Sakon Jagora : Isra’ila ta jira hukunci mai tsanani bayan hari kan Iran
Published: 13th, June 2025 GMT
Bayan harin da gwamnatin Sahayoniya ta kai kasarmu, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aike da sako ga al’ummar Iran. Ga sakon kamar haka
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai
Al’ummar Iran masu daraja!
Gwamnatin yahudawan sahyoniya ta hanyar aikata wani laifi da sanyin safiyar yau, ta sake bayyana munanan dabi’arta da fasadi.
Ta hanyar kai hari dole ne wannan ya fuskanci hukunci mai tsanani.
A wannan harin makiya, kwamandoji da masana kimiyya da dama sun yi shahada.
Wadanda suka gaje su kuma da abokan aikinsu za su ci gaba da aiki nan take akan wannan tafarki, godiya ta tabbata ga Allah.
Ta hanyar wannan danyen aiki, gwamnatin Sahayoniya ta kaddara akan ta cewa zata fuskanci martini mai radadi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Iran Ta Ce Tana Hulda Da Amurka Ta Hanyar Masu Shiga Tsakani
Kasar Iran ta bayyana sake kulluwar hulda da Amurka ta hanyar masu shiga Tsakani
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin siyasa Majid Takht-Ravanchi ya sanar da cewa: Wasu kasashe na tuntubar Iran da Amurka a matsayin masu shiga tsakani.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin siyasa ya shaidawa tashar Haber Turk ta Turkiyya cewa: Akwai tuntuba tsakanin Iran da Amurka ta wasu kasashe masu shiga tsakani, yana mai cewa: “Wasu kasashe suna hulda da Iran da Amurka, kamar yadda kuka sani, don haka Iran tana tattaunawa da Oman a matsayin mai shiga tsakani.”
Da yake amsa tambaya game da ganawar da kungiyar Tarayyar Turai a Istanbul, ya ce: “Iran ta sake gudanar da wani zagaye na shawarwari tare da kasashen Turai a matakin mataimakan ministoci. An dade ana ci gaba da gudanar da wannan tsari, tana ganawa da tattaunawa kan batutuwa daban-daban kan batun makamashin nukiliya. A taron jiya sun tattauna batutuwan fasaha na batun makamashin nukiliya da kuma batun dage takunkumin da aka sanyawa kasar Iran, kamar yadda Iran din ta jaddada cewa dole ne a samar da duk wani bangare na inganta sinadarin Uranium a cikin kasar Iran.”