Kungiyar Hamas Zata Saki Fursunoni 6, Yayin Da’Yan Sahayoniyya Zasu Saki Fursunonin Falasdinawa 602
Published: 22nd, February 2025 GMT
Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas zai saki fursunonin ‘yan sahayoniyya guda 6 a madadin fursunonin Falasɗinawa 602
A cikin tsarin yarjejeniyar musayar fursunoni na Ambaliyar Al-Aqsa da kuma a cikin kashi na bakwai na matakin farko na shirin musaya … za a sako wasu sabbin fursunonin Isra’ila guda 6 da suke hannun dakarun Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas, a ranar Asabar, tare da bayyana sunayensu.
A sakamakon haka, mamayar za ta saki fursunonin Falasdinawa 602: Falasdinawa 50 daga cikinsu an yanke musu hukuncin daurin rai da rai ne, wasu 60 daga cikinsu kuma an yanke musu hukunci mai tsawo, da kuma fursunoni 47 na Wafa al-Ahrar da aka sake kama su, bayan zaman gidan yari a baya. Haka nan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila zata saki fursunonin Falasdinawa 445daga cikinmazauna Gaza wadanda aka kama su bayan ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023.
Fursunonin Isra’ila shida da za a sako a ranar Asabar din nan, za a kara da fursunoni goma sha tara masu rai da kuma matattun yahudawan sahayoniyya guda hudu da gwamnatin Isra’ila ta karbe su tun bayan da aka cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza da ta fara aiki kwanaki 34 da suka gabata.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Isra’ila Ta Kai Hari Ga Rumbun Magungunna A Kudancin Gaza
Hukumar da ke bayar da agajin magungunna ga Falasɗinawa ta ƙasar Birtaniya ta ce Isra’ila ta kai wani hari da ya afkawa rumbun ajiyar magungunna na Asibitin Nasser da ke yankin Khan Younis a tsakar daren da ya gabata a kudancin Gaza .
Hukumar ta ce harin ya auku ne “lokacin da ake kwashe Falasɗinawan da aka kashe da waɗanda aka jikkata zuwa asibiti, bayan wasu jerin hare-haren da Isra’ila ke kai”.
Daga cikin magungunnan da harin ya lalata sun haɗa da waɗanda hukumar ta samar wa asibitin na Nasser. “A yanzu dai muna kallo dukan magungunna da muka bayar tallafi sun ƙone ƙurmus” in ji kakakin hukumar.
Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta fitar da hotunan wuraren da harin ya shafa. Kafar yaɗa labaran Falasɗinawa ta bayar da rahoannin cewa hare-haren da aka kai a birnin sun yi sanadiyyar mutuwar gomman mutane.
Rundunar sojojin saman Isra’ila ta fitar da wata sanarwa cewa a cikin kwana guda kaɗai ta kai hare-hare har 160 a wurare daban-daban da ta ke hara.