Faɗuwar farashin kayan abinci a watan azumi ta shammace mu – ‘Yan kasuwa
Published: 15th, March 2025 GMT
’Yan kasuwa na ci gaba da neman mafita bayan karyewar farashin kayan masarufi, musamman abinci da ake ci gaba da samu, sabanin yadda aka saba fuskantar tashin gwauron zabon farashi a lokacin azumi a Nijeriya.
Farashin kayan abincin ya karye ne a lokacin da wasu ’yan kasuwar suka riga suka saye amfanin gona suka boye tun a lokacin kaka, da nufin rubanya kudinsu idan farashinsa ya yi tashin gwauron zabo daga musamman a lokaci irin wannan na azumin watan Ramadan, da wasu bayin Allah suke saya don raba wa mabukata.
Kudin hatsi irin su shinkafa da wake da masara da dawa da gero da fulawa da kuma cimaka ’yan kamfani da ake sarrafawa daga fulawa kamar taliya da garin samanbita, duk sun yi kasa.
Wasu majiyoyi sun danganta faduwar farashin da janye haraji kan wasu nau’ukan abincin da ake shigo da su daga kasashen waje da Gwamnatin Tarayya ta yi.
An samu kai a wannan yanayi ne a lokacin da manoma suka riga suka sayar da kusan daukacin amfanin gonar da suka noma da damina ga ’yan kasuwa.
Akwai yiwuwar karin sauki — Dan kasuwaA zantawarsa da Aminiya kan yadda faduwar farashin ta shammace su, wani mai sayar da kayan abinci a Babbar Kasuwar Garin Kubwa da ke Abuja, Alhaji Almustafa Imam, ya ce al’amarin ya dagula masu lissafi, da za su jima ba su warware ba.
Amma ya ce gara hakan, idan aka kwatanta da yadda suka rika fuskantar hauhawar farashi akai-akai sama da shekara guda da ta gabata, a duk lokacin da suka koma kasuwa don saro kaya.
“A lokacin dole sai mun yi cikon kudi don iya sayen adadin abin da muke saya,” in ji shi.
Ya ce saukar farashin kayan abincin na yanzu ya sa abokan huldarsu na sayan karin kaya a wajensu, sabanin yadda a baya suke rage adadin da suka yi niyyar saya saboda tashin farashi.
Dan kasuwan ya ce akwai yiwuwar samu karin sauki idan rage farashin mai da Matatar Dangote ta sanar ya yi tasiri a harkar sufuri, ta yadda za a samu sauki kudin jigilar amfanin gona daga kauyuka zuwa kasuwanni, kuma zai taimaka wa wajen rage kudin da manoman rani ke kashewa kan man fetur a injunansu na ban-ruwa.
Shinkafar waje ta fi ta gida saukiDa ya ke bayani kan farashin kayan abincin, Alhaji Almustafa Imam ya ce, lamarin har ya kai ga shinkafa da kamfanonin gida ke sarrafawa tana neman fin wadda ake sayowa daga kasar waje saukin farashi.
“Idan zan yi misali da shinkafa da ake kawowa daga kasar Indiya, akwai wadda ake sayarwa a kan Naira dubu 87, a yayin da ta kamfanin gida kwatankwacinta mai nayin kilo 50 mai suna Big Bull ke kai naira dubu 89.” in ji dan kasuwan.
“A bangaren gero kuwa, na sayi buhu mai nauyi kilo 100 a kan naira dubu 72 a lokacin kaka, sai ga shi a yanzu ya karye ya koma naira dubu 62. Wake mafi daraja da ake kira ‘iron beans’ kuwa, na sayi buhu a kan naira dubu 130 a lokacin kaka, amma yanzu ya koma naira dubu dari da goma.
“Wake da ke biye da ‘iron beans’ a daraja a kan naira dubu 95 aka sayar da shi a lokacin kaka, sai ga shi a yanzu ana samun sa a kan naira dubu 80 a wuraren da ake zuwa sari kamar garin Kontagora, da ke jihar Neja, in ji dan kasuwan, wanda ya ce akwai nau’ukan wake da ba su kai wadannan daraja ba da ake samu a kan naira dubu 70.
Ya ce yakan sayi kayan ne a lokacin kaka ya ajiye don gudun bacin rana, amma sai ga shi wannan karon farashin ya karye.
Dan kasuwar ya bukaci gwamnati da ta wadata manoma da kayan aiki a damina mai zuwa don rage farashin abin da ake nomawa a cikin gida, maimakon dogaro da na waje, wanda ya ce ba shi da tabbas.
Kayan kamfani ma sun yi saukiAlhaji Muhammadu Dan Saleh da ke gudanar a kasuwanci a Babbar Kasuwar IBB da ke garin Suleja a Jihar Neja ya ce an samu saukin farashin kayan masarufi na kamfani kamar garin samambita da semolina da taliya da makaroni da sauransu.
Ya bayyana cewa kafin watan azumi suna sayar da kwalin taliya Mai Kwabo a kan naira dubu 17, amma yanzu ya karye ya koma kimanin naira dubu 15.
Taliyar Glden Penny kuma, a baya suna sayar da ita a kan naira dubu 21, amma a yanzu ta koma dubu 20.
Buhun sukari na Dangote mai nauyi kilo 50 da a baya ake sayarwa naira dubu 82, a ya koma naira dubu 79 duk da kamawar watan azumi.
Ya ce, wasu kayan na kara farashi ne a lokacin da aka fuskanci yankewarsu a kasuwa, inda ya bayar da misali da cewa “kwalin madarar ruwa ta Peak da a baya an yi lokacin da ta kai naira dubu 45, yanzu tana samuwa a kan naira dubu 43 duk da karuwar bukatarta da ake yi a lokaci irin wannan na watan azumi.”
Ga koshi ga kwanan yunwaWasu da Aminiya ta zanta da su sun yaba da saukin farashin kayan abincin da aka samu, sai dai sun yi korafin cewa idan ba a yi dace ba, ’yan kasuwan ne za su sake saye kayan, a nema a rasa a kasuwa.
Wani ma’aikacin gwamnati a yankin Babban Birnin Tarayya, Abuja, Malam Abdullahi Alamuna, ya ce ma’aikata da dama da ya kamata su ci gajiyar saukar farashin, ba a biya su albashinsu na watan Fabrairun da ya gabata ba, sai bayan kamawar sabon wata da kwana hudu.
Hakan, in ji shi, ya sa yawancinsu “ba su iya yin cefanen kayan abinci azumi ba a farkon watan, sannan kasuwanni ba su samu hadahada bayan karban albashi ba, sun kasance cikin karancin ciniki, duk kuwa da saukin kayan abincin da ka samu.”
Shi ma wani mazaunin Abuja, Malam Isa Adamu Rimin Kebe, ya ce “’yan kasuwa da dama a kasuwannin birni na kin sauke farashin kayan abinci duk da saukin da aka samu, inda suke la’akari da farashin tsohon kaya da suka sayo.”
Ya ci gaba da ceaw, “hakan ta sa jama’a da dama da ke neman cin gajiyar saukin da aka samu zuwa kasuwannin kauyuka don samun rangwamen da ya dace.
Hakan ya saba da lokacin da ake samun tashin farashin kayan abinci a kai-akai a baya, inda a wani lokaci waya kadai ’yan kasuwan ke yi da inda suke saro kaya, sai nan take su kara farashi.
Azumin bana sai godiya — MagidantaWani magidanci a garin Kaduna, Malam Umar Ramalan Direba, ya ce, “Gaskiya babu abin cewa sai godiya ga Allah, saboda azumin bana dai kam sai godiya ga Allah.
“Ko ba ka da kudin saye za ka ji dadin cewa abinci ya sauka. A bara gero mun saya dubu 1,400 mudu zuwa 1,500 amma sai ga shi a bana kasa da dubu daya.
“’Yan kasuwa sun wasa wukarsu domin sayar wa jama’a kaya da tsada, amma sai ga shi Allah Ya kamasu, abubuwa suka yi sauki.
“Shi ya sa duk wani magidanci ya samu natsuwa ko da kuwa ba shi da kudin saya domin a bara babu kudi kuma kaya da tsada, ina amfani,” in ji shi.
Abdulmomin Babangida Shehu wani magidanci mai aikin gadi a Kaduna ya ce a yanzu an samu karin masu bayar da taimakon kayan abinci saboda abubuwa sun yi sauki.
“Duk da cewa ba muna son a bamu ba ne kyauta, amma idan abinci ya yi sauki kowa zai samu na ci da budabaki. Shi ya sa muke cikin jin dadi a bana. Domin akwai bayin Allah masu taimako don Allah, ke nan a bana za su samu damar kara taimakawa marasa galihu,” in ji shi.
Shi ma Rimi, wani mai sayar da man fetur a Mogadishi Kaduna cewa ya yi hakika magidanta “Muna cikin farin ciki a bana saboda saukin farashin kayan abinci da aka samu.
“Domin ba a taba samun saukin kayan abinci a lokacin Ramadan ba sai a bana. Sai dai akwai rashin kudi a hannun mutane amma duk da haka muna jin dadin, saukin da aka samu musamman a kasuwanni. Masu shaguna ne kurum suka ki yin sauki,” in ji shi.
Rimi ya kara da cewa a yanzu masu cirani sun fi son su hada kudi su sayi kayan abinci su girka da kansu a kakunansu a maimakon su saya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: kasuwa Ramadan farashin kayan abincin farashin kayan abinci a kan naira dubu kayan abinci a saukin farashi watan azumi
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda Badakalar Tallafin Man Fetur Ta Zame Wa Nijeriya Alakakai
A cewar Bawa, gwamnatocin da a karkashinsu aka wawashe dukiyar kasa, su ne na Mulkin Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo (daga 1999 zuwa 2006), sai Marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua (daga 2007 zuwa 2009), kazalika a mulkin Shugaba Goodluck Jonathan daga (2010 zuwa 2014), sai kuma mulkin Muhammadu Buhari (daga 2015 zuwa 2023).
Wadannan bayanai na kunshe cikin littafin, ‘The Shadow Of Loot and Loss – Uncobering Nigeria’s Petrol Subsidy Fraud,’ wanda tsohon sarkin yaki da cin hanci da rashawa ya rubuta.
Alkaluman da Bawa ya bayyana daga cikin gwamnatocin hudu, shugaba Buhari ne ke kan gaba wajen biyan tallafin da ake ta cece-kuce akai na Naira tiriliyan 11, sai kuma na Jonathan wanda ya kashe Naira tiriliyan 3.9. Gwamnatin Obasanjo ta zo na uku da Naira biliyan 812 yayin da ‘Yar’aduwa ke biye da Naira biliyan 794.
Obasanjo da Buhari sun shafe shekaru takwas suna mulki yayin da Jonathan ya yi mulki na tsawon shekaru shida, tun da farko ya kammala shekaru biyu da gwamnatin Yar’adua ta bari, a matsayin mataimakin marigayin, inda ya lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2011.
A cikin littafin mai shafuka 317, Bawa ya ce kudaden tallafin, wadanda galibi na yaudara ne, ana samun su ne ta hanyar rashin isassun tsare-tsare, raunin tsarin aiwatar da doka, da kuma rashin gaskiya a cikin dukkan tsarin.
Bawa ya ce wadannan kura-kurai sun karfafa karuwar kudaden tallafin daga Naira biliyan 123 a shekarar 2006 zuwa Naira biliyan 886 a shekarar 2014 da kuma mummunan adadi na Naira tiriliyan 11 a shekarar 2023.
Tsohon shugaban na EFCC ya ci gaba da cewa za’a iya bayyana badakalar tallafin man fetur ta Nijeriya ta hanyar amfani da triangle na zamba na “Tsarin (Needs), Opportunity and Rationalisation.”
Ya ce, “Matsi shi ne abin da zai sa mutum ya yi zamba, samun dama kuma ita ce ke bayar da yanayin da mutum zai aikata zambar.
Yadda Aka Aiwatar Da Badakalar
Bawa ya gano hauhawar farashin shigo da kayayyaki, da sauya lokacin daftarin kaya, rashin bayyana dawo da kayan da aka shigo da su ta sama da kasa, da jirgin ruwa mai yawo, shigo da kaya guda daya, tare da biyan tallafi a kansa sau biyu, na daga cikin hanyoyin da aka tafka badakalar tallafin man fetur.
A cewarsa, kamfanonin sayar da man sun yi amfani da yawan shigo da kayayyaki don kara yawan kudaden tallafi daga karshen shekarun 2010.
Ya ce binciken da aka gudanar ya sa hukumar EFCC ta gano haramtattun kudaden da suka haura Naira biliyan 30.
Bawa ya ci gaba da cewa, “A lokuta da dama, an samu jami’an gwamnati da saninsu ko kuma ba da saninsu ba, ta hanyar buga tambari da sanya hannu a cikin takardun jabun, wasu jami’an sun ce sun sanya hannu a kan takardun a lokacin da suke bakin aiki, duk da cewa suna sane da cewa lamarin ba haka yake ba, akwai wadanda suka sanya hannu kan takardun bogi, ba tare da sanin cewa an kirkiresu ba ne.
Ya ba da misali da yadda wani kamfani ya shigo da lita miliyan biyar kasa da mai fiye da lita miliyan 12. An biya kamfanin tallafin Naira miliyan 700, wanda bai cancanta ba.”
Wannan a cewarsa lamari ya ci gaba da haifar da tambayoyi masu mahimmanci game da hanyoyin damfara, gazawar sa ido na hukumomi, da kuma yadda EFCC ta gano wadannan haramtattun ayyuka.
Hanyar Kawo Karshen Lamarin
Dangane da kokarin hukumar na duba matsalar, Bawa ya ba da tarihin bincike, kamawa, tuhume-tuhume, yanke hukunci da kwato haramtattun dukiyoyi da hukumar ta yi.
Ya ce duk da cewa ba a samu wasu laifuka ba a shekarar 2006 da 2007, hukumar ta kwato Naira biliyan 11.5 a shekarar 2008, Naira biliyan 4.88 a shekarar 2009, da kuma Naira biliyan 10.3 a shekarar 2010.
Tsohon shugaban hukumar ta EFCC ya bayyana wata badakala da aka yi a 2011 ta tallafin man fetur, “a lokacin ne muka gano wasu haramtattum ayyukan da suka kai Naira biliyan 41.7.
“A dunkule, ayyukan damfara sun kai kusan Naira biliyan 68, wanda kusan kashi 80 cikin 100 an kwato su,” in ji shi.
Bawa ya kara da cewa, a cikin shekaru 25 na mulkin dimokuradiyya, Nijeriya ta kashe Naira tiriliyan 16.5 wajen bayar da tallafi, inda ya kara da cewa abin da ke daure kai ga daukacin al’amura shi ne yadda aka kashe kaso daga cikin kudaden wajen yin ikirarin karya da satar dukiyar kasa.
Hanyar Samun Ci Gaba
Bawa ya yi nuni da cewa, shi tallafin a kansa ba wani sharri ba ne; amma duk da haka, aiwatar da aikinta na yaudara ya sa gwamnati ta ki amincewa da dimbin albarkatun da aka tanada domin samar da ababen more rayuwa, inganta harkokin ilimi da kiwon lafiya, wadanda ke amfanar da marasa galihu a Nijeriya.
Don haka ya yi kira da a samar da ingantaccen tsarin bayar da tallafi.
Ya ce, “Kiyaye tsarin tallafin da aka sarrafa da kyau zai iya ba da agajin da ake bukata ga masu rauni ta hanyar tabbatar da cewa an dakatar da tsadar rayuwa, sannan gwamnatin ta tsaya tsayin daka wajen samar da wani abin dogaro ga matsalolin tattalin arziki.
“Wannan yana jaddada muhimmancin samar da ingantattun hanyoyin sa ido da daidaita yadda ake raba tallafin don hana cin zarafi da tabbatar da sun cika manufarsu.”
Bawa ya kuma yi kira da a ji tsoron Allah da gaske da kuma samar da ingantaccen tsarin adalci.
Bawa ya ce, “Tsarin ba wai kawai kayan ya ke ba wa kariya da kuma dakile laifuka ba, har ma ya mallakar karfin bincike da kuma hukunta laifukan da suka dace, yana da matukar muhimmanci, irin wannan tsarin na samar da amana da amincewa a tsakanin ‘yan kasa, tare da karfafa hadin gwiwar jama’a da kuma tabbatar da doka da oda.”
Tsohon shugaban na EFCC ya bukaci ‘yan Nijeriya da na kasashen waje da su canja halayensu, su bi ka’idojin da’a, su sanya al’ummar kasa a zuciyarsu sama da kansu.
Bugu da kari, ya yi kira da a samar da isassun kudade tare da tura fasahar kere-kere a cibiyoyin gwamnati domin dakile cin hanci da rashawa.
“Su koma al’adar yin abin da ya dace, ba tare da la’akari da yanayin ba, hakan na iya haifar da sauye-sauye masu dorewa a cikin al’amuran al’umma,” in ji shi.
LEADERSHIP Sunday ta ruwaito cewa an samu wasu ‘yan Nijeriya da dama da laifin zamba a cikin tallafin man fetur, na baya-bayan nan shi ne Mamman Ali, dan Ahmadu Ali, tsohon shugaban jam’iyyar PDP mai mulki a lokacin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp