Gwamnati Za Ta Goyi Bayan Shirin Fim Kan Tarihin Shekaru 25 Na Dimokuraɗiyyar Nijeriya
Published: 15th, March 2025 GMT
Ya ce fim ɗin tarihin zai nuna nasarori, ƙalubale, da darussan da aka koya a wannan tafiya.
Ya ce: “Na yi farin cikin ganin ƙoƙarin da IPAC da shugabannin ta suke yi wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya, musamman ta hanyar fim ɗin wanda zai zama wata muhimmiyar shaida ta tarihi, domin girmama jaruman siyasar ƙasar mu da kuma nuna jajircewar Nijeriya a harkar dimokiraɗiyya.
Ya jinjina wa IPAC kan jajircewar ta wajen cigaban dimokiraɗiyya tare da jaddada muhimmancin haɗin kan jam’iyyun siyasa bayan zaɓe domin ƙarfafa haɗin kan ƙasa da cigaba.
“Gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tana goyon bayan a yi gasa mai kyau a siyasa, domin dimokiraɗiyya tana bunƙasa ne idan ana samun hamayya mai ma’ana da haɗin kai bisa muradin ƙasa ba tare da la’akari da bambancin jam’iyyun siyasa ba,” inji Idris.
Ya ƙara da cewa ɗorewar tsarin dimokiraɗiyya tana buƙatar haɗin gwiwa daga kowane ɓangare.
Ya ce: “Jam’iyyun siyasa su ne ginshiƙin dimokiraɗiyya; kuma yayin da hamayya take da muhimmanci a lokacin zaɓe, dole ne mu haɗa kai bayan haka don gina ƙasar mu.
“Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda babban ɗan dimokiraɗiyya ne, yana mutunta gasa mai tsafta, amma yana kuma fifita haɗin kai da cigaban ƙasa.”
Shugaban IPAC na ƙasa, Honourable Yusuf Ɗantalle, ya ce shirin fim ɗin tarihin zai bayyana cigaban da aka samu a fannonin gina ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, da haɗin kan al’umma.
Ɗantalle ya ce: “Fim ɗin, a matsayin wani muhimmin tarihin ƙasa, zai mayar da hankali kan matasa, musamman ‘yan zamani (Gen Z), domin ya zama wata hanyar ilmantarwa da haɗe kan ‘yan ƙasa kan tafiyar dimokiraɗiyyar Nijeriya. Fim ɗin zai ƙunshi fitattun jaruman Nollywood kuma za a shirya shi da na’urori na zamani domin ya dace da matakin inganci na duniya.”
Daga cikin shugabannin IPAC da suka halarci taron akwai Mataimakin Ciyaman ɗin IPAC na Ƙasa Dipo Olayokun, da memba a majalisar, Cif Dan Nwayanwu, da Sakatare na Ƙasa, Maxwell Mabudem.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Rikicin Iyakar Thailand da Cambodia Ya Tilasta wa Dubban Mutane Barin Muhallansu
Jami’ai sun ce mutane sama da dubu 500 ne kawo yanzu aka tursasawa barin muhallansu a Thailand da kuma Cambodia a yayin da rikicin kan iyaka tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara ƙamari.
Rundunar sojin Thailand ta ce Cambodia ta harba mata dubban makaman roka tun bayan da suka soma rikici da juna.
Dubban mutane ne suke guduwa domin tserewa lugudan makaman roka da ake harbawa daga Cambodia.
Kazalika Thailand ma na ci gaba da kai wa Cambodia hare-hare ta sama.
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce yana kyautata tsammanin zai gana da shugabannin kasashen biyu ta wayar tarho, wanda ya matsa musu lamba aka cimma kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Yulin da ya gabata.
To sai dai ministan harkokin wajen Thailand ya gargadi Amurka akan amfani da wata barazana ko haraji domin tursasa komawa teburin sulhu don cimma yarjejeniyar zaman lafiya.
bbc