasu ’yan ƙasa har yanzu ke shiga cikin haɗari ta hanyar kwasar mai daga motoci da suka kife, wanda hakan kan haifar da asarar rayuka da dukiya.

 

Ministan ya jaddada cewa duk rayuwar ɗan Najeriya tana da muhimmanci, tare da yin kira da a ƙara lura da bin matakan tsaro a lokutan gaggawa.

 

Ya yaba wa Gwamnatin Jihar Neja, jami’an tsaro, da kuma masu aikin ceto bisa saurin da suka nuna wajen kashe wutar da kuma ceto rayuka.

 

Haka kuma, Ministan ya bayyana cewa Hukumar Kula da Bala’o’i ta Ƙasa (NEMA) ta samu umarni da ta ci gaba da ba da tallafi da taimakon gaggawa ga waɗanda abin ya shafa, yayin da Hukumar Wayar da Kan Jama’a (NOA) za ta ƙara ƙaimi wajen yaɗa faɗakarwa domin hana irin wannan bala’i a nan gaba.

 

Gwamnatin Tarayya ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda suka mutu, tare da yin addu’a ga Allah Ya jikansu, Ya kuma ba waɗanda suka jikkata lafiya ta ƙwarai.

 

Bello Wakili

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Kafa Cibiyoyi 296 Na Koyon Fasahar Zamani A Faɗin Nijeriya
  • Nnamdi Kanu Ya Sake Bayyana A Kotu Ba Tare Da Lauya Ba, Zai Kare Kansa Da Kansa
  • Ƙungiyoyin Ma’aikatan Jihar Kaduna Sun Yabawa Gwamna Sani Kan Amincewa Da Sabon Albashin  Ma’aikata
  • Majalisar Tattalin Arziki Ta Amince da Shirin Gyara Cibiyoyin Horar da Jami’an Tsaro
  • Yadda DSS Suka Kama Masu Safarar Makamai Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kaduna
  • Shugabannin jam’iyyar PDP Na Arewa Sun Amince Da Turaki A Matsayin Ɗan Takarar Shugabancin Jam’iyyar Na Ƙasa
  • Gwamnatin Tarayya ta yi jimami kan mutuwar mutanen da suka rasu a fashewar motar mai a Jihar Neja
  • NUJ Reshen Kano Ta Taya Ahmed Mu’azu Murna Kan Naɗin Da NAHCON Ta Yi Masa
  • Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja