Bukatar Kara Yawan Masu Fitowa Kada Kuri’a A Zabuka Nan Gaba
Published: 13th, June 2025 GMT
Sai dai, ya sanar da cewa, ya janye kurin ne, bayan ya tuntubi daidaikun mutane da sauran kungiyoyi a daukacin fadin kasar.
Halin girma da dakkun da Shugaba Abba ya nuna na janye wannan kurin bayan korafe-korafen alummar asar kasar, babu shakka janyewar abu ne, da ya dace, musamman duba da cewa, tursawa ‘yan kasa a tsarin Dimokiradiyya abu ne da bai dace ba, domin kuwa a tsarin dimokiradyya ana bai wa ‘yan zabin abinda zuke bukata, wanda hakan ya sabawa batun tilasta masu yin zabe.
Bugu da kari, batun fitar jama’a yin zabe, abu ne da ake bukatar a rinka wayar da kan ‘yan kasa da nuna masu amincewa, amma bai wai ace za a tilasata su, yin zaben ba da kuma cewar, za a hukunta su ba.
Sashe na 77 (2) a cikin baka da kuma sashe na 132 (5) a cikin baka, na kundin tsarin mulkin kasar nan na1999 da aka sabunta, sun bai wa ‘yan Nijeriya da suka kai shekaru 18 kuma suke zaune a kasar kada ‘yancin yin zabe.
Sai dai, rukunin ‘yan kasar da kundin bai bai wa wannan ‘yancin ba sune, wadanda ba su yi rijista sunayen su a hukumar INEC ba da wadanda aka yankewa hukuncin kisa sai kuma masu tabin hankail.
Wani abin takaici a kasar shi ne, yadda a ranar zabuka a kasar wadda kuma aka haramta zirga-zirgar mutane da gudanar da hada-hadar kasuwanci, amma wasu ‘yan kasar sukan yi burus da wannan haramcin, su fita a ranar zabukan don gudnar da hidindumin su, inda kawai ake ganin wasu, ‘yan kalilan ‘yan kasar ne, ke fita yin zaben.
Abin har ya zama jiki a Nijeriya, domin kusan sama da shekaru uku da suka gabata, duk lokacin da za a gudanar da zabukan gama gari, ana fuskantar karancin masu fitowa kada kuri’a, wanda haka ke nuna cewa, ana samun babban kalubale.
Misali, a 2015, duba da yawan adadin ‘yan kasar da suka canci kada kuri’a su miliyan 67.42, miliyan 29.43 ne kacal, suka fito jefa kuri’a wanda wannan adadin ya nuna cewa, kaso 65 ne kacal, suka kada kuri’unsu.
Bugu da kari, a 2019, wadanda suka canci kada kuri’a su miliyan 84 ne kacal, ba su fito kada kuri’a ba, inda miliyan 28.61 ne kacal, suka fito jefa kuri’arsu, wanda hakan ya nuna sun kai kaso 34.75.
Duba da yadda ‘yan kasar suka nuna matukar bukatar son fita zaben 2023, amma wadanda suka fita zaben, amma miliyan 24.97 ne kawai suka fita zaben wanda hakan ya nuna cewa, kaso 26.72 ne kawai, suka fita zaben, daga cikin wadanda suka canci yin zaben su miliyan of 93.47.
A batu na gaskiya, adadin masu fita zabe a Nijeriya ya yi kasa matuka, idan aka kwatanta da yadda wadanda suka canci kada kuri’a a kasashen Afirka ke yin Farar dango don fita zaben.
Alal misali, alkaluman zabukan da aka gudanar a kasashe kamar irinsu Rwanda, ta kasance tana da kaso 98.2, Gabon na da kaso 59, Liberiya na da kaso 70.
Kazalika, Sierra Leone na da kaso 75 Jamhuriyar Kongo na da kaso 42, Zimbabwe na da kaso 68.86, Afirka ta Kudu na da kaso 65, Masar na da kaso 66.88, sai kuma and Ghana wadda take da kaso 60.
Irin wadannan alkaluman a Nijeriya, batun yasha ban ban, domin a zaben 2023, an samu kaso 26.74 ne.
Zaben shugaban na 2023, tamkar anyi shi ne, na kusan gumurzu wanda shuaban kasar mai ci Bola Tinubu, ya lashe zaben, ta hanyar samun kuri’u 8,794,726 kacal, duk da cewa, Nijeriya na da wadanda suka kai munzalin kada kuri’a, su sama da miliyan 100.
Mai yawa, saboda irin wannan abin damuwar na rashin fita zaben ne, hakan ya sanya Abbas Tajudden da takwaransa Daniel Asama Ago, suka gabatar da dakataccen kudurin na tilasta ‘yan kasar da suka kai munzalin jefa kuri’a fita, domin sauke ‘yancinsu, da kundin tsarin mulkin kasar ya ba su.
Kin fita yin zaben da wasu ‘yan kasar da suke kai munzalin kada kuri’a, abu ne da bai dace ba.
A bisa matakin farko, abinda yafi dacewa a gano shi ne, shin me ke hada ‘yan kasar suka canci kada kuri’a ba su fita yin zaben, sannan kuma a lalubo da mafitar magance hakan.
Sai dai, wani hanzari ba gudu ba, za a iya cewa, ba su fita zuwa sauke nauyin na su ne, gazawar yadda ake tsara komai na gudanar da zabukan.
Karin wani abin takaicin shi ne, yadda wasu ‘yan zamalar ‘yan takara ‘yan siyasa ke hada baki da jami’an zabe, jami’an tsaro, inda kuma daga baya-bayan nan, suke hada baki da wasu Alakalai domin a tabka choge, a murda zabukan.
Irin wannan karfa-karfar da kuma murde zabuka ne, ke janyo karya masu Guiwar masu jefa kuri’ar, domin a bai wandanda ba su ci zaben nasara ba, wanda a lokuta da dama, wasu zabukan, ba a kammala kidaya kuri’un da aka kada.
Bugu da kari, a gefe daya kuma akwai matsalar ‘yan bangar siyasa da ke tayar da yamusti a Rumfunan zabe musamman domin su kare rayukansu daga aukwar ‘yan bangar siyasa da matsalar sayen kuri’u da kuma wallafa labarukan karya na sakamakon zabukan.
Hakazalika, wani batun mai ban haushi shi ne, na rashin hukuntan wadanda suka karyar dokokin zaben.
Karin wani abin takaicin shi ne, na yadda jam’iyyun kasar ba su da dabi’ar ilimantar da masu jefa kuri’a kuma ba su wani takamai-man shirye-shirye da suka tanada, domin yin hakan, sai dai kawai, su buge da yin farfagandar siyasa, wanda idan sun dare madafun iko, su yi watsi da magoya bayansu.
Akwai kuma batun kalubalen rashin samun samun yin rijitsa domin samun katin yin zabe wato PBC.
A bisa ra’ayin wannan Jaridar, mai makon batun matsawa wadanda suka munzalin jefa kuri’a don su yi zaben ba, kamata ya yi ‘yan Majalisar su gabatar da kudurin da zai sanya a sanya wa ‘yan kasar da suka cancanci kada kuri’a sha’awar fita sauke nauyin na su.
Yin haka ne, kadai, zai tabbatar da matsayin Hukumar Zabe ta kasa INEC, tabbacin cewa, Hukuma ce, mai cin gashin kanta.
Kazalika, ya zama wajbi INEC ta kara inganta tsare-tsaren ta kuma dole ne, duk wani jami’ain tsaro da ‘yan siyasar da aka samu da taka dokokin zabe, an hukunta su.
Wannan Jaridar na da yakinin cewa, ‘yan Nijeriya na son fita yin zabe, amma yadda ba a gudanar da zabukan a bisa gaskiya ne ke kara janyo wadanda suka canci kada kuri’ar, ba su fita, domin sauke nauyinsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: wadanda suka canci a gudanar da yan kasar da
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda Masu Bukata Ta Musamman Suka Rungumi Sabbin Dabarun Noma Domin Ciyar Da Kansu
Wannan yana cikin wani tsari na noma da aka kirkiro musamman don masu bukata ta musamman domin su dogara da kansu maimakon rokon hatsi ko neman taimako.
Wannan yana cikin wani tsari na noma da aka kirkiro musamman don masu bukata ta musamman domin su dogara da kansu maimakon rokon hatsi ko neman taimako.
Wakilinmu ya ziyarcj wata kebabbiyar gona dake cikin garin Kaduna, inda gungun wasu manoma da ke fama da lalurori daban-daban irin su makanta da gurguntaka da kurma, suka rungumi sabbin dabarun noma na zamani domin tallafawa rayuwarsu, musamman a wannan damina da aka shiga.
Gonakin da wadanda makafi da guragu ne suke nomawa a duk shekara Sun bayyana cewa suna gudanar da nomansu ne ba tare da wata gudummawa daga gwamnati ba kama da samar musu da takin zamani da sauran kayan noma kamar yadda ake tallafawa Masu lafiya.
A zantawarsa da wakilinmu a cikin gonarsa, Mista William Makiya, wanda ke fama da matsalar gani (makaho), yana noma da huda domin ciyar da iyalinsa. Ya bayyana cewa:
“Ba na gani da idona. Dalilin da yasa nake yin noma shine domin ciyar da iyalina. Ba na yin bara kuma bana san yin bara kwata-kwata rayuwata. Ba na kaunar bara.”
William ya kara da cewa yana jin dadin aikin noma, kuma yana taimakawa makwabtansa masu lafiya da kayan abinci daga gonarsa. Wannan yana karfafa zumunci da hadin kai tsakaninsa da sauran al’umma da suke zaune tare a cikin muhalli daya.
Ya ce:“Da galma nake yin wannan noma. Ina amfani da fatanya da sauran kayan huda wajen noma da kuma cire ciyawa a gonaki.”
Ya ci gaba da cewa gonarsa tana da layukan shuka wanda yake amfani da su wajen shuka wake, dankalin hausa, gyada, da kayan lambu irin su tumatur da kubewa.
A kowace shekara, jajirtattun manoma masu bukata ta musamman ne ke amfani da wadannan filayen noma domin ciyar da kansu, kamar yadda wani matashi mai lalurar kafa Mai Suna Joshua Matthew, ya bayyana cewa Shi ma yana noma da huda a gonarsa.
“Abin da ya kamata a sani shi ne, ni ina noma da huda sosai domin ciyar da iyalina. Ina noma masara da shinkafa da sauran kayayyakin abinci domin rage tsadar rayuwa.”
Joshua ya ce duk da cewa ba shi da kafa, yana zaune yana jan jikinsa domin yin noma da cire ciyawa da sauran ayyukan noma. Ya tabbatar da cewa ya dade yana wannan aiki, kuma babu wahala kamar yadda mutane ke tunani.
Ya jaddada bukatar gwamnati ta tallafa musu domin su zama masu dogaro da kansu.
Duk da karancin ruwan sama a bana, wadannan manoma ba su karaya ba. Sun ci gaba da aiki tukuru a gonakinsu, suna amfani da dabarun noma na zamani domin tabbatar da samun abinci mai yawa da inganci.
Babu shakka, wadannan manoma suna gudanar da aikin noma ta hanyar wani tsarin hada kowa da kowa musamman masu nakasa cikin harkar noma domin yakar yunwa da talauci a Nijeriya. Wannan tsarin na “inclusibe smart farming” ya fara haifar da nasarori, a cewar Kwamared Rilwani Abdullahi, shugaban kungiyar masu bukata ta musamman a Nijeriya.
Ya ce:“Wannan wani yunkuri ne na zama masu dogaro da kai. Saboda haka, muna kira ga hukumomi da su tashi tsaye wajen tallafawa wadannan manoma, da kuma tabbatar da cewa ana sanya su a cikin jerin manoman da ake tallafawa a duk lokacin da ake rabon takin zamani.”
Yanzu haka dai, wadannan gwarazan manoma sun dukufa sosai cikin harkar noma domin ciyar da kansu maimakon barace-barace. Sai dai, sun koka kan yadda ake rarraba takin zamani ba tare da an tuna da su ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp