Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta ce mayar da martani ga gwamnatin Isra’ila hakki ne na shari’a ga Iran kamar yadda doka ta 51 ta kundin tsarin mulkin MDD ta tanada.

Da farko dai ma’aikatar ta mika ta’aziyyar shahadar wasu kwamandoji da jami’an kasar Iran a harin da Isra’ila ta kai wa kasar.

“Hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ta kai wa Iran sun sabawa doka ta 4 sakin layi na 2 na kundin tsarin mulkin majalisar dinkin duniya a matsayin wani mataki na wuce gona da iri kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma Iran tana da hakki na shari’a na halal ta mayar da martani kan wannan zalunci kamar yadda yake a cikin sashe na 51 na kundin tsarin mulkin majalisar dinkin duniya.

Sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kare al’ummar Iran da dukkan karfinsu.”

“Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayinta na mamba a Majalisar Dinkin Duniya, tana mai jaddada wajibcin kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya na daukar matakin da ya dace wajen tunkarar matsalar zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa, sakamakon wuce gona da iri da gwamnatin sahyoniyawan take yi wa Iran.

“Dukkan kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya, musamman na shiyya da na Musulunci, da ‘yan gwagwarmaya, da dukkan duniya ana sa ran nan take za su yi Allah-wadai da wannan aika-aika da kuma daukar matakin gaggawa da hadin gwiwa don tinkarar wannan kasada mai hatsarin gaske wadda ko shakka babu ta nuna yadda zaman lafiya da tsaro a duniya ke cikin wata babbar barazana da ba a taba ganin irinsa ba.”

Iran, ta kuma babu shakka wannan danyen aikin da Isra’ila ta aikata ya samu sahalewar Amurka, don haka a cewar Tehran,  Amurka na da hannu a wannan hare haren na Isra’ila.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki Guda 5 A Wajen Taron Kolin kere-kere .

Rahotanni sun bayyana cewa kasar iran ta bayyana sabbin kayayyaki guda 5 da ta kera a wajen babban taron kere-kere na kasa da kasa karo na 23,kuma dukkansu kamfanonin kasar iran ne suka yi su domin rage dogaro da kayyakin kasashen waje.

Taron ya samu halartar mataimakin shugaban hukumar kula da kimiya da fasaha ta kasa da sauran shuwagabannin kamfanoni inda ya nuna irin karfin iran wajen kere-kere da kuma mayar da hankali kan kamfanoni dake filin shakatawa na pardis technology park.

Daga cikin magungunan da aka gabatar a wajen akwai Sirolimus wanda Zist takhmir company ya kera, kuma magungunan rigakafi ne da ake amfani da su wajen hana dashen gabobin jiki da kuma kula da cututtuka da ba kasafai ake samun su ba.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta. September 16, 2025 Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana September 16, 2025 Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi September 16, 2025 Pezeshkian: Ta’addancin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Kan Kasar Qatar Zalunci Ne Ga Diflomasiyya September 16, 2025 Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya September 16, 2025 Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan   September 16, 2025 Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida September 16, 2025 Tawagar Yan Wasan Damben Gargajiya Ta Iran Ta Zama Zakara A Damben Ta Duniya September 16, 2025 An Fara Taron Hukumar Makamashin Nukliya Ta Duniya IAEA Karo Na 69 A Birnin Vienna September 16, 2025 Espania Ta Soke Cinikin Makamai Na EUR Miliyon 700 Da HKI Saboda Kissan Kiyashi A Gaza September 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kammala Ziyarar Yini 3 A Ma’aikatar Kananan Hukumomin Jihar
  •  Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Falasdinawa  Kisan Kiyashi A Gaza
  • Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya
  • Ma’aikatar Shari’ar Iran Ta Sanar Da Rataye Dan Leken Asirin Hukumar Mossad Ta Isra’ila
  • Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza
  • Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki Guda 5 A Wajen Taron Kolin kere-kere .
  • Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya
  • Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar Wa Atiku Martani Kan Cewar ‘Yan Nijeriya Na Fama Da Yunwa
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Qatar, Turkiyya, Pakistan Da Labanon A Doha
  • Tarihin Ƴan Majalisar Farko Kafin Da Kuma Zamanin Mulkin Mallaka (3)