An Bude Mafiya Yawan Tashoshin Jiragen Sama A Iran Bayan Tsaida Yaki
Published: 4th, July 2025 GMT
Bayan an rufe sararin samaniyar kasar Iran saboda yaki na kwanaki 12 wanda HKI ta dorawa kasar a ranar 13 ga watan yunin da ya gabata, a yau Jumma’a a bude zirga-zirgan jiragen saman a duk fadin kasar daga karfe 5 na safe zuwa 6 na yamma daga ranar Jumma’a 4 ga watan July 4, 2025.
Sake dawo da zirga zirgan jiragen sama yana daga cikin matakan da hukumomi a Iran suka dauka don dawo da nutswa a cikin kasar bayan yakin kwanaki 12 da HKI.
Hukumar zirga zirgan jiragen sama na kasar ta dakatar da sauka da tashin jiragen samane jin kadan bayan da HKI ta awkawa Iran da ya ki a ranra 13 ga watan yuni don lafiyar fasinjoji. Dukkan tashoshin jiragen sama a bude suke sai da birnin Tabriz da kuma Esfahan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisa ta gayyaci CBN da bankunan kasuwanci kan yawan cire wa kwastomomi kuɗaɗe
Majalisar Wakilai ta ƙaddamar da bincike kan ƙaruwar koke-koken ’yan Najeriya kan yawan cire musu kuɗaɗe ba tare da bayani ba daga asusun ajiyarsu da bankunan kasuwanci ke yi.
Wannan mataki ya biyo bayan amincewa da wani ƙuduri da ɗan majalisa Hon. Tolani Shagaya (APC, Kwara) ya gabatar, inda ya nuna damuwa kan abin da ya kira “cire kuɗaɗe ba tare da bayani ba, da kuma yawan kuɗaɗen da ake karɓa ba bisa ka’ida ba,” duk da dokokin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kafa.
An kama mata da miji suna safarar makamai a Kaduna Kofin Duniya: Da sauran rina a kaba duk da Najeriya ta ci Jamhuriyar Benin 4-0Yayin gabatar da ƙudurin a zaman majalisa ranar Talata, Shagaya ya ce duk da cewa ana sa ran bankuna su bayar da muhimman ayyukan kuɗi cikin farashi mai sauƙi, yawancin ’yan Najeriya na fuskantar cire kuɗaɗe da dama.
Ya ce cire kudade kamar kuɗin saƙon SMS, kuɗin gyaran kati, kuɗin kula da asusu, kuɗin canja wuri tsakanin bankuna, harajin tambari, da wasu cire-cire da ba a bayyana ba, da dama daga cikinsu ma ana maimaita su ko ba a bayyana su yadda ya kamata ba.
Ya nuna damuwa cewa irin waɗannan halaye na ci gaba da faruwa duk da cewa CBN ya fitar da ƙa’idoji masu bayyani kan yadda za a sarrafa kuɗaɗen da bankuna ke karɓa, amma yawancin bankuna na take waɗannan ƙa’idoji ba tare da jin tsoron hukunci ba.
“Irin waɗannan halaye na zalunci ya fi shafar ’yan kasuwa, masu ƙaramin karfi, ɗalibai, da ƙungiyoyin da ke cikin mawuyacin hali na tattalin arziki.
“Idan ba a gaggauta bincike da ɗaukar mataki ba, za su ci gaba da rage amincewar jama’a ga tsarin banki, su ƙara yawan waɗanda ba su da damar shiga harkokin kuɗi, kuma su lalata manufofin CBN na faɗaɗa damar shiga tsarin kuɗi,” in ji shi.
Bayan amincewa da ƙudurin, Majalisar ta bukaci CBN da ya fitar da jerin kuɗaɗen da aka amince da su cikin sauƙi ta yadda kowa zai fahimta, tare da tabbatar da aiwatar da hukunci ga bankunan da suka karya doka.
’Yan majalisar sun kuma bukaci babban bankin ƙasa da ya kafa wata hanya mai sauƙi da inganci don karɓar koke-koke daga abokan ciniki da suka fuskanci cire kuɗaɗe ba bisa ka’ida ba ko fiye da kima.
Bugu da ƙari, Majalisar ta bukaci Hukumar Kare Masu Sayen Kaya (FCCPC) da sauran hukumomin da suka dace da su fara yaɗa shirye-shiryen wayar da kan jama’a a faɗin ƙasa don sanar da su haƙƙinsu dangane da kuɗaɗen da bankuna ke karɓa.
Ƙudurin ya kuma umarci Kwamitin Majalisa kan Dokokin Banki da Harkokin Bankuna da su gayyaci CBN da manyan bankunan kasuwanci don bayyana dalilan da ke sa ake ci gaba da cire kuɗaɗe ba bisa ka’ida ba.
An umurci kwamitocin da su dawo da rahoto ga Majalisar cikin makonni huɗu domin ɗaukar matakin da ya dace na gaba.