Aminiya:
2025-07-04@22:19:04 GMT

Gwamnan Bauchi ya ƙaddamar da kwamitin ƙirƙiro da sabbin masarautu

Published: 4th, July 2025 GMT

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya ƙaddamar da wani babban kwamitin ƙirƙiro masarautu da gundumomin hakimai a jihar.

An ƙaddamar da kwamitin ne a wani mataki na magance buƙatu da dama daga al’ummomi daban-daban da kuma inganta al’adu da tsarin mulki na asali a faɗin Jihar Bauchi.

Abba ya naɗa Ahmed Musa a matsayin Babban Manajan Kano Pillars An gano wasu bama-bamai 56 da ISWAP suka binne a Borno

Gwamna Bala ya shaida wa kwamitin da ya sake duba buƙatu na samar da sabbin masarautu a faɗin jihar.

Ya ce, aikin kwamitin shi ne inganta harkokin gudanar da mulki na cikin gida da inganta al’adu da kuma ƙarfafa muhimmiyar rawar da sarakuna ke gudanarwa wajen haɗin kai da ci gaba.

Gwamnan ya bayyana matakin a matsayin alƙawarin da gwamnatinsa ta yi na tabbatar da adalci da haɗa kai da kuma ƙarfafa tsarin mulki da ci gaba a Jiha da ƙananan hukumomi.

Ya bayyanawa kwamitin da ya ba da shawarar al’ummomin da suka cancanta na sabbin masarautu, da ba da shawarar tsarin gudanarwa don ingantaccen aiki na sabbin masarautu, masarautu ko gundumomi da gabatar da cikakken rahoto tare da shawarwari masu dacewa cikin makonni takwas.

Gwamnan ya buƙaci kwamitin da ya gudanar da aikinsa cikin gaskiya da himma da kuma adalci.

Ya bayyana cewa, shirin na cika alƙawuran siyasa ne da nufin karkatar da hukumomi don samar da ingantattun ayyuka da kuma ƙara rarraba albarkatu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: ƙirƙiro masarautu sabbin masarautu

এছাড়াও পড়ুন:

Hadiman gwamnan Kano sun haura 300 bayan naɗa wasu sabbi 19

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin wasu sabbin hadimai 19 da za su yi aiki a matsayin Manyan Mataimaka na Musamman domin ƙara inganta aikin gwamnati a jihar.

Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

Mai shekara 70 ya kashe ƙanwarsa kan gadon gona a Jigawa Gwamnan Bauchi ya ƙaddamar da kwamitin ƙirƙiro da sabbin masarautu

Yanzu adadin hadiman da ke aiki da Gwamna Abba sun zarce mutum 300.

Hadiman sun haɗa da Masu Ba da Shawara na Musamman, Manyan Mataimaka na Musamman, Mataimaka na Musamman da kuma Masu Taimaka Masa.

Gwamnan ya fara naɗa hadimansa ne a ranar 16 ga watan Yunin 2023, inda ya naɗa mutum 14 ciki har da Manyan Mataimaka bakwai, Mataimaka na Musamman uku da Masu Taimaka Masa guda huɗu.

Daga baya, a ranar 18 ga watan Yuli, 2023, ya sake naɗa ƙarin mutum 15 a matsayin Masu Ba da Shawara na Musamman.

A ranar 7 ga watan Agusta, 2023, ya sake naɗa mutum 52, wanda ya kai jimillar hadimansa zuwa 81 a wancan lokaci.

A ranar 2 ga watan Satumba, 2023, ya sake naɗa ƙarin mutum 115; waɗanda suka haɗa da Masu Ba da Shawara 14, Manyan Mataimaka 57 da Masu Ɗaukar Rahoto na Musamman 44.

Hakazalika, a ranar 27 ga watan Satumba, ya sake ƙara mutum 94, wanda ya adadin ya kai zuwa 290.

Bayan haka, a ranar 29 ga watan Satumba, 2023, ya ƙara naɗa mutum 106; ciki har da Manyan Mataimaka 63, Mataimaka na Musamman 41 da wasu 12.

Yanzu kuma, ya sake naɗa mutum 19, wanda adadin hadimansa ya haura 300.

Daga cikin sabbin waɗanda ya bai wa muƙamai akwai Hon. Sunusi Kata Madobi da aka naɗa a matsayin Mataimaki na Musamman Kan Harkar Gidan Rediyo na I domin maye gurbin marigayi Abdullahi Tanka.

Mika’ilu Shu’aibu (Ghari) ya zama Mataimaki na Musamman Kan Harkokin Hisbah, yayin da Muhktar Abdullahi Shuwaki (Ghari) ya zama Mataimaki na Musamman Kan Harkokin Filaye.

Injiniya Sagir Lawan Waziri (Ghari) ya samu muƙamin Mataimaki na Musamman Kan Hakkokin Al’umma (Sashen Ayyuka).

An naɗa Najeef Abdulsalam a matsayin Mataimaki na Musamman Kan Masu Sana’o’i Maza, sai kuma Huwaila Iguda da aka naɗa a matsayin Mataimakiya ta Musamman Kan Masu Sana’o’i Mata.

Naziru Hamidu Bako ya zama Mataimaki na Musamman Kan Hukumar KAROTA, sai Usman Abbas Sunusi da zai riƙe matsayin Mataimaki na Musamman Kan Harkokin Taruka na II.

Injiniya Usman Kofar Naisa zai kasance Mataimaki na Musamman Kan Filin Wasanni na Mahaha, yayin da Danladi Alhassan Mai-Bulala ya zama Mataimaki na Musamman Kan Wayar da Kai II.

Abdulkhadir Umar Kwankwaso ya samu muƙamin Mataimaki na Musamman Kan Harkar Ilimi (Abuja), sai kuma Balarabe Aminu Yusuf wanda aka daga darajarsa zuwa Mataimaki na Musamman Kan Harkokin Gida III (Gidan Gwamnati).

Shukurana Garba Langel ya zama Mataimaki na Musamman Kan Wayar da Kai (Kano ta Arewa), sai Mustapha Ma’aruf Diso da aka naɗa Mataimaki na Musamman Kan Harkar Kiwon Lafiya A Matakin Farko (Primary Healthcare).

Garba Yahaya Labour ya zama Mataimaki na Musamman Kan Harkokin Sufuri na I, yayin da Humaira Sharif ta zama Mataimakiya ta Musamman Kan Wayar da Kan Mata.

Muttaka Sani Gaya, ya samu muƙamin Mataimaki na Musamman Kan Ƙungiyoyin Masu Goyon Bayan Gwamnati na III, Gausu Nuhu Wali ya zama Mataimaki na Musamman Kan Mawaƙan Gargajiya, sai kuma Hadiza Sale (Baby) da aka naɗa a matsayin Mataimakiya ta Musamman Kan Tsaftar Muhalli.

Gwamnatin Kano ta yi fatan sabbin hadiman za su yi amfani da ƙwarewarsu da kishinsu wajen taimakawa wajen cimma burin gwamnatin na mayar da hankali kan ci gaban jama’a da shugabanci na gari.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ku Zama Cikin Shirin Samun Sauyin Yanayi – NiMet
  • Shugaban Kwamitin AU: Kasar Sin Aminiya Ce Da Za A Iya Dogaro Da Ita
  • Hadiman gwamnan Kano sun haura 300 bayan naɗa wasu sabbi 19
  • Abba Ya Yi Sabbin Naɗe-naɗe A Jihar Kano
  • NUC Da Shugabannin Makarantu Sun Yi Kira A Sanya Tsarin Kere-kere A Jami’o’in Nijeriya
  • Tinubu Ya Ƙaddamar Da Cibiyar Fasahar Da Aka Lalata Lokacin Zanga-Zanga A Kano
  • 2027: David Mark zai kai mu ga nasara — ADC
  • Me Ya Sa JKS Mai Tsawon Tarihin Sama Da Shekaru 100 Ta Dore A Kan Mulki
  • David Mark ya fice daga PDP, ya shiga haɗaka don ƙalubalantar Tinubu