Amurka Ta Kakabawa JMI Sabbin Takunkuman Tattalin A Jiya Alhamis
Published: 4th, July 2025 GMT
Gwamnatin kasar Amurka ta dorawa JMI sabbin takunkuman tattalin arziki ta bangaren man fetur a jiya Alhamis, a dai-dai lokacinda take maganar sake farfado tattaunawa da ita.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Scott Bessent sakataren kudi na Amurka yana fadar haka ‘Amurka zata ci gaba da gurgunta tattalin arzikin JMI da dukkan hanyoyin samun kudadenta, har sai ta dawo kan muradunta.
Wannan dai yana daga cikin shirin Amurka na takurawa tattalin arzikin kasar Iran har zuwa lokacinda mutanen kasar zasu kasa hakuri su kuma tashi su kifar da gwamnatin JMI daga cikin gida.
Wannan ne takunkuman tattalin arziki na farko wanda gwamnatin Amurkan ta dorawa JMI bayan yakin kwanaki 12 da ita da HKI suka dorawa kasar.
Takunkuman a halin yanzu ta shafi jami’an gwamnati 7 da kuma wani kamfani mai zaman kansa. Wannan dai yana nuna irin tsarin tupka da warwaran da gwamnatin Amurka take kai, tana neman sake farfado da tattaunawa da kuma kara takurawa kasar Iran a dayan bangaren.
Har’ila yau bayan yakin kwanaki 12 yana cewa ya amince China ta ci gaba da sayan man fetur na kasar Iran.
Wannan dais hi ne takunkuman tattalin arziki na 8 kan abinda ya shafi man fetur wanda gwamnatin Amurka ta dorawa Iran tun bayan dawowansa kan white a farkon wannan shekarar.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: da gwamnatin
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka Ta Dakatar Da Tura Makamai Zuwa Kasar Ukraine Saboda Kada A Sami Karancinsu A Gida
Gwamnatin shugaban Donal Trump na Amurka ta bada sanarwan rage yawan wasu makaman da take aikawa kasar Ukraine.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran na nakalto majiyar Fadar Majiyar fadar white House na bayyana cewa pentagon ko ma’aikatar tsaron kasar ta bada rahoton cewa rumbun ajiyar makaman kasar yayi kasa sosai don haka akwai bukatar a dakatar da aikawa kasar Ukraine wasu makaman, kamar garkuwan kare sararin samaniya da kuma makamai masu taimaka mata wajen kare kanta.
Labarin ya nakalto Anna Kelly kakakin fadar white house na cewa an dauki wannan matakin en don sanya Amurka a gaba, duk da cewa ba zata dakatar da bawa kawayenta taimakon da ya dace ba.