Gwamnatin Colombia Ta Bukatci Bayani Daga Amurka Kan Kashe Wani Dan Kasar A Tekun Carabian
Published: 20th, October 2025 GMT
Gwamnatin kasar Colombia ta bada sanarwan cewa sojojin Amurka wadanda suke cikin ruwan tekun Carabian sun shiga ruwan yankin kasar kuma sun kashe wani mai kama kifi a itasayen da suke yi a cikin tekun don hana abunda suka kira yaki da safarar miyagun kwayoyi.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran IP ya nakalto shugaban kasar ta Colombia yana fadar haka a shafinsa X a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa ‘jami’an gwamnatin kasar Amurka sun aikata laifi, inda suka kashe wani dan kasar mu mai suna Alejandro Carranza a cikin tekun Carabian, sannan ya kara da cewa shi ba mai safarar miyagun kwayoyine ba, aikin kamun kifi shi ne aikinsa tun da dadewa.
Gustavo Petro ya kara da cewa kisan da jami’an tsaron Amurka suka yi a tekun Carabian da sunan yaki da miyagun kwayoyi suna cikin ruwayen karkashin ikon kasar Colombia ne.
Gustavo Petro ya bukaci gwamnatin kasar Amurka ta gabatar da bayanai dangane da ke ta hurumin kasar ta Colombia. Yakuma kara da cewa hare-haren kan mutane a cikin ruwayen kasar Colombia ya sabawa wani kudurin da hukumar kare hakkin bil’adama wanda ya bukaci dukkan masu yaki da miyagun kwayoyi su kula da hakkin bil’adama a cikin ayyukansu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Fara Kidayar Kuri’un Zabukan Kananan Hukumomi 16 Da Aka Yi A Libya October 19, 2025 Araqchi: Iran Da Kasashen China Da Rasha Suna Shirin Kawo Karshen Takunkuman Turai October 19, 2025 Miliyoyin Mutanen Amurka Sun Yi Zanga-zanagr Nuna Kin Jinin Donald Trump October 19, 2025 Sheikh Na’im Kassim Ya Mika Sakon Ta’aziyyar Shahadar Gumari Na Kasar Yemen Ga Sayyid Husi October 19, 2025 Sojojin HKI Sun Shiga Cikin Yankin Qunaidhara Na Kasar Syria October 19, 2025 Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta October 19, 2025 Hamas ta yi Allah wadai da Isra’ila kan keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta October 19, 2025 An gudanar da zanga-zanga a sassa da dama na Amurka October 19, 2025 MDD : “Zai dauki lokaci” kafin a rage yunwa a Gaza October 19, 2025 ICC ta ki amincewa da daukaka karar Isra’ila October 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: tekun Carabian kara da cewa
এছাড়াও পড়ুন:
Sheikh Na’im Kassim Ya Mika Sakon Ta’aziyyar Shahadar Gumari Na Kasar Yemen Ga Sayyid Husi
Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya mika sakon ta’aziyyar shahadar babban hafsan hafsoshin sojan kasar Yemen Birgediya janar Muhammad Gumari ya shugaban Ansarullah Sayyid Abdulmalik al-Husi.
Shekh Na’im Kassim ya bayyana alhininsa mai zurfi na rashin Shahid al-Gumari tare da bayyana shahada a matsayin wata daukaka bayan doguwar tafiya akan tafakin jihadi.Haka nan kuma ya bayyana cewa;shahidin na Yemen ya jagoranci sojojin kasar cikin jarunta, ya kuma taimakawa Gaza wajen fuskanta laifukan ‘yan sahayoniya da Amurka.
Haka nan kuma babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya ce; yin shahadar jagorori wani alfahari da daukaka ne ga al’ummar musulmi, domin jinanensu sun hade a wuri daya, daga Yemen zuwa Lebanon da Iraki da Iraki.
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma taya sabon babban hafsan hafsoshin sojan kasar da aka zaba wanda ya maye gurbin shahidin janar Birgeriya Yusuf Hassan al-madani.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai HKI ta kai hari a Yemen wanda ya yi sanadiyyar shahadar babban hafsan hafsoshin kasar janar Muhammd al-Gumari.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin HKI Sun Shiga Cikin Yankin Qunaidhara Na Kasar Syria October 19, 2025 Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta October 19, 2025 Hamas ta yi Allah wadai da Isra’ila kan keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta October 19, 2025 An gudanar da zanga-zanga a sassa da dama na Amurka October 19, 2025 MDD : “Zai dauki lokaci” kafin a rage yunwa a Gaza October 19, 2025 ICC ta ki amincewa da daukaka karar Isra’ila October 19, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 159 October 19, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan(a) 158 October 19, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Al-Hassan (a) 157 October 19, 2025 KissoshinRayuwa : Sirar Imam Al-Hassan(a) 156 October 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci