Aminiya:
2025-12-07@21:24:23 GMT

Boko Haram sun kai sabbin hare-hare a wasu yankunan Borno da Yobe

Published: 23rd, October 2025 GMT

An zargi mayaƙan Boko Haram da ISWAP da kai hare-hare wasu yankuna biyar da ke Jihohin Borno da Yobe.

Sun kai hare-haren ne garuruwan Mafa, Dikwa, Marte, da Ajiri a Jihar Borno, da kuma Katarko a Jihar Yobe.

Jami’an tsaro sun kama Sowore saboda shirya zanga-zanga DSS ta cafke mutum 3 kan zargin sayar wa ’yan bindiga makamai a Kaduna

Rahotanni sun bayyana cewa ’yan ta’addan sun fara kai hari wani shingen sojoji  da ke Mafa, sannan suka sace makamai da sabbin babura da sojoji ke amfani da su.

Wata majiyar tsaro ta ce: “Sun zo da yawa kuma ɗauke da muggan makamai. Sun sace makamai da baburanmu. Yawansu dana gani abun mamaki ne.”

Ba a tabbatar da adadin sojojin da suka rasu ba, amma wani jami’in tsaro ya tabbatar da cewa sun kashe ’yan ta’adda da yawa a yayin artabun.

Wani mazaunin yankin, ya ce babu wanda aka kashe daga cikin mutanen gari, amma ’yan ta’addan sun sace kayan abinci da sauran kayayyaki, sannan suka ƙone wasu motoci.

“Lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 11 na daren ranar Laraba. ’Yan ta’addan sun fara kai hari shingen sojoji inda matafiya ke jiran a buɗe musu hanya domin su ci gaba da tafiyarsu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa mayaƙan sun kai harin a motoci huɗu ɗauke da bindigogi da kuma babura sa.a da 100, ɗauke da makamai.

Sun kuma kai makamantan waɗannan hare-haren a Marte, Dikwa, Ajiri duk a Jihar Borno, da kuma Katarko a Jihar Yobe.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Boko Haram garuruwa hare hare ISWAP mayaƙa

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga ya hallaka mutum 4, sun sace mata 4 a Sakkwato

’Yan bindiga sun kai sabon hari wasu yankuna na Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane huɗu tare da yin awon gaba da mata huɗu.

Wani mazaunin Gatawa, ya shaida wa Aminiya ce harin ya faru ne a daren ranar Asabar, lokacin da ’yan bindiga sama da goma suka shiga garin a kan babura.

Mutum 5 sun rasu sanadin gobara da faɗa wa rijiya a Kano Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin

A cewarsa, “Sun ratsa gefen gari suka dinga shiga gida-gida. Sun harbe mutane huɗu; uku sun mutu nan take, na huɗu kuma ya rasu a asibiti.”

Ya ƙara da cewa bayan harin, sojoji sun isa garin wanda hakan ya sa maharan suka tsere, amma duk da haka sun tafi da mata huɗu.

Sai dai ya bayyana cewa akwai wani malamin makaranta, Mustafa Malam Malam, da aka taɓa yin garkuwa da shi a baya.

Duk da cewa an biya kudin fansar Naira miliyan ɗaya da rabi, ba su sake shi ba, daga baya suka kashe shi.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, Alhaji Ayuba Hashimu, ya musanta batun cewa an kai hari masallaci.

Ya ce babu masallacin da aka kai wa hari ko aka kashe limami kamar yadda ake yaɗawa a kafofin watsa labarai.

Shi ma ɗan majalisar yankin, Aminu Boza, ya ce ba su da labarin wani hari da aka kai wa masallaci a yankin.

A wani labarin kuma, ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Shallah da ke mazabar Turba a Ƙaramar Hukumar Isa, inda suka kashe mutum ɗaya.

Daga nan sai suka wuce garin Barkeji, inda suka ƙone rumbunan abinci a daren ranar Asabar.

Ya zuwa yanzu babu wata sanarwar daga rundunar ’yan sandan jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hamas : ‘’Babu batun kwance damarar makamai matuƙar Isra’ila ta ci gaba da mamaya’’
  • Iran : sabbin dabarun tsaron Amurka cimma maradun Isra’ila
  • ’Yan bindiga sun hallaka mutum 4, sun sace mata 4 a Sakkwato
  • ’Yan bindiga ya hallaka mutum 4, sun sace mata 4 a Sakkwato
  • Amurka: Mun Yi Kokarin Kifar Da Gwamnatin JMI Har Sau Biyu Ba Tare Da Samun Nasara Ba
  • Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri ta Jigawa Ta Bada Kiyasin Kasafin Kudi na Sama da Naira Biliyan 161
  • Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta Kare Kasafin Kudin 2026 a Gaban Majalisa
  • ’Yan sanda sun ceto yara 2 da aka yi garkuwa da su a Borno
  • Fyaɗe ga ’yar shekara 12 ya ja wa matashi ɗaurin rai-da-rai a Yobe
  • Yan Sanda Sun Kama Muhuyi Magaji, Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci a Kano