Rundinar IRGC, ta sanar da shahadar babban kwamandanta Manjo Janar Hossein Salami a harin ta’addancin Isra’ila
Published: 13th, June 2025 GMT
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun sanar a cikin wani sako mai cike da alhini da shahadar Manjo Janar Hossein Salami, babban kwamandan dakarun IRGC wanda ya yi shahada da asubahin ranar Juma’ar nan yayin wani hari na ta’addanci” da gwamnatin sahyoniyawan ta kai kan hedkwatar rundunar.
Hukumar soji tana jinjinawa wannan babban kwamandan da aka gabatar a matsayin babban jigo wajen kare manufofin juyin juya halin Musulunci na Iran, tare da yin alkawarin mayar da martani mai tsauri ga makiya.
Ga yadda sanarwar IRGC ta kasance :
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai
A cikin bakin ciki da radadi muna sanar da shahadar Manjo Janar Hossein Salami, babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci, da da wasu mukarabansa, a lokacin harin ta’addancin da gwamnatin sahayoniya ta kai a safiyar wannan ranar ta Juma’a akan hedkwatar IRGC yayin da suke gudanar da muhimmin aiki na tsaron kasa.
Muna mika ta’aziyyarmu ga Jagoran juyin juya halin Musulunci kuma babban kwamandan sojojin kasar, Imam Khamenei, da iyalan duk wadanda abun ya shafa.
Duk da wannan harin na dabbanci, muna tabbatar wa al’ummar Iran masu daraja cewa, har yanzu rundunar sojojin Iran a shirye suke don maida martani ga gwamnatin sahyoniyawan.
Nan ba da jimawa ba za a isar da cikakken bayani kan halin da ake ciki biyo bayan harin na makiya da kuma matakin da za a dauka na hukunta su.
Haka zalika kafofin yada labarai na Iran sun rawaito shahadar babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Mohammad Hossein Baqeri.
Shi ma Manjo Janar Baqeri ya yi shahada a wani harin ta’addanci da gwamnatin sahyoniya ta kai birnin Tehran a safiyar yau Juma’a.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: juyin juya halin Musulunci babban kwamandan Manjo Janar
এছাড়াও পড়ুন:
Harin Ta’addanci A Wani Coci Ya Lashe Rayukan Mutane Fiye Da 21 A Gabashin Kongo
Fiye da mutane 21 ne suka mutu a wani harin ta’addanci da aka kai kan wani coci a gabashin Kongo
Rahotonni sun tabbatar da cewa; Sama da mutane 21 ne aka kashe a wani hari da mayakan ‘yan tawayen kungiyar Allied Democratic Forces (ADF) suka kai kan wani cocin Katolika da ke gabashin Kongo, wanda ya hada da kona gidaje da shaguna a yankin.
A ranar Lahadin da ta gabata ne mayakan da suke da alaka da kungiyar Allied Democratic Forces (ADF) da ke samun goyon bayan kungiyar ‘yan ta’adda ta ISIS suka kaddamar da harin ta’addanci kan wata majami’ar Katolika a gabashin Kongo.
“Sama da mutane 21 ne aka kashe a ciki da wajen cocin,” Dieudonné Duranthabo, wani jami’in kungiyoyin farar hula a Komanda, ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Associated Press cewa: “Sun gano akalla gawarwakin mutane uku da suka kone, sannan an kona gidaje da dama.”
Harin ya faru ne da misalin karfe 1:00 na safiyar Lahadi a cikin wani cocin Katolika da ke yankin Komanda a gabashin Kongo. An kuma kona gidaje da shaguna da dama.