Shugaban Amurka Yace Yana Jirin Hamas Cikin Sa’o’i 24 Masu Zuwa Don Tsagaita Wuta Na Kwanaki 60
Published: 4th, July 2025 GMT
Shugaban kasar Amurka Donal Trump Ya Bayyana cewa nan da kwana guda ko sa’o’ii 24 masu zuwa ne zai sani, ko kungiyar Hamas ta amince da ‘shawararsa ta tsagaita wuta da HKI kuma ta karshe a gaza.
Shafin yanar gizo ta labarai ‘Arabnews ta kasar Saudia’ ta nakalto Trump yana fadar haka a yau jumma’a.
A wani bangare shugaban ya ce yayi magana da gwamnatin kasar Saudia dangane da fadada yarjeniyar Ibrahimia wacce ya samar da ita a shugabancinsa na baya wacce take bukatar kasashen larabawa su samar da huldar jakadanci da HKI, wanda kuma ya sami nasarar a kan wasu kasashen larabawa na yankin tekun Farisa.
Daga shekara ta 2023 ya zuwa yanzu yahudawan sun kashe falasdinawa kimani 56,000 sannan fiye da dubu 12000 suka ji rauni.
Majiyar Falasdinawan ya zuwa yansu, ta bayyana cewa fatansu shi ne tsagait wutar ta kaika ta zamam din-din din.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
SON Ta Bada Shaidar Ingancin Kayayyaki Ga Wasu Kamfanoni A Kaduna
Hukumar Kula da Ingancin Kayayyaki ta Najeriya (SON) ta gudanar da bikin bayar da takardun shaidar MANCAP ga kayayyaki 31 da suka cika sharuddan inganci a ofishinta da ke Kaduna.
Taron wata babbar nasara ce ga masana’antun da abin ya shafa, duba da yadda ya kara jaddada muhimmancin tabbatar da inganci a masana’antun cikin gida na Najeriya.
A jawabin maraba da ya gabatar, Injiniya Mamza Irimiya, mai kula da ofishin SON na jihar Kaduna, ya yabawa kokarin wadanda suka sami shaidar, yana mai cewa “Samuwa ko mallakar takardar shaidar MANCAP ba abu ba ne da ake siya, tsari ne na jajircewa da kokari. Yau an karrama ku ne saboda kokarin ku, wanda hakan mataki ne farko , domin tabbatar da ingancin kayyaki abu ne da za a ci gaba da yi lokaci bayan lokaci.”
Injiniya Irimiya ya jaddada muhimmancin kirkire-kirkire da sabbin fasahohi, tare da karfafa gwiwar wadanda suka samu shaidar da su ci gaba da yin kokarin da zai kai kayayyakin su zuwa kasuwannin duniya a maimakon cikin gida kawai.
Ya bayyana cewa, shaidar tana kara wa masu amfani da kayayyakin cikin gida kwarin gwiwa kan ingancin kayayyakin Najeriya.
Wakilin Babban Daraktan SON, Dr. Ifeanyi Chukwunonso Okeke, wato Daraktan Yankin Arewa maso Yamma, Mr. Isaac Omebije Onojo, ya bayyana cewa “Bin ka’idoji a masana’antu yana da matukar muhimmanci, domin rashin yin hakan na iya jefa kasuwancin cikin barazana.Shirin MANCAP yana tabbatar da cewa kayayyakin da ake sarrafawa a Najeriya suna da inganci da aminci ga masu amfani.”
Mr. Onojo ya taya wadanda suka samu shaidar murna, yana kuma karfafa su da su ci gaba da inganta ayyukansu. Ya kuma gargadi masu masana’antu kan illar samar da kayayyaki marasa inganci, yana mai cewa hakan ba wai kawai yana cutar da masu amfani ba ne, har ma yana bata sunan masana’antun.
Ya kara da cewa, “Bin ka’idoji yana bunkasa kasuwanci tare da kare lafiyar jama’a.”
A nasa jawabin, Kwamishinan Harkokin Kasuwanci, Kirkire-Kirkire da Fasaha na jihar Kaduna ya bayyana cewa samun shaidar nan ya nuna jajircewar kamfanonin wajen kare hakkin masu amfani da tabbatar da ingancin kayayyaki.
Ya yaba wa SON bisa kokarin da suke yi wajen tabbatar da cewa kamfanoni da dama sun samu takardun shaidar domin inganta kayayyakin da ke kasuwa.
Daga cikin kamfanonin da suka samu takardar MANCAP akwai Global Care Industry Ltd., Simalox Paint and Decoration Services, Matrix Fertilizer Ltd., Euro Form, da Al-babello Trading Company Ltd., da sauransu.
Wannan nasara na da matukar muhimmanci wajen habbaka masana’antu da gamsar da bukatun kasuwa tare da taimakawa ci gaban tattalin arzikin jihar Kaduna.
Shamsuddeen Mannir Atiku