Aminiya:
2025-07-04@15:44:58 GMT

Kotu ta ci tarar Natasha N5m saboda kin bin umarninta

Published: 4th, July 2025 GMT

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja a ranar Juma’a ta sami dakatacciyar Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natsha Akpoti-Uduaghan da laifin raina kotu, sanna ta ci ta tarar naira miliyan biyar.

Da take yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Binta Nyako, ta ce Natasha ta wallafa wata wasikar zambo ta ban hakuri ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, duk da umarnin kotun na baya.

’Ya’yana na da ’yancin mallakar filaye a Abuja – Wike Makusantan Gwamnatin Buhari da suka shiga haɗakar ADC

A cewar kotun, wasikar zambon, wacce Natasha ta wallafa a shafinta na Facebook ranar bakwai ga watan Afrilu, rain ice ga umarnin da kotun ta bayar a baya ga dukkan bangarorin guda biyu.

A kan haka ne kotun ta ba Natasha wa’adin mako daya ta wallafa sakon ban hakuri a shafukan manyan jaridu guda biyu da kuma a shafin nata na Facebook.

Bugu da kari, kotun ta uamrce ta da ta biya tarar naira miliyan biyar saboda aikata laifin.

Kodayake dai hukuncin na kotun nay au ya biyo bayan bukatar hakan da Akpabio ya yi, amma kotun ta ki amincewa da dukkan ragowar bukatun nasa.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

’Ya’yana na da ’yancin mallakar filaye a Abuja – Wike

Ministan Babban Birninn Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya musanta labarin cewa ya yanka wa ’ya’yansa manyan filaye a Abuja, inda ya ce in ma haka ne suna da hakki a matsayinsu na ’yan Najeriya.

Ana dai zargin Wike da ba biyu daga cikin ’ya’yansa fili mai fadin murabba’in hekta 2,082, dayan kuma mai fadin hekta 1,740, wanda aka kiyasta darajarsu ta haura Naira tiriliyan tara.

Da yake zantawa da ’yan jarida a Abuja ranar Alhamis, Wike ya karyata labarin na cewa ya ba ’ya’yan nasa filayen a unguwannin Maitama da Asokoro.

Makusantan Gwamnatin Buhari da suka shiga haɗakar ADC Filato: Mahara sun cire hannun matashi a kan hanyar komawa gida daga jana’iza

To sai dai duk da haka, ya kare batun, inda ya ce a matsayin su na ’yan Najeriya, su ma sun cancanci su mallaki filayen matukar dai an bi ka’ida.

“Alal misali, amma ba wai na amsa haka ba ne, a ce ’ya’yana sun nemi filayen, shin ba su cancanta a ba su ba ne? ko su ’yan Ghana ne? ko kuwa a’a, kawai saboda ni ina minista shi ke nan ba su cancanta ba?,” in ji Wike.

Ministan ya zargi wasu mutane da ya ce ba su da suna daga jihar Adamawa da kitsa zancen domin kawai su bata masa suna.

“Da farko ma ka fara lissafa hekta 2,000 na fili sai ka fada min a ina za ka sami hakan a Asokoro da Maitama. Na san daga jihar Adamawa aka shirya wannan kitimurmurar,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • “ADC za ta fuskanci matsala wajen zaɓen wanda zai yi mata takarar shugaban ƙasa”
  • Kotu Ta Umarci Majalisar Dattijan Nijeriya Da Ta Gaggauta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Natasha
  • Kotu ta umarci a mayar da Sanata Natasha majalisa
  • ’Ya’yana na da ’yancin mallakar filaye a Abuja – Wike
  • An sa zare tsakanin ‘yan Kannywood da Alhikima
  • Ambaliya: Zulum ya bada umarnin tallafa wa mutanen Damboa da Askira-Uba
  • Kotu ta yanke hukuncin rataya ga dalibin da ya kashe malaminsa a Jos
  • Za a fara cin tarar masu shigar banza N50,000 a Delta
  • Kayan Aro Baya Rufe Katara