Aminiya:
2025-08-01@16:00:56 GMT

’Yan bindiga sun sace mutum 10 da raunata 2 a Kaduna

Published: 13th, March 2025 GMT

Wasu ’yan bindiga da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu ’yan ƙauye su goma daga wasu unguwanni uku da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a daren ranar Larabar, da misalin ƙarfe 2 na tsakar dare inda wasu gungun ’yan bindiga suka kai farmaki a unguwar Unguwan Yashi-Maraban Kajuru tare da yin garkuwa da mutane shida.

Kano: Gobara ta kashe mutum 7 da lalata kadarorin N50m a Fabrairu Galibin ’yan Najeriya na neman muƙaman gwamnati don arzuta kansu — Obasanjo

Waɗanda aka sace su ne: God-Dream Ladan, Lady God-Dream, Philip Mudakas, Mercy Philip, Bitrus Philip, da Gmen Philip.

Hakazalika, a ƙauyen Makyali, wasu mutane biyu sun samu raunuka na harbin bindiga, kuma a halin yanzu ana jinyarsu a asibitin Maraban Kajuru bayan ’yan bindiga sun kai wa unguwar hari.

An kuma yi garkuwa da wasu mata biyu Rahina Yahaya da Zulai Yahaya a ƙauyen. Waɗanda suka jikkata dai sun haɗa da: Ubale Yahaya da Abdullahi.

An samu rahoton cewa gungun ’yan bindigan sun koma Ungwan Mudi Doka da misalin ƙarfe 4 na asubahi inda suka yi garkuwa da wasu mutane biyu – Amos Michael da Samita Amos.

Muƙaddashin Hakimin Kufana, Stephen Maikori ya tabbatarwa Aminiya faruwar lamarin a ranar Alhamis, inda ya ce a baya-bayan nan an samu raguwar kai hare-haren, amma kuma a cikin makon nan ne suka sake kunno kai.

“Ya zuwa yanzu, an tafi da mutane goma, yayin da biyu suka samu raunuka, yanzu suna karɓar magani. Muna roƙon a ƙara ɗaukar matakan tsaro cikin gaggawa da ɗaukar matakin ceton rayuka da dukiyoyi a cikin wannan yankin,” in ji shi.

Ya kuma ƙara da cewa an kai rahoton faruwar lamarin ga hukumomin tsaro a kan lamarin.  A halin da ake ciki dai har yanzu gwamnatin jihar da rundunar ’yan sanda ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan, an kasa samunsa ta wayar tarho har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

Wasan Kwallon Mutum-Mutumi Ya Nuna Yadda Sin Ta Shirya Wa Karbar Bakuncin Wasanninsu Na Duniya

Wadannan ’yan wasan kwallon kafa na mutum-mutumi sun sake nuna bajintar da kasar Sin ke nunawa a fagen kere-keren mutum-mutumi masu siffar dan’adam da kuma yadda masana’antar bangarensu ke samun ci gaba cikin hanzari a kasar.

A watan Agusta mai kamawa ne kasar Sin za ta karbi bakuncin gasar wasannin motsa jiki na mutum-mutumi masu siffar dan’adam. Kuma wannan wasan kwallon kafa na mutum-mutumi da aka gwabza fafatawar karshe a dandalin wasannin motsa jiki na fasahar zamani da ke birnin Beijing, wata kyakkyawar shaida ce a kan yadda kasar ta shirya wa karbar bakuncin wannan gasa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Zulum Ya Sauke Kwamishinoni Biyu Tare Da Maye Gurbinsu Da Wasu
  • Yanzu-yanzu: Sanata Dino Melaye Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
  • Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa
  • Hare-hare: ’Yan bindiga sun raba mutum 5,000 da muhallansu a Katsina
  • Wasan Kwallon Mutum-Mutumi Ya Nuna Yadda Sin Ta Shirya Wa Karbar Bakuncin Wasanninsu Na Duniya
  • Kwamandan NDA Ya Bukaci Dalibai Su Dage da Karatu a Taron FGC Malali
  • ’Yansanda Sun Ceto Mutane 28 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Katsina
  • Yadda ’yan bindiga suka tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina
  • ’Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina
  • Ku Daina Kashe Mutane Ko Ku Miƙa Wuya – Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Bindiga