Nijeriya Ce Ta 3 A Manyan Kasashe Masu Karfin Masana’antu 10 Na Afirka
Published: 13th, June 2025 GMT
Tsarin yanayin masana’antu na Masar yana bunkasa kan fitar da kayayyaki zuwa Turai da Gabas ta Tsakiya. Tare da kasancewa mai karfi a cikin sinadarai, siminti, da kantin magani, Masar ta sanya kanta a matsayin jagorar masana’antun nahiyar da ke goyan bayan gyare-gyaren masana’antu.
An san kasar da samar da siminti, yadudduka, magunguna, da sinadarin man fetur da sauransu.
Sai kuma kasar Nijeriya mai rike da kambu na uku wacce ta kasance mai samun habaka a bangaren kasuwanci da masana’antu. Kamfanonin Dangote, musamman matatarsa da kuma rukunin kamfanonin BUA sun taimaka wa kasar wajen jan ragamar a bangaren masana’antu.
Manyan masana’antun kasar nan sun hada da na siminti, kayayyakin mabukata, abinci da abin sha, da tace mai, wanda manyan masana’antun kamar Dangote Group, BUA Group, Nestlé Nigeria, da Unileber Nigeria ke gudanarwa.
Morocco kuwa babbar cibiyar masana’antu ce a Arewacin Afirka, tana jawo hannun jari kai tsaye daga ketare a manyan masana’antu kamar kera motoci da hada-hadar jiragen sama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Barazanar Amurka Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya: Tinubu Da Trump Za Su Gana Kwanan Nan — Bwala
Da yake mayar da martani ga wannan zargin na Amurka, Bwala ya ce gwamnatin Tinubu tana jajircewa wajen kare dukkan ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da addini ba, yana mai cewa Amurka da Nijeriya sun dade suna hadin gwiwa a yaki da ta’addanci.
“Shugaba Bola Tinubu da Shugaba Donald Trump suna da kudiri iri ɗaya a yaƙi da ta’addanci da duk wani nau’in ta’addanci a kan bil’adama,” in ji Bwala.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA