SON Ta Bada Shaidar Ingancin Kayayyaki Ga Wasu Kamfanoni A Kaduna
Published: 4th, July 2025 GMT
Hukumar Kula da Ingancin Kayayyaki ta Najeriya (SON) ta gudanar da bikin bayar da takardun shaidar MANCAP ga kayayyaki 31 da suka cika sharuddan inganci a ofishinta da ke Kaduna.
Taron wata babbar nasara ce ga masana’antun da abin ya shafa, duba da yadda ya kara jaddada muhimmancin tabbatar da inganci a masana’antun cikin gida na Najeriya.
A jawabin maraba da ya gabatar, Injiniya Mamza Irimiya, mai kula da ofishin SON na jihar Kaduna, ya yabawa kokarin wadanda suka sami shaidar, yana mai cewa “Samuwa ko mallakar takardar shaidar MANCAP ba abu ba ne da ake siya, tsari ne na jajircewa da kokari. Yau an karrama ku ne saboda kokarin ku, wanda hakan mataki ne farko , domin tabbatar da ingancin kayyaki abu ne da za a ci gaba da yi lokaci bayan lokaci.”
Injiniya Irimiya ya jaddada muhimmancin kirkire-kirkire da sabbin fasahohi, tare da karfafa gwiwar wadanda suka samu shaidar da su ci gaba da yin kokarin da zai kai kayayyakin su zuwa kasuwannin duniya a maimakon cikin gida kawai.
Ya bayyana cewa, shaidar tana kara wa masu amfani da kayayyakin cikin gida kwarin gwiwa kan ingancin kayayyakin Najeriya.
Wakilin Babban Daraktan SON, Dr. Ifeanyi Chukwunonso Okeke, wato Daraktan Yankin Arewa maso Yamma, Mr. Isaac Omebije Onojo, ya bayyana cewa “Bin ka’idoji a masana’antu yana da matukar muhimmanci, domin rashin yin hakan na iya jefa kasuwancin cikin barazana.Shirin MANCAP yana tabbatar da cewa kayayyakin da ake sarrafawa a Najeriya suna da inganci da aminci ga masu amfani.”
Mr. Onojo ya taya wadanda suka samu shaidar murna, yana kuma karfafa su da su ci gaba da inganta ayyukansu. Ya kuma gargadi masu masana’antu kan illar samar da kayayyaki marasa inganci, yana mai cewa hakan ba wai kawai yana cutar da masu amfani ba ne, har ma yana bata sunan masana’antun.
Ya kara da cewa, “Bin ka’idoji yana bunkasa kasuwanci tare da kare lafiyar jama’a.”
A nasa jawabin, Kwamishinan Harkokin Kasuwanci, Kirkire-Kirkire da Fasaha na jihar Kaduna ya bayyana cewa samun shaidar nan ya nuna jajircewar kamfanonin wajen kare hakkin masu amfani da tabbatar da ingancin kayayyaki.
Ya yaba wa SON bisa kokarin da suke yi wajen tabbatar da cewa kamfanoni da dama sun samu takardun shaidar domin inganta kayayyakin da ke kasuwa.
Daga cikin kamfanonin da suka samu takardar MANCAP akwai Global Care Industry Ltd., Simalox Paint and Decoration Services, Matrix Fertilizer Ltd., Euro Form, da Al-babello Trading Company Ltd., da sauransu.
Wannan nasara na da matukar muhimmanci wajen habbaka masana’antu da gamsar da bukatun kasuwa tare da taimakawa ci gaban tattalin arzikin jihar Kaduna.
Shamsuddeen Mannir Atiku
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Shin Babu Wata Hanyar Magance Matsalolin ASUU Ne Sai Ta Yajin Aiki?
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Shekara da shekaru kungiyar malaman jami’oi ASUU ta kwashe ta na gudanar da yajin aiki ba tare da samun biyan bukata ba.
Irin wannan yajin aiki da kungiyar malaman ke shiga ya jefa dalibai da malaman da ma harkar ilimi cikin halin ni ‘yasu a Najeriya.
NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa DAGA LARABA: Yadda Aka Yi Almajiri Ya Zama MabaraciShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wasu hanyoyin da kungiyar malaman ASUU za ta iya bi don warware matsalar ta ba tare da dogaro da gwamnatin tarayya ba.
Domin sauke shirin, latsa nan