Sojojin Iran Sun Ce A Shirye Suke Su Mayar Da Martani Akan Kowace Barazana Ga Tsaron Kasar
Published: 13th, March 2025 GMT
Kwamandan sojojin kasa na JMI Laftanar-Janar Kiyomars Haydari ya bada sanarwan cewa; A bisa umranin jagoran juyin musulunci Imam Sayyid Ali Khamnei , sojojin kasa na JMI suna cikin shirin ko ta kwana domin mayar da martani akan kowace irin barazana ga tsaron kasar.
Laftanar janar Haidari ya kuma ce: A halin yanzu da akwai rundunoni 11 da su ke cikin shiri a kan iyakoki kasar domin sanya idanu da tattara bayanai saboda tabbatar da tsaron kasar.
Kwamandan sojan kasa na Iran ya kuma ce; Saboda sojojin suna cikin shirin ko-ta-kwana ne, barazanar da ake fuskanta ta zagwanye, da hakan ya ke a matsayin kandagarko.
Har’ila yau Laftanar janar Haidari ya yi ishara da rawar dajin da sojojin kasa su ka yi, har sau uku a cikin shekarar hijira Shamshiyya ta 1403. Sannan da wadanda za su a sabuwar shekara da za ta shigo.
Ya ce za’a gudanar da wani atisayen wanda zai da ce da girman barazanar da ake fuskanta.
Haidari ya kammala da cewa a sabuwar shekarar Iran da za a shiga, za ta zama ta kara yawan karfin tsaron kasar ne, domin takawa makiya birki.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Rasha Ta Mayar Da Martani Ga Shugaban Amurka Kan Gindaya Wa’adin Kawo Karshen Yakin Ukraine
Martanin da Rasha ta mayar dangane da sabon wa’adin Trump na kawo karshen yakin Ukraine
Mataimakin shugaban kwamitin tsaron Rasha Dmitry Medvedev ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump game da takaita wa’adin tsagaita bude wuta tsakanin Rasha da Ukraine, yana mai cewa matakin kunna yaki ne.
Medvedev ya rubuta a kan dandalinsa na X cewa: “Trump yana wasa, irin wasan gargadi tare da Rasha: Na kayyade mata kwanaki 50 ko 10 … amma ya kamata ya tuna abubuwa biyu: Na daya Rasha ba Isra’ila ba ne ko kuma Iran. Na biyu. duk wani sabon gargadi yana matsayin barazana ne kuma matakin kunna wutar yaki ne. Ba tsakanin Rasha da Ukraine ba, amma tare da kasarsa. Amurka ta nshiga taitayinta!”
Da sanyin safiyar litinin ne shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da rage wa’adin kwanaki 50 da ya sanya a farkon wannan wata na tsagaita bude wuta a Ukraine zuwa tsakanin kwanaki 10 zuwa 12. Ya ce “ba ya ganin wani ci gaba wajen warware rikicin Ukraine” kuma “babu amfanin jira.”