Haɗarin Da Ke Ƙunshe Da Jin Ɓangare Ɗaya Na Labari
Published: 4th, July 2025 GMT
A ɗaya ɓangaren kuma
Fita zuwa wani yanki daban da ba naka a halin yanzu, yana da nasa fa’idar. Domin kuwa, na ziyarci wasu jihohi uku kwanan nan; waxanda labarai a kansu babu daxin ji. Jihohin su ne, Delta, Inugu da kuma Zamfara, waxanda galibi labaransu marasa daxi ne ta fuskar siyasa, ta’addanci da sauran munanan laifuka.
Duk da cewa, kowace jiha akwai abubuwan da ta fi bai wa muhimmanci, su ma kamar sauran jihohin; suna fuskantar qalubale na yi wa al’umma aiki ta hanyar samar da damammaki, rage talauci da kuma tsantseni wajen sarrafa dukiyar al’umma.
Duk da cewa, har yanzu akwai sauran rina a kaba, amma abin da na gani a xan wannan lokaci da na ziyarci waxannan jihohi uku, tattakina zuwa Jihar Zamfara; shi ne mafi matuqar tsoro a wajena
Zuwa Gusau
A karon farko da aka gayyace ni zuwa babban birnin jihar, Gusau, sai na yi watsi da tafiyar. Domin kuwa, a tafiya irin wannan akwai buqatar yin tunani da nazari mai zurfin gaske, musamman ganin yadda nake samun munanan labarai a kan Ado Aliero da sauran tawagarsa ta ‘yan ta’adda da ke yankin.
Har ila yau, sai aka sake turo min da wata gayyatar. Amma dai, a wannan karon akwai ɗan qwarin gwiwa, musamman ganin cikin tawagar da zan bi na tattaunawa ta farko da za a yi da Gwamna Dauda Lawal kai tsaye a kan wa’adin shekaru biyu da ya kwashe kan mulki. Tawagar ta qunshi; Gbenga Aruleba daga gidan talajin na AIT, Reuben Abati, ARISE TV da matarsa, Kiki, sai Ahmed Shekarau daga Media TRUST, Onuoha Ukeh daga SUN da kuma Babajide Otitoju, wanda Olajumoke Olatunji ya maye gurbinsa daga TVC.
ChatGPT da Gusau
Amma fa akwai matsala. Ta yaya za mu isa Gasau, duk da sanin abin da muka sani, na tambayi ‘ChatGPT’. Sai amsa min da cewa, kada ku tafi idan har tafiyar ba mai muhimmanci ba ce.
Ya ba da sanarwar tafiye-tafiye daga ofishin harkokin waje na burtaniya, Australia, Canada da kuma Amurka tare da gargaxi game da tafiye-tafiye saboda tashin hankali, ta’addanci da kuma garkuwa da mutane, yana mai bayyana cewa; “Babbar matsaya daga hukumomin kula da tafiye-tafiye, ba ta ba da shawarar yin tattaki zuwa Jihar Zamfara, idan har ba akwai buqatar yin hakan ba.
“Titin Zariya zuwa Zamfara, musamman Funtua da ke Jihar Katsina, Tsafe, Maru-Dansadau, an bayyana su a matsayin wasu yankuna na mutuwa, wato wani filin wasa ne na Dogo Gide da Bello Turji, wanda tawagarsu ta ‘yan ta’adda suka kashe matafiya aqalla 20, kamar yadda rahoton AP ya bayyana a watan Afrilun wannan shekara. Ina kan hanya, amma na qudiri niyyar tafiya.
Mutuwa da dawowa
Na yi ta mutuwa ina dawowa a cikin awa biyu da minti sha biyar, tsoro ya gama kama ni tare da alhinin cewa; idan na mutu a shekara 60, ba wai na mutu da ƙuruciya ba ne. Ban san cewa, matata ta lallava ta sanya min wani abin kariya a cikin wata ‘yar ƙaramar kwalba.
Gaba-xaya ban lura ba, sai da na dawo daga tafiyar ina goge jakata, wannan ya isa ta bugi qirji da cewa; ta taimaka min da wani sirri na kariya. Na kasance a ankare cikin tsawon wannan tafiya ta kimanin kilomita 450 daga Abuja, cike da ximuwa.
Abin da ya ba ni mamaki, titin da ke tsakanin Zaiya da Katsina, mai layi biyu ne, sannan kuma yana da kyau sosai; titin bai tsuke ba sai da muka shiga Katsina, kana kuma ya sake buɗe bayan mun yi nisa ga duwatsu masu ban sha’awa da tsaunika da dukkanin vangarorin titin biyu. Amma titin Abuja zuwa Kaduna, abin kunya ne idan aka kwatanta shi da wannan, amma duk da haka; babban titin Abuja zuwa Kadunan ya lalace, kai ka ce shi ne qofar shiga Arewa Maso Yamma.
Fargaba da ɗimuwa…
Bayan Zariya, a wasu lokuta, mun wuce garuruwa masu yawan jama’a, amma mafi shahara a cikinsu shi ne garin Funtua, garin wasu daga cikin jiga-jigan ‘yan siyasa da suka haxa da marigayi Malam Ismail Funtua da kuma fitaccen xan kasuwa, Umaru Mutallab.
Kowa ya yi tsit, kuma na kasa tambayar kaina cewa; ko mutanen da ke zaune a qauyukan da qananan garuwan da muke ratsawa, sun san abin da ake faxa game da su kafafen yaxa labarai? Yayin da muka shiga Tsafe, garin xaya daga cikin manyan ‘yan ta’addan da suka yi qaurin suna wajen garkuwa da mutane, waɗanda suka samu nasarar share wajen zama a Jihar Katsina kafin ziyarar tamu, duk gashin da ke jikina sai da ya tashi.
Duk da cewa, mun samu rakiyar jami’an ‘yansanda ga kuma shingayen sojoji da dama a hanyar, yayin da muka isa Tsafe, kilomita 48 zuwa Gusau, ba ku ga irin tsoro da firgicin da ke cikin motarmu ba. shiru kake ji kowa ya yi xif.
Bayan Tsafe, na yi zaton tashin hankali ya qare a wannan tafiya. Sai kuma na ji na samu sauqi tare kuma da shiga ruɗani da muka shiga Gusau. Sauqin shi ne da muka isa lafiya, ruxanin kuma saboda titi mai hannu biyu da ake dab da kammala, wanda ya haxe da na Zamfara mai tattare da haɗari da ban tsoro a tare da shi.
An samu canji
Ashe da rabon zan ga irin waxannan al’amuran a Enugu, inda rabo da zuwa tun
2006 (lokacin Chimaroke Nnamani yana gwamna). Ziyarar da na yi zuwa Zamfara na yi ta tun a farkon shekarun 1990, lokacin tana haɗe da Jihar Sakkwato. Bayan wani Kantoman Mulkin Soji xaya, da kuma wasu gwamnonin farar hula huxu, kafin Dauda, na biyar, Zamfara ta kasance wani abu kamar tallan shirin wasan kwaikwayo na Kannywood, inda ‘yan siyasa ke kwashe dukiyar qasa, ciki har da jama’arta, tare da nuna iko
ko shakka babu Dauda zai iya nuna bambanci a wannan tsari. A cikin shekaru biyu, ya inganta asibitocin tuntuva da ke Gusau zuwa asibitin koyarwa mai xauke da wasu kayan aiki na zamani, ya kuma inganta harkar samar da ruwan sha, sannan ya kawar da koma bayan kudin WAEC da NECO na dalibai, lamarin da ya sa jihar ta kasance da ta samu kyakkyawan sakamako na tsawon shekaru. Haka kuma ya gina sabon filin jirgin sama wanda za a iya budewa kafin Satumba.
Gwamnati ta ce ta biya basussukan gratuti da kuma fansho ga ma’aikatan kananan hukumomi da na jiha tun daga shekarar 2011, da aka kiyasta kudin sun kai Naira biliyan 13.6, baya ga biyan bashin albashin watanni hudu da ya gada tare da kara mafi karancin albashi daga Naira 7,000 duk wata zuwa Naira 70,000.
“Komawar harkoki”
A lokacin da ake tattaunawar kai tsaye da Abati ya tambayi Dauda yadda ya sanya jihar a kan turba mai ban sha’awa, ciki har da ba ta wutar lantarki ta farko tun bayan da aka kirkiro ta shekaru 29 da suka gabata, gwamnan ya ce hakan ya faru ne ta hanyar toshe leken asiri ta hanyar amfani da fasaha, da kuma ba da fifiko wajen bunkasa albarkatun jama’a da kuma inganta karfinsu.
Ya ce an kuma yi amfani da fasaha don tattarawa da yin amfani da bayanan sirri don gina jiha mafi aminci, yana mai shan alwashin cewa ba za ai yi sulhu da ‘yan fashi da masu laifi ba.
Idan rayuwar dare ta daidaita a Gusau, babu shakka dukkan jama’ar da suka rasa matsugunai da wuraren sana’a za su dawo inda suke musamman gonaki a hankali. Wannan kuma wani hangen nesa ne da mutum zai iya duba jihar da aka ayyana kusan shekaru talatin ta hanyar cusa tsattsauran ra’ayi na addini, sata da kuma ‘yan fashi.
Ishiekwene Babban Editan LEADERSHIP kuma mai
Rubuce-rubuce a Kafofin watsa labarai da harkokin Kudi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Shin Ko Hadakar Sabuwar Jamiyyar ADC Za Ta Fidda Wa ‘Yan Najeriya Kitse Daga Wuta?
Yan Najeriya da dama na ta bayyana mabanbantan ra’ayoyi kan sabon hadakar ‘yan siyasa zuwa sabuwar jami’yyar ADC.
A yayin da wasu ke ganin wannan hadaka za ta cire musu kitse daga wuta, wasu kuwa gani suke yi duk kanwar ja ce.
A ranar laraban nan ne dai gaggan ‘yan siyasa daga jamiyyu daban daban suka hadu don dinkewa wuri daya da niyyar kalubalantar jamiyya mai mulki ta APC, a cewar su za su ceto Najeriya daga halin da jamiyyar ta jefa su a ciki.
NAJERIYA A YAU: Ɓoyayyun Ƙalubalen Da Sabuwar Haɗakar ADC Za Ta Iya Fuskanta DAGA LARABA: Cutukan Da Sinadaran Yin Burodi Ke HaifarwaShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan ko sabuwar hadakar jamiyyar ADC za ta fidda ‘yan Najeriya daga matsalar da suka ce suna ciki?
Domin sauke shirin, latsa nan