2025-07-04@21:26:35 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6367

«Karl Max»:

    “A wasu lokutan, ana cajin kudi masu yawa waje tallace-tallace. Wadannan abubuwan na cikin rashin bin doka a cikin dokar zabe ta 2022 wadda ke hana amfani da matsayi don musguna wa kowanne jam’iyya ko dan takara. “Hukumarmu za ta yi aiki tare da cibiyar hadakar jam’iyyu (IPAC), kuma za mu kara karfafa hadin gwiwarmu...
    Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ya amsa tambayoyin ‘yan jaridu, dangane da soke takunkumin tattalin arziki da cinikayya da kasar Amurka ta kakabawa kasar Sin. Kakakin ya ce, bayan tattaunawar tattalin arziki da cinikayya da aka yi tsakanin kasar Sin da kasar Amurka a birnin London na kasar Burtaniya, cikin ’yan kwanakin...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin wasu sabbin hadimai 19 da za su yi aiki a matsayin Manyan Mataimaka na Musamman domin ƙara inganta aikin gwamnati a jihar. Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a....
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a gun taron manema labarai da aka yi a yau Juma’a cewa, Sin na fatan kara hadin gwiwa da Ghana, don gaggauta bunkasuwar huldarsu ta abota bisa manyan tsare-tsare. Yayin da Mao Ning take tsokaci game da cika shekaru 65 da kulla huldar diplomasiyya tsakaninsu,...
    Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Sojojin kasarsa sun koya wa ‘yan sahayoniyya masu wuce gona da iri babban darasi Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, a jawabin da ya gabatar a taron kolin kungiyar Hadin Gwiwar Tattalin Arziki ta ECO da aka gudanar a kasar Azarbaijan a yau Juma’a, ya jaddada cewa: Sojojin kasar Iran...
    Shugaban kasar Iran ya gana da fira ministan kasar Pakistan Shugaban kasar Masoud Pezehkian ya gana da fira                             ministan Pakistan Shehbaz Sharif a gefen zaman taron kungiyar hadin kan tattalin arziki ta ECO da Jamhuriyar Azabaijan ta karbi bakunci. Fira ministan Pakistan Shehbaz Sharif ya yaba da irin rawar da shugaban kasar Iran ya taka...
    Hadin Gwiwa Da Hukumar IAEA Shugaban kasar Iran ya rattaba hannu kan dakatar da hadin gwiwa tsakanin Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, bisa wata doka da Majalisar Shawarar Musulunci ta kafa kwanan nan Sanannen abu ne cewa: Wannan doka ta zo ne bayan hare-haren da Amurka da yahudawan sahayoniyya suka...
    Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehra mya bayyana cewa: Hukuncin shari’a da ya hau kan Trumpm da Netanyahu shi ne kisa Limamin da ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran a yau ya bayyana cewa: Amurka da karen da suka horar sun yi barazana ga Jamhuriyar Musulunci ta...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun mayar da cibiyoyin bada agaji zuwa filin yakin kashe Falasdinawa a Zirin Gaza Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da mayar da cibiyoyin bayar da agajin jin kai zuwa wani mummunan tarko na aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa, wanda hare-haren baya-bayan nan da suka kai kan fararen hula sunka yi...
    Yakubu ya jaddada kokarin hukuma wajen yin adalci. “Za mu duba dukkan bukatun cikin adalci ba tare da la’akari da matsayin wadanda suka kawo su ba, lallai hukumar zabe ba za ta taba karya ka’idojinta ba.” Shugaban INEC ya musanta zarginsu cewa hukumar kokarin hada kai da wasu domin saba ka’ida wajen yin ragisara, ya...
    Wani mummunan lamari na kisan gilla ya afku a ƙauyen Galadanchi da ke Ƙaramar hukumar Dutse a Jihar Jigawa. Rundunar ’yan sandan jihar ta kama wani tsoho mai shekara 70 bisa zargin kashe ƙanwarsa saboda rikici kan filin gado. Gwamnan Bauchi ya ƙaddamar da kwamitin ƙirƙiro da sabbin masarautu An gano wasu bama-bamai 56 da...
    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce Sin ba ta goyon bayan wani bangare a rikicin Ukraine. Mao, wadda ta bayyana hakan yau Juma’a yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ta ce har kullum matsayar Sin ita ce karfafa gwiwar komawa ga tattaunawar wanzar da zaman lafiya....
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kwanan baya, wasu kamfanonin samar da kayan shayi masu tamburan kasar Sin sun jawo hankalin sassan kasa da kasa, sakamakon yadda suka fara sayar da hannayen jarinsu a kasuwar hannayen jari ta kasa da kasa. Baya ga haka, wasu kayayyaki masu tamburan kasar Sin na kara samun karbuwa a kasuwannin duniya. Har ma wasu kafofin...
    Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya ƙaddamar da wani babban kwamitin ƙirƙiro masarautu da gundumomin hakimai a jihar. An ƙaddamar da kwamitin ne a wani mataki na magance buƙatu da dama daga al’ummomi daban-daban da kuma inganta al’adu da tsarin mulki na asali a faɗin Jihar Bauchi. Abba ya naɗa Ahmed Musa a matsayin...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauya shugabancin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars. Ya naɗa tsohon kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa, a matsayin sabon Babban Manajan ƙungiyar. An gano wasu bama-bamai 56 da ISWAP suka binne a Borno “ADC za ta fuskanci matsala wajen zaɓen wanda zai yi mata takarar shugaban ƙasa”...
    Gwamna Abba ya bayyana gamsuwarsa da ƙwarewar sabbin jami’an da aka naɗa, inda ya bayyana cewa za su taka rawar gani wajen aiwatar da manufofin gwamnatinsa. Ya ce jajircewa da ƙwarewarsu na daga cikin dalilan da suka sa aka zaɓe su domin su taimaka wajen ci gaban Jihar Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare....
    A yayin bincike, ’yansanda sun ƙwato motocci huɗu, wuƙa, kayan sojoji, da harsasai. Game da fashi da makami, rahoton ya nuna cewa an samu rahotannin guda biyar daga watan Mayu zuwa Yuni, kuma an kama mutane 17 da ake zargi da aikata laifin fashin. Kwamishinan ya kuma ce an samu rahotannin safarar yara guda huɗu,...
    Dakarun rundunar sojin  ‘Operation Haɗin Kai’ sun ce dakarunsu sun kai ga nasarar gano wasu bama-bamai guda 56 da ake zargin mayaƙan ISWAP ne suka binne a kan gadar Marte zuwa Dikwa da ke Jihar Borno. Sojojin sun kuma daƙile wani harin da ka iya zama wani babban harin da zai haifar da mummunan ɓarnar...
    A ɗaya ɓangaren kuma Fita zuwa wani yanki daban da ba naka a halin yanzu, yana da nasa fa’idar. Domin kuwa, na ziyarci wasu jihohi uku kwanan nan; waxanda labarai a kansu babu daxin ji. Jihohin su ne, Delta, Inugu da kuma Zamfara, waxanda galibi labaransu marasa daxi ne ta fuskar siyasa, ta’addanci da sauran...
    Bayan Plato sai kuma masani Aristotle shi ma ya zo da ta shi fahimtar, a shekara 340 kafin zuwan Annabi Isah (AS). A tunani irin Aristotle, yawaitar al’umma ba ta da wani alfanu, don haka hakki ne da ya rataya kan gwamnati ta kayyade yawan iyalin da mutum zai iya haifa. Idan matar mutum ta...
    Ya yi nuni da cewa, jami’o’i na cikin tsaka mai wuya wajen samun sauye-sauye a duniya cikin sauri da kuma bukatu na cikin gida, wanda ke bukatar lallai sai sun sake yin nazari sosai kan tsarinsu, da dabi’unsu, domin samar da ingantaccen muradun al’ummarmu da nahiyarmu. Ya kuma jaddada mahimmancin hangen nesa inda jami’o’i za...
    Hukumar ta NSEMA ta jagoranci gudanar da aikin, tare da tattara kayan aiki gami da tura kungiyoyin bayar da agajin gaggawa tare da hadin gwiwar hukumomin kananan hukumomi.’ Arah, ya bayyana cewa, kafin lokacin damina, hukumar ta NSEMA ta kaddamar da shirin wayar da kan jama’a game da ambaliyar ruwa a duk shekara a matsayin...
    A ɓangare guda kuma, kotu ta samu Natasha Akpoti-Uduaghan da laifin saɓawa umarnin kotu ta hanyar rubutun zaulaya da ta yi a shafinta na Facebook a ranar 7 ga watan Aprilu, inda take bayar da haƙuri amma ta hanyar zaulaya ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Alpabio. Kotun ta ce rubutun cin fuska ne ga umarninta,...
    Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta umarci Majalisar Dattawa da ta mayar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya. A watan Maris, Majalisar Dattawa ta dakatar da Natasha na tsawon watanni shida, bayan wata taƙaddama da ta ɓarke tsakaninta da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio. Kotu ta ci tarar Natasha N5m saboda...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Kula da Ingancin Kayayyaki ta Najeriya (SON) ta gudanar da bikin bayar da takardun shaidar MANCAP ga kayayyaki 31 da suka cika sharuddan inganci a ofishinta da ke Kaduna. Taron wata babbar nasara ce ga masana’antun da abin ya shafa, duba da yadda ya kara jaddada muhimmancin tabbatar da inganci a masana’antun cikin...
    Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja a ranar Juma’a ta sami dakatacciyar Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natsha Akpoti-Uduaghan da laifin raina kotu, sanna ta ci ta tarar naira miliyan biyar. Da take yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Binta Nyako, ta ce Natasha ta wallafa wata wasikar zambo ta ban hakuri ga Shugaban...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump Ya Bayyana cewa nan da kwana guda ko sa’o’ii 24 masu zuwa ne zai sani, ko kungiyar Hamas ta amince da ‘shawararsa ta tsagaita wuta da HKI kuma ta karshe a gaza. Shafin yanar gizo ta labarai ‘Arabnews ta kasar Saudia’ ta nakalto Trump yana fadar haka a yau jumma’a....
    Bayan an rufe sararin samaniyar kasar Iran saboda yaki na kwanaki 12 wanda HKI ta dorawa kasar a ranar 13 ga watan yunin da ya gabata, a yau Jumma’a a bude zirga-zirgan jiragen saman a duk fadin kasar daga karfe 5 na safe zuwa 6 na yamma daga ranar Jumma’a 4 ga watan July 4,...
    Gwamnatin kasar Amurka ta dorawa JMI sabbin takunkuman tattalin arziki ta bangaren man fetur a jiya Alhamis, a dai-dai lokacinda take maganar sake farfado tattaunawa da ita. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto  Scott Bessent sakataren kudi na Amurka yana fadar haka ‘Amurka zata ci gaba da gurgunta tattalin arzikin JMI da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi watsi da labarin da ministan harkokin wajen kasar Jamus ya watsa dangane da shirin Nukliyar kasarsa ya kuma kara da cewa labarin jabu ne. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a shafinsa na X . Ya kuma yi watsi...
    Ministan Babban Birninn Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya musanta labarin cewa ya yanka wa ’ya’yansa manyan filaye a Abuja, inda ya ce in ma haka ne suna da hakki a matsayinsu na ’yan Najeriya. Ana dai zargin Wike da ba biyu daga cikin ’ya’yansa fili mai fadin murabba’in hekta 2,082, dayan kuma mai fadin hekta...
    Kusoshin gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari sun shiga haɗakar jam’iyyun adawa ta ADC da nufin kayar da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta APC. Tsofaffin mukarraban gwamnatin Buhari da suka koma haɗakar ADC sun haɗa da tsofaffin ministoci da tsofaffin gwamnoni da masu muƙaman siyasa. Yawanci sun raba gari da APC ne saboda zargin an...
    Yan Najeriya da dama na ta bayyana mabanbantan ra’ayoyi kan sabon hadakar ‘yan siyasa zuwa sabuwar jami’yyar ADC.   A yayin da wasu ke ganin wannan hadaka za ta cire musu kitse daga wuta, wasu kuwa gani suke yi duk kanwar ja ce. A ranar laraban nan ne dai gaggan ‘yan siyasa daga jamiyyu daban...
    Kazalika, gazawar Hukumar Bayar Da Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA da kuma sauran hukumomin na jihohi na sauke nauyinsu, hakan ya nuna a zahiri, na irin kalubalen da ake fuskanta, na rashin sauke nauyinsu, na bayar da agajin na gaggawa. Misalii, an ruwaito cewa, a sansanin na ‘yan gudun hijira na Yelwata, musamman yadda suke...
    Taron nay au dai an ba shi taken; Girmama Kwamandan Farmakin ” Wa’adussadiq” za kuma a yi shi ne da marecen yau a birnin Tehran a Husainiyyar ” Fatimatuzzahra ( a.s) dake karkashin rundunar soja ta ” Arrasulul-Muhammad ( a.s). Shi dai Birgediya Shahid Hussain Salami ya yi shahada ne a wani harin ta’addanci da...
    Daga safiyar yau juma’a, Falasdinawa 17 sun yi shahada sanadiyyar hare-haren da HKI ta kai wa Falasdinawa ‘yan hijira a yankin Mawasi dake Kudancin Khan-Yunus. Tun da safiyar yau ne dai jiragen yakin HKI su ka kai hare-hare a gabashin birnin Gaza, haka nan kuma ‘yan sahayoniyar sun yi amfani da jirgin sama maras matuki...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya bayyana cewa, kungiyar na ci gaba da nazartar na rabar da man kai tsare, na shirin na matatar man ta Dangote, wanda daga baya, kungiyar za ta shiga cikin shirin gadan-gadan. Clement, ya sanar da cewa, kafin kungiyar ta shiga cikin shirin kai tsaye, yana da kyau a fara tattaunawa da Dangoten da kuma...
    Janar Ali Fadi wanda tashar talabijin din Iran ta yi hira da shi a jiya da dare, ya bayyana cewa; Iran tana da damar kera makamin Nukiliya da kuma rufe mashigar ruwan Hurzum. Janar Fadli ya ce; Dakarun na kare juyin musulunci sun lakanci yadda ake kera shi, tare da bayyana fatan cewa kar  makiya...
    Shugaban hukumar tsaron ta fararen hula janar Jalali ya bayyana cewa; saboda aiki da ka’idojin tsaro sun yi nasarar hana fitowar sanadarorin Nukiliya da za su iya cuta da mutane.  Kamfanin dillancin labaru na “Mehr” ya nakalto janar Jalali yana cewa; Amurka ta kai hare-hare akan muhimman cibiyoyinmu da suke dauka cewa yana da girma...
    Dantsoho wanda ya samu wakilicin Babban Manajan a Hukumar ta NPA Femi Oyewole, ya bayyana cewa, Shugaban Hukumar ta NPA, Hukumar ta mayar da hankali wajen ganin cewa, ana kare kimar Tekunan kasar. “Hadurran zuba baraguzan kusan a kurkusa suke, wanda kuma, suke ci gaba da karuwa, wanda hakan ya nuna cewa, akwai matukar bukatar...
    Kwamatin Harkokin Kananan Hukumomi na Majalisar Dokokin jihar Jigawa ya fara rangadin kwanaki biyu a karamar hukumar Roni a ci gaba da rangadin kananan hukumomin jihar 27 da kwamatin ya kaddamar. A jawabin sa a sakatariyar karamar hukumar Roni, Shugaban kwamatin Alhaji Aminu Zakari, ya ce tsarin mulkin kasa ya bai wa majalisa ikon dubawa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rasha ta zama ƙasa ta farko da a hukumance ta amince da gwamnatin ƙungiyar Taliban da ke mulkin ƙasar Afghanistan. Wannan na zuwa ne bayan Rashar ta karɓi takardun shaidar kama aiki na sabon jakadan Afghanistan, wanda hakan ya sa ta zama ƙasa ta farko da ta amince da gwamnatin Taliban a ƙasar. Ambaliya da...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Bayar da agajin gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA) ta bayyana cewa, ambaliya da iska mai ƙarfi sun rushe da lalata gidaje 171 a yankunan jihar cikin watanni biyu da suka gabata, lamarin da ya haddasa asara da kuma mutuwar yara huɗu. Sakataren zartarwa na Hukumar SEMA, Malam Abdullahi Haruna Abdullahi ne ya bayyana hakan...
    Majalisar riƙon ƙwarya ta Gwamnatin Mali ta bai wa Shugaban Mulkin Sojin ƙasar, Janar Assimi Goita, wa’adin mulki na shekara biyar, wanda za a iya sabunta shi fiye da sau daya ba tare da zaɓe ba. A bara ne Janar Goita ya yi alƙawarin maido da mulkin dimokuradiyya a ƙasar, sai dai hakan ba ta...