Nijar ta kori wasu kamfanonin China 3 daga ƙasar
Published: 15th, March 2025 GMT
Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta kori manyan jami’an wasu kamfanonin CNPC da WAPCO da SORAZ na China daga ƙasar.
Haka nan, gwamnatin ta kuma soke lasisin wani babban Otel na China da ke birnin Yamai.
Faɗuwar farashin kayan abinci a watan azumi ta shammace mu – ‘Yan kasuwa ’Yan bindiga na neman N30m domin fansar gwarzon gasar Al-Qur’ani a KatsinaGwamnatin Nijar ɗin na zargin kamfanonin da ƙin mutunta dokokin aiki a ƙasar da ma na yarjejeniyar aiki da suka sanya wa hannu.
Wasu majiyoyi na kusa da gwamnatin sun tabbatar da cewa tun a ranar Larabar da ta gabata Shugaba Janar Abdourahmane Tchiani ya bayar da wa’adin sa’o’i 48 ga manyan daraktacin kamfanonin CNPC mai aikin haƙar man fetur a Nijar da na kamfanin WAPCO da ke kula da jigilar ɗanyen man Nijar ta bututu zuwa tashar ruwan Cotonou da kuma na babbar matatar mai ta SORAZ su bar ƙasar baki ɗaya.
Majiyoyi na cewa hukumomin ƙasar ta Nijar na zargin kamfanonin na Chinar da aikata laifuka daban-daban da suka haɗa da ƙin mutunta yarjejniyar horas da ma’aikata ‘yan Nijar.
Haka kuma, hukumomin na zargin ci da gumin ma’aikatan Nijar ta hanyar ba su albashin da bai taka kara ya karya ba a gaban takwarorinsu na Chinar da ma shirya makarkashiyar da ta haddasa matsalar karancin man fetur a baya bayan nan a kasar.
Yanzu haka dai ko baya ga korar waɗannan manyan daraktoci na ƙasar China, gwamnatin mulkin sojan Nijar ta kuma sanar da ƙwace lasisin aiki na babban Hotel na SOLUXE mallakar China da ke birnin Yamai.
A ɓangaren ɗaya kuma Gwamnatin Nijar ɗin ta ba da izinin rufe asusun ajiyar kuɗi na babbar matatar mai ta kasa ta SORAZ.
Kawo yanzu dai kasar ta China ba ce uffan ba, haka kuma mahukuntan kamfanonin da abin ya shafa da aka tuntuɓa ba su magantu a kan lamarin ba.
A shekarar da gabata ce Nijar ta ƙulla yarjejeniyar cefanar da ɗanyen man fetur ta dala miliyan 400 da ake haƙowa a ƙasar.
A yayin da wasu ‘yan Nijar ke yaba wa da matakin wasu na ganinsa a matsayin barazana ga makomar hulɗar ƙasar da China da ma tattalin arzikin Nijar ɗin baki ɗaya.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Katsina ta amince da ƙidayar almajirai, makarantun Islamiyya
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda ya bai wa Hukumar ƙididdiga ta jihar damar gudanar da ƙidayar almajirai da makarantun Islamiyya a jihar.
Babban jami’in ƙididdiga na jihar, Farfesa Saifullahi Sani wanda ya bayyana hakan a Katsina ranar Alhamis, ya ce maƙasudin gudanar da ƙidayar shi ne tsara dabarun inganta tsarin.
’Yan sanda sun kashe ’yan fashi da ƙwato makamai a Kaduna An tallafawa iyalan ’yan sanda da Naira miliyan N13.4m a BornoBabban jami’in ƙididdigar ya bayyana hakan ne yayin wani muhimmin taro na yini ɗaya da masu ruwa da tsaki a jihar.
Sani ya ce, “Manufofin ƙidayar sun haɗa da samar da cikakkun bayanai na dukkan Makarantun Alkur’ani da kuma samar da cikakken tsarin yaran da ba su zuwa makaranta a jihar.
“Manufofin hakan su ne, a tabbatar da halin da ɗaliban suke ciki, don sanin halin da suke ciki, da samun cikakkun bayanai na malaman makarantun.
“Haƙiƙa wannan an yi shi ne don samun cikakkun bayanai na ɗalibai a fannin.
“Haka kuma don tabbatar da adadin ɗaliban da suka tsunduma cikin harkar bara a jihar da kuma taimakawa wajen fahimtar hanyoyin aiwatarwa a halin yanzu, gano giɓi da jagoranci wajen samar da matakan da suka dace.”
Ya bayyana cewa, sakamakon ƙidayar zai sanar da shiga tsakani da kuma fara ƙoƙarin da suka dace na sauya tsarin karatun Alkur’ani a halin yanzu.