Darussan Hadisin Aikin Hajjin Manzon Allah S.A.W (2)
Published: 13th, June 2025 GMT
Hadisin Aikin Hajjin Annabi (SAW) ya koyar da cewa sumbantar Hajrul As’wad yayin da aka shiga Ka’aba da kuma sake sumbantarsa yayin fita sunnah ce, amma idan mutum bai samu iko ba; ya yi sumbar ta hanyar nuni da hannu.
Hadisin ya kuma nuna mutum zai je ya yi Safa da Marwa. Zai fara da Safa kamar yadda Annabi (SAW) ya yi.
Idan mutum ya iya, ya ce “Subhanallahi wal-Hamdulillah wa La’ilaha’illallahu wal-Lahu akbar. La’ilaha’illallahu wahdahu lashariyka lahu sadaka wa’adahu wa nasara abdahu wa hadamal ahzhaba wahdahu”. Idan mutum bai iya ba, ya yi ta fadin La’ilaha’illallah. Sai ya yi addu’a.
Daga nan ya gangaro zuwa Marwa, a kan hanyarsa zai ga wani wuri da aka sanya koriyar fitila (tsakiyar Safa da Marwa), ana so ya yi sassarfa a wurin. Zai rika yin sassarfar a duk lokacin da ya zo wurin har ya kammala Sa’ayi, ba kamar sassarfar Dawafi da ake yi a kewaye uku ba kawai. Idan mutum ya hau Marwa, a can ma zai yi Zikiri ya yi addu’a.
Hadisin ya nuna cewa idan mutum ya kare Sa’ayi a kan Marwa, to ya kammala Umurarsa sai kawai ya yi aski amma ga mai Tamattu’i.
Bayan ya koma gida zai cigaba da harkokinsa na halas ciki har da kwanciya da iyali wadda aka haramta masa lokacin da ya yi harama har sai zuwa ranar Tarwiyya da za a yi niyyar Hajji.
Wani darasin Hadisin kuma shi ne, duk wanda ya warware haraminsa bayan ya kammala Umura, zai sake yin niyyar Hajji tare da fita zuwa garin Mina. Haka nan shi ma wanda bai warware ba (mai Hajjin Kirani) zai fita zuwa Mina. Sannan yana daga sunna mutum ya yi sallolin farilla guda biyar a can Mina (Azahar, La’asar, Magriba, Isha’i da Subahi). Kuma mutum zai kwana a Mina (daren ranar Arfa).
Haka nan sunna ce mutum kar ya fita zuwa Arfa har sai rana ta fito, kuma kar ya shiga Arfa sai bayan rana ta yi zawali (lokacin Azahar). Idan mutum yana da kokari, bayan an shiga Arfa sai ya tafi can Masallacin Namira ya saurari huduba; a yi Sallolin Azahar da La’asar da shi lokaci daya. Bayan kammala sallolin sai ya dawo Arfa (hukumomin can sun sanya alamomin da ke nuna kan iyakokin Arfa).
Yana daga sunna Liman ya yi huduba kafin gabatar da sallolin nan (Azahar da La’asar). Wannan ita ce huduba ta biyu, ta farkon ita ce wacce Annabi (SAW) ya yi a rana ta bakwai ga Zhul-Hijja. Akwai kuma huduba ta uku da Liman yake yi ranar Sallah, sai kuma ta hudu a ranar tafiya ta farko (kwana biyu bayan sallah).
Hadisin ya kuma koyar da mu cewa bayan mutum ya dawo daga sallolin, zai dawo cikin Arfa ya tsaya a kan abin hawansa (idan yana da hali), don haka Annabi (SAW) ya yi. Idan bai samu ba, sai ya zauna ya cigaba da yin Zikiri da addu’o’i har rana ta fadi. Idan mutum ya samu hali ya je wurin da Annabi (SAW) ya tsaya, idan bai samu shi kenan, ko ina (inda aka shata) Arfa ne. Ana so a fuskanci Alkibla yayin tsayuwar ana addu’a. Babu laifi a je a ci abinci ko a dan yawata saboda gajiya duk dai a cikin kewayen Arfar.
Annabi (SAW) ya ce fiyayyen abin da ake karantawa ranar Arfa shi ne: “La’ila’ha’illallahu wahdahu lashariyka lahu lahul mulku wa lahul hamdu yuhyi wa yumiytu wa hul hayyu layamuutu biyadihil khair wa huwa ala kulli shai’in kadiyr”, guda 100.
Bayan an taso daga Arfa sai a nufi Muzdalifa cikin natsuwa ban da gaggawa. Annabi (SAW) ya rika jan akalar abar hawansa har kanta yana taba sirdi domin tafiya a hankali zuwa Muzdalifa. Hadisin ya kuma nuna mutum ya rika horon mutane da natsuwa a yayin komawa Muzdalifa. Da farko shi ya tabbatar da ya natsu, kana sai ya hori wasu da yin hakan.
Idan mutum ya isa Muzdalifa sai ya sauka a nan ya yi Sallolin Magriba da Isha’i a hade (Magriba cikakkiya, Isha’i kasru) ba kuma tare da yin nafila ba. Ana so da an kammala a samu wuri a huta kawai, kamar yadda aka ga Manzon Allah (SAW) ya yi.
Kwanan Muzdalifa na daga cikin sunna, amma an yi sauki ga marasa lafiya ko tsofaffi tukuf-tukuf ko mata masu kiba sosai da ake ji musu tausayin ba za su iya shiga jama’a ba masu yawa, duk sai su yi gaba don su yi Jifa da wuri kana su tafi Makka. Amma matukar mutum lafiyarsa kalau; kar ya yi gaggawa, ya tsaya ya kwana a nan Muzdalifa.
Hadisin ya kuma koyar da mu cewa sunna ce bayan mutum ya kwana a Muzdalifa bayan ya yi Sallar Asuba sai ya kama hanyar Minna zuwa Masallacin Mash’aril Haram ya dan jira zuwa wayewar gari sannan ya nufi wurin Jifa.
Idan mutum ya zo wurin da ake kira Badanil Muhassar sai ya dan yi sauri don a wannan wurin ne Allah ya halakar da Aburahata sa’ilin da ya zo zai rushe Ka’aba. Amma idan mutum bai san wurin ba shi kenan, dama shi wurin Jifa ya nufa.
A wannan ranar, Jifa daya za a yi na Jamratul Akaba da tsakuwa bakwai (wannan Hadisin ya nuna girman tsakuwar kamar na wake ko gyada wadda ko an samu wani ba za a ji ma sa ciwo ba). Duk lokacin da mutum ya daga hannu zai yi Jifar ya ce Allahu Akbar har ya kammala guda bakwan.
Yana daga falalar Jifar shaidan, Annabi (SAW) ya ce “duk wanda ya yi Jifa bai ji (a ransa) cewa an yafe masa zunubansa ba, to a sannan ne ma ya yi laifi.”
Daga nan idan mutum yana Hajjin Kirani ko Tamattu’i ne sai ya nufi wurin da zai yanka dabbarsa, idan ya gama ya yi aski sai ya nufi Makka don yin Dawaful Ifada.
Da zarar ya kammala Dawafin, to komai da aka haramta masa lokacin da ya yi harama ya halasta. Amma idan bai yi wannan Dawafin ba, an halasta ma sa sauran abubuwan da aka haramta wa mai Hajji, sai dai ban da kwanciya da iyali.
Bayan nan sai ya dawo Mina ya yi kwana biyu ko kwana uku. A yayin zaman na Mina kullum mutum zai yi Jifa uku. Daga nan Aikin Hajji ya kare, sai mutum ya je Makka ya yi Dawafin bankwana.
A takaice, wadannan su ne kadan daga cikin darussan Hadisin da Annabi (SAW) ya sanar da cewa duniya ta zo ta ga yadda zai yi Aikin Hajji a shekarar da ya fara yi (SAW).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Hadisin ya kuma Idan mutum ya idan mutum ya
এছাড়াও পড়ুন:
Mutum ɗaya ya tsira da ransa cikin 242 a hatsarin jirgin India
Jirgin saman fasinja da ke kan hanyarsa ta zuwa Landan wanda ya yi hatsari a birnin Ahmedabad na Indiya a ranar Alhamis.
Mutum ɗaya ne ya tsira daga cikin mutane 242 da ke cikin jirgin, tare da fasa gine-ginen likitoci da iyalansu.
Wani ɗan jarida na AFP ya ga gawarwakin da aka zaƙulo daga wurin da jirgin ya faɗi, da kuma bayan jirgin ƙirar Boeing 787-8 Dreamliner a rataye a gefen wani gini da ya rutsa da shi a lokacin cin abinci.
Mayar da Nijeriya tsarin jam’iyya ɗaya ba ya cikin manufofinmu — Tinubu An ciro gawarwaki sama da 200 daga jirgin Indiya da ya yi hatsari“Iftila’in da ya afku a Ahmedabad ya ba mu mamaki da kuma ɓacin rai. Abin takaici ne da ba za a iya cewa komai ba,” in ji Firayim Minista Narendra Modi a bayaninsa bayan jirgin Air India mai lamba 171 ya yi hatsari bayan tashinsa.
Kwamishinan ’yan sandan birnin GS Malik ya ce gawarwakin fasinjoji da waɗanda abin ya rutsa da su a ƙasa na daga cikin 204 da aka gano zuwa yanzu, yayin da ma’aikatan lafiya ke jinya da dama waɗanda suka jikkata a birnin.
Yayin da aka fara fargabar mutuwar duk wanda ke cikin jirgin, jami’in kula da lafiya na jihar Dhananjay Dwivedi ya shaida wa AFP cewa “an tabbatar da wanda ya tsira” kuma ana jinyar shi a asibiti.
Ɗan jaridar na AFP ya ga wani gini ya ƙone ƙurmus bayan faɗuwar jirgin, inda hayaƙi ya turnuke sama da wani ɓangare na jirgin a ƙasa.
“Rabin jirgin ya faɗo cikin ginin mazaunin da likitoci ke zaune tare da iyalansu,” in ji Krishna, wani likita da bai bayyana cikakken sunansa ba.
Krishna ya ce ya ga “kusan gawarwaki 15 zuwa 20 da suka ƙone”, yayin da shi da abokan aikinsa suka ceto ɗalibai kusan 15.
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Indiya ta ce, akwai mutane 242 a cikin jirgin, ciki har da matuƙan jirgi biyu da ma’aikatan cikin jirgin 10.
Kamfanin jirgin Air India ya ce, akwai fasinjojin Indiya 169 da 53 ‘yan Burtaniya da ‘yan Portugal bakwai, da kuma wani ɗan ƙasar Kanada a cikin jirgin da zai nufi filin jirgin saman Gatwick na Landan.