Boko Haram ta ƙona wuraren ibada da gidaje a Adamawa
Published: 27th, February 2025 GMT
Mayaƙan Boko Haram sun kai hari a cikin dare inda suka ƙona wuraren ibada da gidaje da makarantu da shaguna a ƙauyen Kwapre da ke yankin Sabuwar Yadul a Ƙaramar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa.
Gabanin Sallar Isha’ a ranar Talata ne mayaƙan suka far wa yankin da hari, inda suka yi ta cin karensu babu babbaka.
Mazauna sun bayyana cewa maharan sun ƙona wuraren ibada da makarantu da gidaje da shaguna sannan suka sace dukiyoyin jama’a.
Mai unguwar kauyen Kwampre da Joel Kulaha, ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma ya ce ba a samu asarar rai ba.
NAJERIYA A YAU: Halin da jama’a za su shiga idan Kamfanin Kaduna Electric ya ƙi sauraren ma’aikatansa Dangote ya rage farashin man fetur zuwa N860 a LegasYa bayyana cewa mazauna yankin sun tsare bayan farmaki da ’yan ta’addan suka kai musu.
“Mun samu tsira da rayukanmu, amma mu rasa duk wani abu da muka mallaka,” in ji shi, yana mai cewa babu dalilin harin da aka kawo musu.
Rahotanni sun bayyana cewa sojojin da aka girke a yankin Garaha da ke kusa da wurin sun kawowa al’ummar ɗauki, inda suka yi artabu tare da fatattakar maharan.
Sai dai mazauna na zargin cewar jami’an tsaron sun yi jinkirin zuwa, shi ya sa maharan suka yi ɓarna fiye da kima.
Wakilinmu ya yi ƙoƙarin zantawa da kakakin Birget na 23 na rundunar Sojan Najeriya, A. S. Adewunmi, amma jami’in bai amsa kiran waya ko rubutaccen sakon da aka aika masa ba.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane Da Dama A Yola
Ruwan sama mai ƙarfn gaske ya haddasa mummunar ambaliya a Yola ta Kudu, Jihar Adamawa, inda mutane da dama suka mutu, yayin da wasu da dama suka rasa matsugunnansu.
Yankunan da ambaliyar ta fi shafa sun hada da Shagari, Sabon Pegi da Anguwan Tabo.
Ayyukan ceto suna ci gaba da gudana, inda Sojoji da hukumomin agaji ke kwashe mazauna yankunan da abin ya shafa.
Hukumomi sun shawarci mazauna yankunan da ke fuskantar barazanar ambaliya da su gaggauta barin wuraren, kasancewar ana hasashen karin ruwan sama.
RN