Leadership News Hausa:
2025-09-17@23:15:04 GMT

Yawaitar Al’umma: Martanin Karl Marx Ga Rabaran Malthus

Published: 4th, July 2025 GMT

Yawaitar Al’umma: Martanin Karl Marx Ga Rabaran Malthus

Bayan Plato sai kuma masani Aristotle shi ma ya zo da ta shi fahimtar, a shekara 340 kafin zuwan Annabi Isah (AS). A tunani irin Aristotle, yawaitar al’umma ba ta da wani alfanu, don haka hakki ne da ya rataya kan gwamnati ta kayyade yawan iyalin da mutum zai iya haifa. Idan matar mutum ta samu juna biyu (ciki) bayan sun kai adadin da gwamnati ta shardanta, ba su da wata mafita, in ji Aristotle, da ya wuce a zubar da cikin.

Shi kuwa masani Abdurrahman Ibn Khaldun wanda aka haifa a ranar 27 ga watan Mayun 1332 ya na daga cikin wadanda ke goyon bayan yawaitar al’umma. Ibn Khaldun ya ce, rashin tunani da hangen nesa ne ma mutum ya yi da’awar kin jinin yawaitar al’umma, saboda duk inda aka samu yawaitar al’umma ana samun yawaitar taimakekeniya da ayyuka na musamman. Za a samu kwararru a fannoni daban daban, wanda hakan zai kawo ci gaba.

Wadannan ‘yan misalan sun nuna mana cewa ashe an jima a tarihin duniya ana fafata takaddama dangane da yawaitar mutane a cikin al’umma. Wani Masani mai suna Rabaran Thomas Malthus wanda aka haife shi a shekarar 1766 a kasar Scotland, amma kusan karatunshi duk a kasar Ingila ya yi. A shekarar 1798 ya fidda nashi ra’ayin dangane da wannan tattaunawa a littafinsa mai suna ‘First Essay on Population’, inda a ciki ya kawo wasu abubuwa guda biyu. Na farko ya ce, mutane a duniya suna bukatar abinci domin su rayu. Na biyu kuma, dabi’a ce ta dan Adam haihuwa (kowa na son ya haihu).

Malthus ya ci gaba da karin bayani da cewa matukar ba a samar da wata hanyar yin garanbawul ga wannan yawaitar haihuwar na mutane ba, toh lallai akwai barazanar tulin matsaloli. A nazarinshi, muddin aka ci gaba da haihuwa barkatai, watan watarana yawan mutane zai fi karfin abincin da ake iya samarwa. Kuma duk ranar da yawan mutane ya rinjayi na abincin da su ke iya samarwa, za a fada wa ukubar yunwa, masifa, talauci da cututtuka.

A nan Malthus ya na kokarin nuna mana cewa idan har al’umma ba ta bi hanyoyin kiyaye yawaitar mutane ba, yawaitar mutanen zai nemarwa kanshi mafita, kuma mafitar ita ce ta hanyar wanzar da mugun talauci.

Amma, in ji Malthus; idan al’umma ta bi hanyar da ya kira ‘Prebentibe checks’, to za a tsallakewa matsalar yunwa da wanzuwar talauci. Wannan hanyoyin sun hada da: Jinkirin aure, da kauracewa mata na wani lokaci wanda a harshen turanci ake kira da ‘Permanent Celibacy’.

Idan a al’adar al’umma ana kulla sabon aure ne ga wadanda suka kai shekaru 15, sai Malthus ya ce, saboda kiyayewa sai a mutum ya shekara 30 sannan zai yi auren farko. Haka nan kuma kar a yarda mutum ya yi aure har sai an tabbatar da cewa ya gina kanshi ta yadda zai iya ciyar da iyalin ya kuma dauki dawainiyar gidan yadda ya kamata don gudun talauci.

A wurin Rabaran Thomas Malthus, haramun ne yin amfani da magunguna ko matakan jinkirta haihuwa. A maimakon haka gwamma ka jinkirta yin auren, saboda magungunan hana haihuwa a wurinshi sun sabawa da’a da ka’idar addini. A karshe ya kamata a gane cewa shi a wurin Malthus, duk wani rikici talaka ne ke janyowa kanshi, saboda shi ne baya yin aiki tukuru don samar da abinci, sai dai aukin haihuwa da tara iyali.

Masana irinsu Dabis da sauransu sun yi dirar mikiya a kan ra’ayin Malthus. Dabis ya ce a wannan nazari na Malthus ya yi kwan-gaba, kwan-baya. Ya zarge shi da cewa, me ya hana shi tsayawa wuri daya; da farko ya fara dora nazarin a mizanin kimiyya wurin gano irin matsalolin da za a iya fuskanta matukar a ka ci gaba da haihuwar barkatai, daga karshe kuma wurin samar da mafita sai ya shigo da matakan kiyayewa ta fuskar addini. A nan ana kalubalantar Malthus ne a kan me ya hana shi ya samar da mafitar matsalar a kimiyyance?

Akwai wasu mabambantan martanoni ga wannan ra’ayi na masani Malthus, kuma dukkan martanin sun sha bamban da wanda Karl Mard (1818 zuwa 1883) ya yi, tare da hadin gwiwar masani Friedrich Engels.

Karl Mard da Engels ba wai sun fitar da wani nazari na musamman bane dangane da yawaitar al’umma, a’a, sun dora ne a kan wanda Matlhus ya yi, ta hanyar caccakar alakanta talauci ga rashin hobbasan talakawa (sakaci) da masanin yayi. Haka kuma Mard sun ce atafau ba gaskiya ba ne a ce wai idan aka samu yawaitar al’umma za a samu barazanar talauci. Ra’ayinsu shi ne, idan a ka samu yawaitar al’umma ne ma za a samu habbakar masana’antu da kasuwanci don ci gaba mai amfani.

Ra’ayin Mard shi ne, misali a Nijeriya, ai kuskure ne mutum ya ce, mana wai yawan haihuwa ne ya janyo yawan talakawa da talaucin da a ke fama da shi. Saboda kasar Nijeriya na da arziki mai dimbin yawa; sai kuma ga shi Malthus ya tafi akan cewa; “Saboda karancin kasar noma, mutane ba za su iya samar da abinci me yawa wanda zai magance talauci ba, don haka a rage haihuwa kawai..”

A nan za mu iya cewa tabbas Nijeriya kadai ta isa ta nuna gazawar nazarin Malthus, saboda akwai wadatacciyar kasar noma, ga ruwan sama na sauka gunin ban sha’awa. Don haka ba mu da karancin kasar noma. Watakila Karl Mard, ya na da amsar da zai bayar. Bari mu ji…

“Shi talauci babu wani abu da ke janyo shi sai tsabar danniya, wariya da mugun halin ‘yan jari hujja. Azzalumin salon da ‘yan jari hujja ke bi wurin sarrafa masana’antu ne ya haifar da talauci da yawan talakawa. Don sune ke rike da iko, kuma da yawan mutane ba su da aiki, kalilan ke da aikin. Saboda ganin cewa akwai dubun dubatan mutane wadanda basu da aikin yi, sai su rika tauye hakkin ma’aikata, karancin albashi, wahalarwa, da sauransu. Duk wanda ya nuna damuwarshi dangane da albashi ko tsarin masana’antarsu, sai a kore shi a dauki sabon ma’aikaci.” In ji Karl Mard

Idan za a samar da masana’antu wadanda za a a ba ‘yan kasa ayyukan da suka dace, sannan a rika biyansu albashin da ya dace ba tare da cuta da cutarwa ba, da cikin kankanin lokaci za a ga yadda za a fatattaki talauci.

Don haka idan abin mu kwatanta ne, sai mu ce a kasar Chana akwai yawaitar al’umma, amma wannan yawan bai kawo mugun talauci, yunwa da fatara kamar yadda ake da shi a Kasar Nijar ba, wacce ba wani yawan al’umma suke dasu ba. Da wannan misalin ma Malthus da ra’ayinshi na yawan mutane ne ke haifar da talauci ya yi fawul.

Sai ka ga mutum don ya mallaki kudi, ya mallaki jari, ya na hura hanci ya na wulakanci; a wurin Karl Mard wannan girman kai da raina mutane, da yi wa mutane kallon banza don an dankara musu talauci da karfin tsiya shi ne babban matsala, ba wai haihuwa da yawan mutane ba.

Mafita a wurin Karl Mard ita ce a rusa wannan tsarin na girman kai, ji – ji da kai da ‘yan jari hujja su ka doru a kai. A sauke musu wannan girman kan da tinkaho ta hanyar yakar muguwar akidarsu, talakawa su hada kai, su gane ainihin matsalarsu, su rabu da kangin bauta.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Karl Max yawaitar al umma yawan mutane

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima

Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba ta da niyyar gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a 2027.

Galadima ya bayyana hakan ne ranar Talata a wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce gwamnatin da jam’iyyar APC ke jagoranta ta kankane cibiyoyin gwamnati don amfaninta.

Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo

“Wannan gwamnati ba ta shirya gudanar da zaɓen adalci ba. Daga yadda suke tafiyar da al’amura, za ka gane yadda suke tarwatsa jam’iyyun siyasa. Wannan yana nuna cewa ba sa son a samu hamayya a lokacin zaɓe,” in ji shi.

Galadima ya kuma yi gargadi kan shirin nada wani da ya kira mai lam’a a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), yana mai cewa hakan na iya jefa ƙasar cikin rudani.

“Ina fatan ba gaskiya ba ne, domin idan wannan mutumin ya zama shugaban INEC, ka tabbata cewa wannan gwamnati na neman tayar da yaƙin basasa,” in ji shi.

Sai dai bai ambaci sunan mutumin ba.

Dangane da batun fara yaƙin neman zaɓe da wuri da wasu jam’iyyu ke yi, Buba Galadima ya zargi INEC da gazawa wajen aiwatar da tanade-tanaden dokokin zaɓe.

“Wannan batun fara yaƙin neman zaɓe kafin INEC ta ba da izini, gwamnatin da ke kan mulki ce ta fara shi. Wannan yana nuna cewa INEC ba za ta iya zama mai adalci a irin wannan yanayin siyasa da muke ciki ba,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5 
  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
  • Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
  • Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025
  • Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi
  • Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
  • Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000
  • Sarki Sanusi II ya koka kan yawan cin bashin Najeriya