’Yan sanda sun ƙwato miyagun ƙwayoyi a Gombe
Published: 17th, October 2025 GMT
Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka, inda ta gudanar da samame a wata maɓoya da ake zargi da aikata ayyukan ta’addanci da safarar ƙwayoyi a cikin jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ta bayyana cewa jami’an da ke ƙarƙashin Gombe Division ne suka gudanar da samamen da misalin ƙarfe 9:00 na dare a ranar Alhamis 10 ga Oktoba, 2025.
A cewar sanarwar, jami’an sun kai samamen wata maɓoya da ke bayan jerin shagunan Ƙaramar hukumar Gombe, (Local Government Shopping Complex), inda ake zargin wasu fusatattun matasa ke gudanar da ayyuka irin na ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.
“Da zarar matasan suka hangi isowar jami’anmu, suka tsere suka bar kayan ƙwayoyi da sauran haramtattun abubuwan da aka haramta,” in ji DSP Abdullahi.
Daga cikin abubuwan da aka ƙwato akwai nau’ukan miyagun ƙwayoyi kamar Suck and Die, Tramadol da allurarai na Diazepam.
An tura kayan shaida ɗin zuwa ofishin ’yan sanda domin ci gaba da bincike.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, CP Bello Yahaya ne ya tabbatar da ƙudirin rundunar na ci gaba da tabbatar da Gombe ta zauna lafiya an kuma tsarkake ta daga miyagun ƙwayoyi.
Ya kuma gargaɗi masu aikata laifuka da su daina irin waɗannan ayyuka ko kuma su fuskanci hukuncin doka.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Miyagun ƙwayoyi miyagun ƙwayoyi
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’an FRSC Sun Mayar Da N6.2m Da Suka Tsinta Bayan Aukuwar Hatsarin Mota A Katsina
Wani daga cikin waɗanda suka ji rauni, wanda shi ne mai kuɗin, ya gode wa jami’an FRSC bisa gaskiya da amana da suka nuna, yana mai cewa abin koyi ne ga kowa.
FRSC ta gargaɗi direbobi da su riƙa kula da motoccinsu akai-akai tare da bin ƙa’idojin hanya domin guje wa aukuwar haɗura.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA