Isra’ila ta kaddamar da hare hare kan wasu gine-gine da cibiyoyi a sassa daban daban na Iran ciki har da Tehran babban birni a cikin daren jiya wayewar wannan safiya ta Juma’a.

Kafofin yada labarai na Iran sun ce akwai mata da yara da dama daga cikin wadanda suka yi shahada a hare-haren.

An kuma bayar da rahoton kai hari a wurare a Natanz, Khorramabad, da Khondab, da dai sauransu.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce harin da Isra’ila ta kai wa Iran zai kai tsawon kwanaki idab akwai bukatar hakan.

“Za a ci gaba da gudanar da wannan aiki na tsawon kwanaki kamar yadda ake tsara don kawar da wannan barazanar,” in ji Netanyahu a cikin wata sanarwa ta bidiyo.

Hare-haren da sojojin gwamnatin sahyoniyawan suka kai kan Tehran ya yi sanadiyar shahadar wasu fitattun masana kimiyyar nukiliya na Iran, Mohammad Mahdi Tehranchi da Fereydoon Abbasi, dama wasu fararen hula.

Tehranchi shi ne shugaban jami’ar Azad ta Musulunci ta Iran.

Fereydoon Abbasi ya kasance tsohon shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran.

An dakatar da zirga-zirgar jiragai a filin jirgin saman Imam Khumaini na Tehran.

Harin ya zo ne kwanaki biyu gabanin wani sabon zagaye na shawarwarin nukiliyar Iran da Amurka.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Karamar Hukumar Birnin Kano Ta Kaddamar Da Kula Da Lafiyar Ido Kyauta

Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, Alhaji Salim Hashim Idris Gwangwazo, ya kaddamar da shirin kula da ido kyauta domin tallafawa jama’a da ke fama da ‘Glaucoma’ da ke lalata rijiyoyin ido, da ‘Cataract’ wato yanar ido da sauran cututtukan ido.

An gudanar da shirin ne a Asibitin Kwalli tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar, ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, da Hukumar Lafiyar Farko ta Jiha, da ƙaramar hukumar da masu bada tallafi daga kasashen waje.

Shirin ya haɗa da gwaje-gwajen lafiyar ido, da bayar da magunguna da kuma rarraba tabarau kyauta, musamman ga marasa ƙarfi a cikin al’umma.

Shugaban ƙaramar hukumar, ta bakin Kwamishinan Lafiya Alhaji Mustapha Darma, ya bukaci jama’a da su ci gaba da tallafawa gwamnati wajen samar da ingantaccen kulawa.

A baya-bayan nan, gwamnatin jihar ta dauki nauyin kula da lafiyar ido ga mutum  sama da 500 daga Birnin Kano da sauran kananan hukumomi.

Shugaban kula da lafiya am matakin farko na ƙaramar hukumar, Alhaji Lawan Jafar, ya ce wadanda lalurar su ba ta tsananta ba za a ba su shawarwarin kula da lafiyar su, da magunguna, wa su ma har da tabarau, yayin da wadanda ta su ta  tsananta kuma za a musu tiyata.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana sun nuna godiya tare da yi wa gwamnati addu’a don samun nasara.

Shugaban tawagar likitocin, Dr. Kamal Saleh, ya tabbatar da cewa shirin ya samu nasara sosai.

 

Daga Khadijah Aliyu 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • Microsoft ya ƙwace shafukan wasu kamfanoni 340 a Najeriya
  • Karamar Hukumar Birnin Kano Ta Kaddamar Da Kula Da Lafiyar Ido Kyauta
  • Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza
  • DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya
  • NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 
  • Sabunta Cinikin Ba Da Hidima, Masu Zuba Jari Na Waje Suna Ganin “Damar Da Kowa Ke Bukata A Kowane Lungu Na Sin”
  • NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas
  • Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato