Kayayyakin Sin Na Kara Samun Karbuwa A Kasuwar Duniya
Published: 4th, July 2025 GMT
Kwanan baya, wasu kamfanonin samar da kayan shayi masu tamburan kasar Sin sun jawo hankalin sassan kasa da kasa, sakamakon yadda suka fara sayar da hannayen jarinsu a kasuwar hannayen jari ta kasa da kasa. Baya ga haka, wasu kayayyaki masu tamburan kasar Sin na kara samun karbuwa a kasuwannin duniya.
Wadannan kayayyakin kasar Sin suna samun karbuwa a kasuwannin duniya ne sabo da fasahohin zamani da al’adu da ke tattare da su da ma yadda aka tsara fasalinsu, kuma hakan ya faru ne sakamakon cikakken tsarin samar da kayayyaki da yanayin kasuwa mai bude kofa da adalci a kasar, da ma yadda kasar ta dade tana dukufa a kan kirkire-kikire da kuma samun ci gaba mai inganci.
Shiga kasuwannin duniya da kayayyakin kasar Sin suka yi na bai wa masu sayayya na duniya damar samun karin zabi. A sa’i daya kuma, Sin na maraba da zuwan karin kamfanonin ketare masu ingantattun tamburan kasar, ta yadda za a yi koyi da juna da samun ci gaba tare, don al’ummun duniya su ci gajiyar dunkulewar tattalin arzikin duniya. (Mai zane da rubutu: MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Aragchi: Hare-Haren HKI Ya Kara Rashin Zaman Lafoya A Yankin Yammacin Asiya
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hare-haren HKI da Amurka a yankin yammacin Asiya ya kara rashin zamn lafiya a yankin.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadin haka ne a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Girka a jiya talata . Ya kuma kara da cewa hare-haren sun yu watsi da hanyar zaman lafiya da kuma zaman lumana a yankin. Ya kuma yi sanadiyyar karin tashe tashen hankula a yankin.
Ministan ya bukaci kasashen duniya gaba daya su yi tir da HKI da kuma Amurka wadanda suka keta hurumin kasa mamba a MDD ba tare da wani daloli nay an haka ba. Ya ce hare-haren da kasashen biyu suka kaiwa JMI wanda ya cinye rayukan mutane da dama ya sabawa kudurin MDD ta 2231, wanda hakan barazana ce ga zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa.
Ministan ya kara da cewa wadannan hare-hare sun zo ne a dai-dai lokacinda Iran da Amurka suna kan teburin tattaunawa don fahintar juna kan shirin Nukliyar kasar. Wanda haka yin watsi da hanyar diblomasiyya da kuma zaman lafiya ne.
Daga karshe ministan ya bayana cewa ayyukann ta’addanci wanda HKI take aikatawa a Gaza shi ne yake kunna wutan fitina a yankin da kuma duniya gaba daya.
A nashi bangren ministan harkokin wajen kasar Girka ya ce, yana mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wadannan hare-hare sannan yana fatan tsagaita wutan da aka samu zai dore. Ya kuma nuna damuwarsa da abinda yake faruwa a gaza kan falasdinawa musamman rashin barin abinci ya shiga yankin.