Gidauniyar Sarki Salman Ta Rab Tallafin Abinci Ga Mutane 2,450 A Kebbi
Published: 27th, February 2025 GMT
Gidauniyar Sarki Salman ta Saudi Arabiya ta bayar da tallafin kayan abinci ga marasa ƙarfi 2,450 a Jihar Kebbi ta hannun hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA). An gudanar da rabon ne a Birnin Kebbi, inda aka raba buhuhunan shinkafa da wake mai nauyin kilo 25, garin masara kilo 2, da man gyada. An gudanar da rabon kayan ne a ɗakin ajiyar abinci na gwamnatin jihar da ke Bulasa.
Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida, wanda ya wakilci Gwamna Nasir Idris a wajen rabon, ya gode wa gidauniyar bisa tallafin da ta ke bai wa mutanen jihar.
Amurka Da Rasha Sun Kammala Tattaunawar Kawo Ƙarshen Yakin Yukiren A Ƙasar Saudiyya Hajjin 2025: Kamfanin Saudiyya Ya Amince Da Kwangilar Aiki Da NAHCON Bayan Sabunta YarjejeniyaYa ce wannan ba shi ne karo na farko da gidauniyar ke taimakawa ba, yana mai yabawa da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin su da ƙasar Saudi Arabiya, musamman kan ayyukan jin ƙai da aikin hajji. Gwamnatin jihar ta yaba da rawar da NEMA ta ke takawa wajen rabon tallafin.
Shugabar hukumar NEMA ta ƙasa, Hajiya Zubaida Umar, wadda Hajiya Fatima Kasim ta wakilta, ta ce gidauniyar Sarki Salman ta dauki tsawon lokaci tana bayar da irin wannan tallafi tun daga shekarar 2018 domin taimakawa marasa galihu a Nijeriya. Ta bayyana cewa bayan Kebbi, za a ci gaba da rabon kayan abinci a jihar Adamawa. NEMA ta gode wa gwamnatin tarayya da Gwamnatin Jihar Kebbi bisa haɗin kan da suka bayar wajen ganin an aiwatar da aikin cikin nasara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
Daga Usman Muhammad Zaria
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar.
Ya bayyana cewa, wannan gudummawa ta nuna cikakken kudirin gwamnatin Gwamna Namadi na ƙara inganta harkokin tsaro da kuma tallafawa Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya wajen aiwatar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.
Kwamishinan ya nuna cewa, waɗannan sabbin motoci 10 za su taimaka matuƙa wajen rage lokacin da ake ɗauka kafin amsa kiran gaggawa, tare da ƙara inganta aikin rundunar a fadin jihar.
Ya ƙara da cewa, za a yi amfani da motocin yadda ya kamata, tare da kula da su don tabbatar da ingantaccen tsaro.
CP Dahiru Muhammad ya kuma sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.