NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya
Published: 14th, March 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Rashin aikin yi na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da Najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman idan aka yi la’akari da yadda ake ci gaba da samun matasa masu lafiya da kuzari amma ba su da aikin yi.
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta fitar da rahoto da ke nuna cewa rashin aikin yi ya ƙaru a Najeriya da kaso 5.
Haka kuma, binciken ya nuna cewa mutane da ba su yi karatu mai zurfi ba sun fi samun aiki sama da waɗanda suka yi karatu mai zurfi.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai duba matsalar rashin aikin yi da kuma hanyoyin da za a iya bi don magance ta.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: karatu Rashin Aiki
এছাড়াও পড়ুন:
Sanata Sunday Marshall Katung Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC
Sanata Sunday Marshall Katung, wanda ke wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu a majalisar dattawa, ya sanar da hukuncin da ya yanke na komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yana mai cewa wannan mataki ne da ya dace domin inganta aikin wakilci da kuma tabbatar da ƙarin haɗin kai ga al’ummar mazabarsa.
A cikin wata sanarwa mai taken “Sabon Babin Rayuwa: Saƙon Haɗin Kai da Manufa Ɗaya,” Sanata Katung ya bayyana cewa wannan shawara ta biyo bayan dogon shawarwari da aka yi da mazauna mazabarsa, jagororin siyasa, iyalansa da abokan aikinsa.
Ya ce, “Wannan sauyin matsayi yana fitowa ne daga niyyar gaskiya ta yin wa mutanenmu hidima cikin inganci, da tabbatar da cewa muryarmu tana da ƙarfi kuma ana jin ta a manyan teburan yanke shawara da ke tsara makomar al’ummarmu.”
Ya ƙara da cewa wannan mataki ya zama dole ne bayan kiraye-kirayen da aka yi daga sassa daban-daban na mazabarsa, tare da yabawa irin sha’awar da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, suka nuna wajen yin aiki tare da shi domin kawo “ci gaba mai tarihi da ban mamaki” a yankin.
Sanata Katung, yayin canza shekan tare da Hon. Daniel Amos da wasu abokansa a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, ya nuna gamsuwa da “ayukan ci gaban” jam’iyyar APC a yankin Kaduna ta Kudu, yana mai cewa suna nuna adalci, daidaito, da ci gaba.
Ya ce, “Zamanin warewa da nuna bambanci, musamman a baya-bayan nan, yana gushewa, kuma ana maye gurbinsa da gwamnatin da ke da manufa da haɗin kai.”
“Saboda haka muna matsawa gaba domin tabbatar da cewa waɗannan nasarori sun dore kuma sun yadu zuwa sauran al’ummomi da dama a yankin,” in ji shi.
Sanatan ya kuma roƙi abokai da abokan aiki da ba su goyi bayan wannan mataki nasa ba, da su mutunta ra’ayoyi daban-daban, tare da kaucewa barin siyasa ta kawo rarrabuwar kawuna a tsakaninsu.
Ya ambaci kalmar Thomas Jefferson da cewa, “Ban taɓa ɗaukar bambanci a ra’ayi na siyasa, addini ko falsafa a matsayin dalilin janye ƙauna daga aboki ba.”
“A tare, mu ci gaba da zama ɗaya a manufa, mu dage da fata, kuma mu mai da hankali wajen samar da makoma mafi kyau ga al’ummar Mazabar Kaduna ta Kudu.”
Sanata Katung ya tabbatar da ƙudurinsa na ci gaba da aiki don haɗin kai da cigaba.
Daniel Karlmax