Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447: Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (1)
Published: 4th, July 2025 GMT
Lallai wannan kalanda ana ce mata ta Musulunci; gaskiya ne, ta Musulmi ce tsantsa sannan kuma ta duk halitta ce domi duk halitta suna amfani da wannan, ko sun sani ko ba su sani ba. Sai dai kawai, mu a cikin ibadojinmu Addininmu Balarabe ne kuma Larabawa da wata suke yin kirgensu, kuma shi ne ya dace da halittar Dan Adam, mun gode Allah.
Muna kira ga daukacin al’ummar Musulmi kowa ya yi tanadi na musamman kar ya bari a bar shi a baya, a bana idan Allah ya kai mu watan Rabi’ul Auwal maulidin da za a yi shi ne zai zama Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1,500 da haihuwa.
Yadda abin yake shi ne, idan ka dauki shekarun haihuwar Manzon Allah (SAW) 40 kafin a fara aiko masa da manzanci ka hada da shekarun da ya yi a Makkah guda 13 bayan fara saukar da manzanci zai ba ka shekaru 53. To, idan ka hada shekaru 53 da shekarar Hijira 1446 a bara, lissafin zai ba ka cewa a baran Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1499 da haihuwa. A bana kuma zai zama Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1,500 da haihuwa kenan.
Hatta wadanda ba su yin maulidi ya kamata a bana su yi kokari su yi wani abu ko yaya kar a bar su a baya, saboda yanzu idan Allah ya ja da rayuwarmu muka ga watan Rabi’ul Auwal mai zuwa lokacin da Manzon Allah zai cika shekara 1,500 da haihuwa, to zai yi wahala mu ga lokacin da zai cika shekara 2,000 kuma. Domin da wahala a samu wani daga cikin mutanen da ke rayuwa a doron kasa yanzu ya kara wasu shekaru 500 a raye.
A lokacin da Annabi Isah (AS) ya cika shekaru 2,000 da haihuwa an ga yadda duk duniya ta dauki murna, to mu ma ya kamata Musulmi mu girgiza duniya da bukukuwa na murnar mu ma Annabinmu (SAW) ya cika shekaru 1,500 a duniya. Wannan babban alheri ne da tarihi a rayuwarmu. Allah ya hore mana dukkan abun da za mu yi hidima da shi Albarkar Annabi (SAW).
Game da shiga sabuwar shekarar musulunci ta hijirah kuwa ta 1447 da muka shigo, za mu yi waiwaye game da tarihin kafuwar shekarar kamar yadda muka taba yi a baya saboda karatu ne mai muhimmancin gaske.
Annabi (SAW) ya umurce mu da mu bi sunnarsa, mu bi sunnar Khalifofi shiryayyu bayansa. Wannan Hijirah sunnar Manzon Allah (SAW) ce. Kuma sunnar Sayyidina Umar ce (RA) da sauran Sahabbai. Domin Sayyidina Umar ne ya kafa mana wannan kalandar ko in ce kirgen ta Hijirah.
Manzon Allah (SAW) ya yi Hijira ne a watan Rabi’ul Auwal, amma me ya sa ba a faro kirgen daga watan ba? Abin da suka yi na farowa daga Muharram akwai kaifin hankali a ciki. Akwai wata babbar hidima a cikin watan na Rabi’ul Auwal, ita ce murnar haihuwar Manzon Allah (SAW). Idan abu biyu ya zamo wuri daya sai daya ya kwace daya, kamar a ce yau ce ranar haihuwar Manzon Allah kuma yau ce ake bikin sabuwar shekarar Hijira, dole daya ya kwace daya. Bare wanda aka hada da shin ma Mauludi ne na Manzon Allah (SAW). To, shin waye ana bikin haihuwar Manzon Allah zai tuna ya yi wata murnar sabuwar shekara? Wannan ya sa suka dauko farawar sabuwar shekarar suka matso da ita baya ta fara a watan Muharram.
Sannan a halittar Allah, Allah ya shirya cewa wata guda 12 ne, idan wata ya fito ya koma a ce Muharram, idan ya fito ya yi girma har ya cika kuma ya fara karewa har ya tafi baki daya sai a ce Muharram ya kare, idan ya kuma fitowa sai a ce Safar. Watan da ya fito a Muharram shi din ne dai zai kara fitowa bayan karewarsa a Muharram din a ce Safar. Shi din ne dai yake ta wannan juyawar. To watan idan zai yi ta fitowa babu kayyadadden kirga, sai a yi ta kirgawa har zuwa miliyoyi. Shi ya sa Allah ya shirya cewa idan watan ya fito sai a ce daya, idan ya koma ya sake fitowa a ce biyu har dai a yi 12. Idan an yi haka sai a ce shekara ta kare, sai a kuma dawowa wata sabuwar shekara. To a wannan abu da Allah ya shirya, sai ya sanya Almuharram a matsayin farkon wata. La’alla Annabi Adamu (AS) yana da wani suna da yake kiran watan daban da na Larabawa ko kuma ya zama daya ne, ga shi nan dai Muharram shi ne farko.
Wanda aka gada wajen Larabawa dai Almuharram shi ne farko, sai Safar, Rabi’u Auwal, Rabi’u Akhiri, Jimada Auwal, Jimada Akhir, Rajab, Sha’aban, Ramadan, Shauwal, Zulkida sai kuma Zulhajji. Sauran wasu Yarukan ma suna da nasu, kamar Turawa suna da Janairu, Fabarairu, Maris har zuwa Disamba. Idan ka ce ai na turawan sunayen gumaka ne, to ai na Musuluncin ma ba sunayen Allah ne aka sa musu ba, kinaya ce. Kila an ambace su da yanayin da ake samu a lokacinsu. Kila kamar lokaci ya yi zafi akwai rana sosai sai a ambace shi da Ramadana, idan kuma Rajab ne kila lokacin da suke cire kan mashi ne saboda ba za a yi yaki ba, sai a ce masa Rajab. Ko wanne dai za ka ga kila saboda wani abu da yake faruwa lokacin aka ambaci watan da sunansa na wannan abun. To amma Annabi (SAW) lokacin Hajjinsa na karshe a cikin hudubarsa ya fadi cewa, “zamani ya kewaya ya kewayo”. Tun ranar da Allah ya halicce shi a Azal, aka fara da Muharram a farko, haka abin yake har zuwa 12. Sai dai, ko wane yaruka suna da nasu. Yanzu lokacin da wannan Muharram din ya shiga, ya kasance a farkon wata na 9 ne a wurinsu. Su dai suka kai shi na 9 mu babu ruwanmu, a wurin Allah dai Muharram shi ne na daya.
Don haka idan Musulunci zai yi kirge dole ya dawo Muharram, bai taba na Rumawa da sauransu ba saboda ba za su yarda ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa ba a sa Rabi’u Auwal a matsayin farkon watan shekarar Musulunci ba, da kuma kasancewar Rabi’ul Auwal shi ne na uku a watannin Musulunci, kuma ai ba za a fara kirge daga uku ba. Wannan ya sa Rabi’ul Auwal bai zama farkon shekara ba. Haka Allah ya shirya tun Azal. Haka Annabi (SAW) ya fada a ranar Hajjin ban-kwana cewa zamani ya kewaya ya kewayo. Ka ga yanzu, Allah ya ganar da Sahabbai abin da Annabi (SAW) ya koyar da su, kuma dama mutane ne Malamai, duk abin da Annabi (SAW) ya koyar da su suna yi a aikace.
Sannan me ya sa ba za mu dinga yin murnar shekarar ba a watan da aka yi Hijirar na Rabi’ul Auwal? Sai mu ce watan Rabi’ul Auwal yana da nashi gagarumin murnar da muke yi na bikin haihuwar Manzon Allah (SAW), shi kenan ka ga ba sai an rungumi wani biki na daban an sake kaiwa cikinsa ba. Kamar dai yadda aka samu sabani na ilimi a tsakanin Sayyidina Umar da Sayyidina Aliyu (RA). Domin sabanin malamai rahama ne ga al’umma.
Za mu tsaya a nan sai mako mai zuwa za mu ci gaba cikin yardar Allah. Allah ya kaimu da rai da lafiya Albarkar Annabi (SAW).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam haihuwar Manzon Allah watan Rabi ul Auwal ya cika shekaru 1 Allah ya shirya sabuwar shekara Muharram shi
এছাড়াও পড়ুন:
Ya kamata ‘yan fim su rika taimaka wa kananan cikinsu-Rukayya Abdullahi
Rukaiya Abdullahi mawakiya ce a Masana’antar Kannywood wacce daga bisani kuma ta dawo yin fim duk a masana’antar. A hirarta da Aminiya ta bayyana yadda ta fara aiki a matsayin sakatariya ta ofishin daya daga cikin masu shirya fim.
Ga yadda hirar ta kasance:
Gabatar da kanki ?
Sunana Rukaiya Abdullahi
Yaushe kika shigo Masana’antar Kannywood?
Na shigo Masana’antar Kannywood a shekarar 2020, amma zan samu kamar shekara 15 ina tare da su sai dai ban fara yin fim ba sai a 2020.
Me ya jawo hankalinki kika shigo harkar fim?
To da farko dai ba harkar fim na fara da ita ba a Kannywood, na fara da aikin sakatariya ne a wurin ’yan fim, yayan Nasiru Sarkin waka wato Musbahu Ahmad to shi ne wanda ya dauke ni aiki a matsayin sakatariya. To sakamakon akwai babana Ibrahim Mandawari shi ne bayan na nuna masa sha’awata ta yin fim to sai ya tambaye ni shin fim nake son yi ko aiki da ’yan fim? To sai na ce masa ina sha’awar yin fim ne. Sai ya ce to tunda ina sha’awar yin fim akwai wanda zai hada ni da shi ya ba ni aiki tukuna. Sai na ce ba komai ko ma aikin ya ba ni zan yi, sai ya fada min to akwai abokinsa sakataren MOPPAN Alhaji Salisu Ofisa zai yi magana da shi.
Sai ya kira shi, ya yi masa Magana, ya fada masa cewa zai turo masa wata ’yarsa. Haka ya tura ni, na je na samu Alhaji Salisu Ofisa a matsayin ’yarsa a Industry din, daga nan ne kuma sai na zama sakatariyarsa.
Wato dai da aikin sakatariya kika fara a Kannywood kafin ki koma ki rika fitowa a fim. Haka ne?
Eh haka ne, daga nan ban koma na fara fim ba sai bayan shekara 2, to a can dai sai ni ma na fara koyon waka, kuma ina ma’amala da ‘yan fim masu zuwa ofishinsa, wasu in sun zo haka muna hira da su sai su rika tambaya ta ke ’yar fim ce ?
To wata rana akwai wani darakta Ahmad Jifa da ya ce wa Alhaji Salisu sakatariyarka ta ce za ta yi fim, shi kuma sai ya ce eh, ta ce min tana sha’awar shiga fim. To ba zan manta ba, wata rana ina zaune sai Musbahu ya kirawo Ofisa ya ce ya turo masa sakatariyarsa ga wani gurbi da za ta hau a fim, shi ne da na je sai Musbahu ya ce min ke kin ce kina sha’awar yin fim, to ga wata dama da za a ba ki, ki fara fitowa a fim din, sai na ce to ina murna na tafi.
Da kika ce kin fi yin waka a fim, wakar ita ta fi rinjaya ko fim?
Gaskiya na so yin harkar fim, to sai dai na dawo ina tunanin ko Allah ne bai yi akwai abincina a harkar fim ba, ban sani ba sai wakar dai ta rinjayi fim din. Ni kuma ga shi zuciyata tana ga fim din, ina son a kira ni a ba ni aiki.
Yi bayanin irin wakokkin da kika yi yadda duk wanda ya karanta wannan labari zai iya gane cewa lallai ke ce?
Yawwa wakar da na fara farkon ita ce wakar Kwankwaso, a lokacin yana APC, sai na yi ta Buhari (marigayi tsohon Shugaban kasa ) to daga ta Buhari sai ta Sarkin Biu sannan na yi wa Dan Majalisar Jiha kuma na yi wa Dan Majalisar Taraiya shi ma dai na Biu din.
Duk da kina Kannywood a iya cewa waka ta rinjayi yin fim?
Gaskiya wakokin da na yi sun fi finafinan da na yi yawa.
Kin ce kina fitowa a matsayin ’yar tijara a fim, ko za ki yi mana bayanin ma’anar tijara a fim. Me hakan yake nufi ?
Tijara tana nufin ina fitowa a matsayin masifaffiya, wato a mafi yawan finafinai a wannan matsayin aka san ni. Ita wannan tijara ina yin ta ne da mazajena wato mijina a fim.
Yi mana karin haske dangane da irin tijarar da kike yi a fim?
Ina fada da mazajena, wato duk wanda ya gani ana so ya fahimci halayemu daban-daban, wata mafadaciya ce wata kuma mai hakuri ce kuma ni a karan kaina ba haka nake ba, kuma mazajen da nake yin fada da su, ina fada da su ne a saboda ba sa yi min adalci. Kuma irin rashin adalcin da suke yi min shi ke bata min rai har nake yi musu tijara. Wato ba ni da hakurin da zan jure abin da suke yi min.
Wannan darasi na yin tijara da kike yi a fim, ko yana yin tasiri ga mata masu irin wannan hali wadanda ake yi abin domin su suka kalla, kuma ya mazan naki ke kasancewa a fim din?
Gaskiya su ma mazajen biye min suke yi su fada, in fada
Kuma auren yana yin karko?
Aure yana karko halayya ce ta irin wasu matan ake nunawa da yadda za a yi hakurin zama da su da halinsu shi ne cin ribar zamantakewar.
A wadannan shekaru da kika yi a Kannywood wadanne irin kalubale kika fuskanta ta bangaren iyaye ko ’yan uwan ko al’umma?
Eh, to gaskiya ni dai ban samu wani kalubale daga gida ko yan uwana ba ko wasu mutane daban da ba iyayena ba. Iyayena tunda na taso ina kyautata musu kuma mu 9 ne a dakinmu, maza guda 3 nake bi, amma a cikinsu ba zan ce na fi su ba amma ni ce mafi kyautata wa iyayenmu kuma iyayenmu suna da kyakkyawan zato a kaina. Da na ce musu zan yi fim sai suka ce to Allah Ya ba ki sa’a
A al’adance idan aka kira ki da suna Delu za ki amsa sunan ko?
Insha Allahu ko Kande ko Delu idan aka kira ni sunana ne zan amsa.
Nasarori fa?
Eh to gaskiya na samu nasarori Alhamdulillahi. Babbar naasarar da na samu saboda tun da da na zo Industry din nan gaskiya ban samu wani abu ba na akasi ba har zuwa yanzu, kullum ci gaba nake samu
Wane kira za ki yi wa ‘yan Kannywood da kuma masu kallon fim din ki?
To ni babban kiran da zan yi musu shi ne ya kamata ‘yan Kannywood a rika tausayin juna, akwai dattawan gaske da ya kamata a ce ana taimakawa da wasu daga cikinmu ‘yan Kannywood ta fuskar taimakon juna musamman kamar mu na kasa-kasa kamata ya yi a ce suna sama su taimake mu. Amma sai ka ga kullum mai akwai shi suke taimaka mawa mara shi kuma ba a taimaka masa. Wato sai dai a kara wa mai karfi karfi.