Yadda mota ta kashe mutum 8 ’yan gida daya bayan dawowa daga yawon Sallah a Kaduna
Published: 13th, June 2025 GMT
Wani mummunan hatsarin mota a hanyar Kaduna zuwa Zariya ya yi sanadin mutuwar mutum takwas ’yan gida daya, yayin da wasu mutum biyu ke can kwance a asibiti rai a hannun Allah.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne wajen misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Litinin a garin Barakallahu da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya, ana tsaka da bukukuwan Babbar Sallah.
A cewar rahotannin, lamarin ya faru ne lokacin da wata mota da ke tsala gudu ta kwace sannan ta danne mutanen da ke tsaye a gefen hanya bayan dawowarsu daga yawon sallah.
Sojoji sun kashe kasurguman ’yan bindiga 3 a Zamfara Mutum ɗaya ya tsira da ransa cikin 242 a hatsarin jirgin IndiaA cewar mahaifin mamatan, Malam Jamilu Usman Maiyadi, wata mota kirar GLK Marsandi mai ruwan toka ce ta take iyalan nasa, kuma wani yaro ne yake tuka ta.
Sai da a cewarsa, yaron wanda suka yi ittifakin dan gidan wani fitaccen dan siyasa ne a yankin, ya cika wandonsa da iska bayan faruwar lamarin.
Ya ce, “Mun rasa iyalai takwas ’yan gida daya a rana daya. Daga ciki akwai matata Khadija Umar da ’ya’yana su biyu sai kuma kanne da yayyen matar tawa da kuma wata gwaggonsu, duk sun mutu.
“A jimlance, mutum takwas kenan motar ta take; takwas sun mutu nan take, biyu kuma har yanzu suna asibiti,” in ji shi.
Malam Jamilu ya ce iyalan nasa na tsaye ne a bakin hanya suna jiran su sami motar da za ta kai su gida lokacin da motar ta kwace daga kan titi ta afka musu.
Ya kuma ce, “Tabbas motar na gudun wuce sa’a lokacin faruwar lamarin saboda kafar matata ta yi karayar da ba za a iya gyarawa ba, sannan sai jami’an hukumar kiyaye hadura ne ma daga baya suka gano wasu sassan jikin dana Sadiq,” Malam Jamilu ya fada fuskarsa cike da alhini.
‘Har da mai cikin wata takwas da za ta haifi tagwaye a cikin wadanda suka mutu’
Daga cikin wadanda suka rasu har da Zainab Muhammad wacce ke dauke da juna-biyun wata takwas da za ta haifi tagwaye.
Mijin marigayiyar, Sulaiman Abdulkadir Mai Shinkafa, wanda malamin addini ne a Hayin Rigasa, ya bayyana lamarin a cikin alhini.
Ya ce, “Ta kusa haihuwa. Mun riga mun sayi duk kayan jarirai muna shirye-shiryen haihuwar. Har mun ma sanya wa jariran sunan Hassan da Hussaini. Sannan akwai danmu mai shekara shida mai suna Khalid da aka kashe.
“An take matar tawa, sannan dana sai da muka kankaro namansa da katako kafin a yi musu jana’iza. Abu ne da babu wanda zai yi fatan ya gani a rayuwarsa.”
‘Ko uffan iyalan yaron da ya take mu ba su ce mana ba’
Kamar sauran masu alhinin, Malam Sulaiman ya nuna takaici kan yadda ya ce iyalan yaron da gwamnati sun yi watsi da su ko uffan ba su ce musu ba.
“Babu wani daga cikin iyalan yaron, wanda dan wani fitaccen dan siyasa ne a yankin da ya tuka motar, ko kuma daga gwamnatin jihar Kaduna da ya zo ya yi mana ta’aziyya.
“Ko uffan ba su ce mana ba. hatta mahaifin direban motar bai zo ba, sai ka ce yaruwar iyalan namu ba ta da wani amfani,” in ji shi.
Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta alakanta shi da gudun wuce sa’a da kuma kwacewar mota a kan hanyar da ba a jima da dauke ruwan sama ba.
Kwamandan shiyya na hukumar a Kaduna, Tijjani Iliyasu ne ya tabbatar da hakan.
Sai dai ya ce sun mika lamarin zuwa hannun ’yan sanda domin fadada bincike a kai.
Kazalika, duk kokarin wakilinmu na jin ta bakin rundunar ’yan sandan Kaduna da gwamnatin jihar sun ci tura saboda sun ki cewa komai a kai.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hatsarin mota Zariya
এছাড়াও পড়ুন:
Ambaliyar Mokwa: An sake gano gawar mutum bayan kwanaki 8
Kwanaki takwas bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye garin Mokwa, hedikwatar Ƙaramar hukumar Mokwa a Jihar Neja, an gano gawar mutum ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, an tsinci gawar ne a ranar Alhamis a wata gona da ke kan hanyar wucewa kusa da wani wuri da aka fi sani da ‘dam’.
Ambaliya: Gwamnatin Kano ta fara tsaftace magudanan ruwa Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — FayemiA cewar shaidun gani da ido, an kasa tantance wanda abin ya shafa saboda gawar ta lalace. An binne shi ne a inda aka gano gawarsa.
Wata mazauniyar yankin mai suna Tswata Mai Rubutu da ta zanta da Aminiya ta wayar tarho, ta ce an tsinci gawar a kan hanyar da ruwa ke wucewa.
“Gawar wani babban mutum ne, amma ba za mu iya gane shi ba saboda tuni ya fara lalacewa. An binne shi a wurin tun da ba a iya motsa gawar,” in ji shi.
An yi ƙoƙarin jin ta bakin Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Abdullahi Baba Arah, domin ƙarin bayani lamarin ya ci tura.
Tun da farko hukumar ta tabbatar da mutuwar mutane 161, yayin da wasu da dama suka ɓace bayan iftila’in ambaliyar.