An gano wasu bama-bamai 56 da ISWAP suka binne a Borno
Published: 4th, July 2025 GMT
Dakarun rundunar sojin ‘Operation Haɗin Kai’ sun ce dakarunsu sun kai ga nasarar gano wasu bama-bamai guda 56 da ake zargin mayaƙan ISWAP ne suka binne a kan gadar Marte zuwa Dikwa da ke Jihar Borno.
Sojojin sun kuma daƙile wani harin da ka iya zama wani babban harin da zai haifar da mummunan ɓarnar rayuka da dukiyoyi.
Majiyoyin da ke da alaƙa da rundunar ta OPHK ta tabbatar da a ranar Juma’a cewa, aka gano bama-baman a wani samame da sojojin na runduna ta 24 da ke Dikwa, Jihar Borno suka yi.
A cewar majiyar, ’yan tada ƙayar bayan sun sanya bama-baman ne a kan gadar da dabarar da nufin yin ɓarna mai yawa tare da daƙile zirga-zirgar sojoji da fararen hula a kan hanyar.
Majiyar ta ce, “Sojojin da ke aiki da sahihan bayanan sirri, sun gano na’urorin kafin su tarwatse.
Ya ƙara da cewa, nan take aka tura tawagar da ke kawar da bama-bamai (EOD) zuwa wurin domin taimakawa wajen tabbatar da tsaron na’urorin don kwance su kafin su kaiga tashi.
Hotunan farmakin sun nuna wasu bama-bamai da aka gano a jikin wasu muhimman sassan gadar da ta haɗa manyan garuruwa biyu a Arewacin Borno.
Majiyoyin sun ce saurin shiga tsakani da sojojin suka yi ne ya daƙile wani mummunan harin ta’addanci, wanda ake iya kaiwa jami’an tsaro, al’ummomin farar hula da masu ayyukan jin ƙai a yankin.
Ana ci gaba da sa ido a yankin, yayin da ake ci gaba da aikin share sauran abubuwan fashewa a yankin da zarar an gano su.
Don haka rundunar ta OPHK ke kira ga jama’a musamman masu abubuwan hawa da su riƙa yin taka tsantsan gami da lura akan waɗannan hanyoyin tare da kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga jami’an rundunar don magance shi akan lokaci kafin ya kai ga haddasa mummunan lamari.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dikwa ISWAP Marte Operation Haɗin Kai
এছাড়াও পড়ুন:
PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu da ke da alaƙa da Wike
Rikici a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, na ƙara ƙamari, bayan da jam’iyyar ta dakatar da sakatarenta na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, da wasu da ake ganin ’yan tsagin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike ne.
Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba ne, ya sanar da dakatarwar bayan wani taro da Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC), ya gudanar a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.
Zargin Kisan Kiristoci: Maganar Trump a kan Najeriya tsagwaron ƙarya ce — Shehu Sani Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia ta yi tazarce da kashi 97 an ƙuri’uSauran da aka dakatar sun haɗa da Mai Bai wa jam’iyyar Shawara kan Harkokin Shari’a, Kamaldeen Ajibade (SAN); Sakataren Tsara Harkokin Jam’iyya, Umar Bature; da Mataimakin Mai Bai wa jam’iyyar Shawara kan Harkokin Shari’a.
Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda aka dakatar ba sa halartar tarukan jam’iyyar.
An dakatar da su na tsawon wata ɗaya, sannan aka miƙa lamarinsu ga Kwamitin Ladabtarwa na jam’iyyar PDP domin gudanar da bincike.
Waɗanda aka dakatar ’yan tsagin Wike ne, kuma sun raba ƙafa a rikicin da jam’iyyar ke fuskanta tun bayan zaɓen 2023.
Idan ba a manta ba, a ranar Juma’a ne, wata Babbar Kotu a Babban Birnin Tarayya, ta dakatar da PDP daga shirin gudanar da babban taronta da aka tsara yi a Ibadan, Jihar Oyo, a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025.
Sai dai jam’iyyar ta ce za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin, kuma hakan ba zai hana ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da taron ba.
Wasu daga cikin ’ya’yan jam’iyyar sun ce rashin jituwa a PDO shi ne babban dalilin da ya sa aka kai ƙarar taron’ kotu.