Kotu ta yanke wa matashi ɗaurin wata 6 kan satar kaza
Published: 27th, February 2025 GMT
Wata kotun majistare da ke zamanta a Ago Iwoye, Jihar Ogun, ta yanke wa wani matashi ɗan shekara 21, Adebanjo Segun, hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari bisa samunsa da laifin satar kaza.
Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar tsaro ta Civil Defence , Dyke Ogbonnaya ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
An ce an fara samun matsalar ne a ranar Laraba, 19 ga Fabrairu, 2025, kan Adebanjo mai shekara 21 a lokacin da aka kama shi da laifin satar kaza.
Zulum ya rage adadin tallafin rabon abinci da kashi 90 a Borno An shiga ruɗani bayan Obasa ya koma majalisar Legas da ’yan sandaOgbonnaya ya bayyana cewa, “Bayan an yi nazari sosai kan lamarin tare da kammala bincike, an gano cewa wanda ake tuhuma ya aikata irin wannan laifin a wani lokaci a watan Disambar 2024 inda aka yi masa afuwa a matsayin wanda ake zato da ya yi laifin farko.
“Saboda bayyana laifin da ya aikata a baya, an gurfanar da shi a gaban Kotun Majistare ta Ago-Iwoye kan tuhume-tuhumen da ya shafi sashe na 430 na dokokin manyan laifuka na Jihar Ogun, Nijeriya 2006, a ranar 20 ga Fabrairu, 2025.
“Bayan ya amsa laifinsa a gaban Alƙali O.F. Adeduntan, an same shi da laifin kuma kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari.”
Hakazalika, an kuma yanke wa wani Kazeem Tobi mai shekara 20 hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari bisa samunsa da laifin satar janareta na Elepaƙ wanda kuɗinsa ya kai kusan N120,000 kacal.
An ce an sake gurfanar da Tobi a ranar Talata, 4 ga watan Fabrairu, 2025, kuma bayan da aka yi nazari sosai a kan lamarin, an gurfanar da shi a gaban Kotun Majistare ta Ago-Iwoye kan tuhume-tuhume biyu da suka shafi haɗa baki wajen aikata laifi da kuma mallakar wani abu da ake zargin an sace.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gidan Yari satar kaza
এছাড়াও পড়ুন:
Wani abin fashewa ya kashe mutum 26 a Borno
Wani abin fashewa da ake zargin bam ne ya kashe aƙalla mutum 26, ciki har da mata da yara a kan hanyar Rann zuwa Gamboru Ngala da ke Jihar Borno.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin a lokacin da motoci suka tayar da bama-baman da aka ɗana a gefen hanyar, da ya rutsa da maza 16 da mata huɗu da ƙananan yara guda shida.
Ta yi wa saurayinta ƙaryar shekarunta 27 maimakon 47 An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da PortugalMajiyoyi, ciki har da wani babba soja, sun tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu da harin na baya bayan da safiyar ranar Talata.
Sun bayyana cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su suna kan hanyarsu ta tafiya Gamboru Ngala ne daga Rann lokacin da suka isa inda ‘yan ta’addan Boko Haram suka ɗana bam ɗin.
Bayanai sun ce baya ga mutum 26 da suka mutu, ƙarin mutum uku sun ji munanan raunuka.
“Mun tura wasu masu ba da agajin gaggawa inda lamarin ya auku domin kwashe mutane tare da tabbatar da tsaron sauran fararen-hula a wurin,” kamar yadda wata majiyar sojin da ba ta yarda a bayyana sunanta ba ta shaida wa Anadolu.
Ali Abass, wani ganau wanda ke tafiya a kan hanyar a lokacin da lamarin ya auku, ya ce sojojin da ‘yan sa-kai sun kai waɗanda suka jikkata wani asibiti. Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin ‘yan’uwansa na cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Harin yana zuwa ne yayin da hare-hare ke ƙara ƙaruwa a yankin Tafkin Chadi, inda ‘yan ta’addan Boko Haram ke ƙara ƙaddamar da hare-haren bama-bamai da kwanton-ɓauna kan motocin fararen-hula da na sojoji.
An ba da rahoton hare-hare irin wannan a ranakun 21 ga watan Maris da 12 ga watan Afrilu. Kawo safiyar ranar Talata dai, jami’an tsaro a Borno ba su fitar da wata sanarwa a hukumance game da lamarin ba.