Ambaliya da iska sun lalata gidaje 171 a Gombe — SEMA
Published: 4th, July 2025 GMT
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA), ta ce ambaliya da iska mai ƙarfi sun lalata gidaje 171 a wasu yankunan jihar cikin watanni biyu da suka wuce.
Wannan iftila’in ya jawo asara da kuma rasuwar yara huɗu.
Sojoji sun kashe ’yan ta’adda da ƙwato makamai a Borno Kotu ta umarci a mayar da Sanata Natasha majalisaSakataren hukumar, Malam Abdullahi Haruna Abdullahi ne, ya bayyana wa manema labarai a Gombe cewa ambaliya da iska sun shafi ƙananan hukumomin Dukku, Kwami, Gombe da Akko.
Ya ce: “An samu rushewar gidaje 87 a Dukku, 27 a Kwami, 30 a Gombe, da kuma 27 a Akko.
“Haka kuma wata coci ta lalace. Mafi yawan mutanen da suka mutu yara ne guda huɗu.”
Ya ce rashin tsaftar muhalli da sare bishiyoyi na taimakawa wajen haifar da irin wannan iftila’i.
Ya roƙi mutane da su guji zubar da shara a cikin magudanan ruwa, su kuma yi amfani da wuraren da gwamnati ta tanada domin zubar da shara.
“Dole ne kowa ya taimaka wajen kare muhalli, musamman a lokacin damina. Iyaye su kula da yara domin guje wa hatsari,” in ji shi.
Abdullahi ya kuma nuna damuwarsa kan yadda mutane ke sare bishiyoyi don yin gawayi da girki, inda ya bayyana cewa hakan yana kawo fari da lalacewar muhalli.
Ya shawarci mutane da su yi amfani da damina wajen dasa bishiyoyi a gidaje da unguwanni domin rage hatsarin iska da kuma hana ƙara yaɗuwar hamada.
Hakazalika, ya ce SEMA na shirin kai kayan agaji ga mutanen da ambaliya da iska suka shafa a sassan jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ambaliya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
Daga Ali Muhammad Rabi’u
Gwamnatin Jihar Kwara ta kafa kwamitoci biyu domin tantance bayanan wadanda suka yi ritaya a matakin jiha da kananan hukumomi.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinar Kudi ta jihar, Dakta Hauwa Nuru ta fitar, ta bayyana cewa kwamitocin za su tantance tare da tabbatar da sahihancin bayanan wadanda suka yi ritaya, domin a biya su bisa lokacin da suka bar aikin gwamnati.
A cewarta, kwamitin mutum takwas da aka kafa don kula da kudaden ritaya na matakin jiha zai kasance karkashin jagorancin Mai Duba Asusun Jiha, wato (Auditor General), yayin da wanda ke kula da matakin kananan hukumomi zai kasance karkashin Mai Duba Asusun Kananan Hukumomi.
Sanarwar ta bayyana cewa babban burin kwamitocin shi ne tabbatar da cewa an tattara bayanan masu ritaya bisa gaskiya da adalci, tare da biyan su kai tsaye ta asusun ajiyar banki.
Ta kara da cewa, mambobin kwamitocin sun hada da wakilan tsofaffin manyan sakatarorin, kungiyar tsofaffin ma’aikata, Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), da kungiyar kwadago ta TUC, da sauransu.