2025-10-29@00:24:13 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2534
«duwatsu masu daraja»:
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa matasa dubu ɗaya (1,000) za su samu horo kan tsaron yanar gizo (cyber security) da fasahar binciken dijital (digital forensics) ta hanyar Cibiyoyin Koyon Fasahar Dijital ƙarƙashin Shirin Renewed Hope Initiative (RHI) a Jihar Nasarawa. Uwargidan Shugaban Ƙasan ta bayyana haka ne yayin bikin kaddamarwa da...
Uwargidan Shugaban Ƙasa ta Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta kaddamar da Dijital E-Learning Library a Gusau, Jihar Zamfara — ɗaya daga cikin jihohi goma da aka zaɓa a faɗin ƙasar domin aiwatar da wannan muhimmin aiki ƙarƙashin Shirin Renewed Hope Initiative (RHI) tare da haɗin gwiwar Hukumar bunkasa ayukkan fasaha ta kasa (NITDA). A yayin...
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa gobara ta lalata rumfuna 529 daga cikin rumfuna na wucin gadi a Kasuwar Shuwaki da ke ƙaramar hukumar Gari, Jihar Kano. Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar, Alhaji Saminu Abdullahi, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Kano. A cewarsa,...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzuwar Shekarar 2025 Sanata Oluremi Tinubu October 24, 2025 Manyan Labarai Dauda Lawal Gwarzon Gwamnan 2025: Ceto Zamfara Domin Ci Gaba October 24, 2025 Manyan Labarai Buƙatar Daƙile Badaƙalar Amfani Da Takardun Karatun Bogi A Nijeriya October 24, 2025
Baya ga haka, sabon ginin ma’aikatar harkokin mata da ci gaban al’umma ta Jihar Zamfara da aka sake ginawa da kuma sabon ginin kwalejin fasaha da kimiyya na Jihar Zamfara (ZACAS) da aka gyara, sun yi matuƙar haskaka Gwamnatin Dauda Lawal. Har ila yau, jihar ta samu gagarumin ci gaba wajen inganta fannin kiwon lafiya...
Kazalika, har yanzu batun tsohon shugaban Majalisar Wakilai wato Salisu Buhari, na 1999, na yin amfani da Takardun karatu na bogi da ya yi iƙirarin ya samo daga Jama’iar Toronto, baƙalar na ci gaba da kafa babban misali, a ƙasar. Badaƙalar ta sa, ba ta tsaya nan ba, ya kuma ƙaryar shekarun na haihauwa, domin...
Sashen haƙar ma’adinai na Cote d’Ivoire da ke samun ci gaba cikin sauri zai fuskantar matsala da tsaiko kafin zaɓen shugaban ƙasa na ranar Asabar, yayin da Shugaba Alassane Ouattara ke neman wa’adi na hudu. A cewar Reuters, haƙar ma’adinai muhimmin ɓangare ne daga cikin ayyukan da Ouattara yake mayar da hankali a kansu, don...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A cikin ‘yan watannin da suka gabata, an sake ganin karuwar hare-haren Boko Haram da ISWAP musamman a yankin Arewa maso Gabas. Kazalika, ko a kwanan nan ma anga irin wadannan hare hare. Wadannan hare-haren sun fi karkata kan sansanonin sojoji, inda ake samun asarar rayuka da...
Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya rantsar da Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC). An gudanar da bikin rantsarwar ne a ranar Alhamis a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, mako guda bayan Majalisar Dattawa ta amince da nadinsa a ranar 16 ga watan Oktoba. Sanarwar Bayan...
An zargi mayaƙan Boko Haram da ISWAP da kai hare-hare wasu yankuna biyar da ke Jihohin Borno da Yobe. Sun kai hare-haren ne garuruwan Mafa, Dikwa, Marte, da Ajiri a Jihar Borno, da kuma Katarko a Jihar Yobe. Jami’an tsaro sun kama Sowore saboda shirya zanga-zanga DSS ta cafke mutum 3 kan zargin sayar wa...
Sanarwar ta ce, sojojin sun yi aiki da sahihan bayanan sirri, sun kama wanda ake zargin tare da kwato bindiga kirar AK-47 guda daya, da wata mujalla cike da harsashai na musamman masu tsawon 7.62mm har guda 10, wayar hannu, da kuma kudi naira 12,000. “Sakamakon nasarar da aka samu ya haifar da...
Har ila yau, an kama wasu mutane biyu da ake zargi a kauyen Doka da ke Kachia, kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, yayin da ake zarginsu da safarar bindigogi kirar AK-47 guda uku ga ‘yan bindiga a cikin wata mota kirar Golf. Da yake mayar da martani kan wannan ci gaban, Gwamna Uba Sani...
“Allah ya albarkace mu da shugaba mai tsoron Allah da kishin jama’a – mutum ne mai kaunar al’ummar jihar Kano da Nijeriya, kuma me aiki tukuru domin ganin ci gabansu,” in ji Yusuf. Ya kuma jaddada kudirin sa na ciyar da jihar gaba bisa tsarin falsafar Kwankwasiyya, wanda ke jaddada hidima, rikon amana, da...
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da yin ƙarin albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikata daga cfa 30,000 zuwa cfa 42,000, wanda ya yi daidai da naira 108,780 a Najeriya. Wannan ƙarin albashi na daga cikin matakan gwamnatin domin inganta rayuwar ma’aikata da ƙarfafa su wajen gudanar da ayyukansu na yau da kullum, kamar yadda gwamnatin ta...
Shugabannin jam’iyyar PDP Na Arewa Sun Amince Da Turaki A Matsayin Ɗan Takarar Shugabancin Jam’iyyar Na Ƙasa
Sanarwar da aka fitar a karshen taron ta bayyana cewa, matakin na daga cikin kokarin da ake yi na karfafa hadin kan jam’iyyar da tabbatar da daidaiton wakilcin yanki a cikin tsarin shugabancin jam’iyyar PDP. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Waɗanda Fashewar Tankar Mai Ta Rutsa Da Su A Neja ...
Masu Tasiri a Kafafen Sada Zumunta sun samu horo kan RMNCAH+N, Tsarin Iyali da Rigakafin Cin Zarafin Mata
Ƙungiyar Centre for Communication and Social Impact (CCSI) tare da haɗin gwiwar abokan aikin ta na EngenderHealth Consortium sun shirya taron horo na yini ɗaya a Kano domin ƙarfafa ƙwarewar ’yan jarida da masu tasiri a kafafen sada zumunta (social media influencers) wajen yada sahihan bayanai da tallafawa manufofin kiwon lafiya da daidaito tsakanin jinsi....
Kwamishinan Ilimi Na Kano Ya Yi Kira Da A Karfafa Shugabancin Makarantu Domin Inganta Karatun Dalibai
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda, ya jaddada muhimmancin samun ƙwararrun shugabannin makarantu wajen inganta koyarwa da haɓaka sakamakon karatu a fadin makarantun jihar. Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi, Kwamared Balarabe Abdullahi Kiru, ya sanya wa hannu. ...
Gwamnatin Tarayya ta koka da cewa, duk da wayar da kan jama’a da kuma gargadin da ake ci gaba da yi, wasu mutane har yanzu suna kasada da rayukansu ta hanyar yunƙurin ɗibar mai yayin da tankunan dakon mai suka faɗi. Ya jaddada cewa, kowace rai ta ɗan Nijeriya tana da daraja kuma irin...
Hon. Musa ya kara da cewa, aikin zai mayar da hankali ne kan nazari da binciken kimiyyar kasa a yankunan da ake tunanin cewa suna dauke da uranium, danyen man fetur, da iskar gas, da nufin tattara dukkan bayanan da ake bukata don ci gaba da aiki. A cewar kwamishinan, amincewar wani bangare ne...
Tehran ta yi maraba da hukuncin da wata kotun Faransa ta yanke na yi wa ‘yar kasar Mahdieh Esfandiari saki bisa sharadi. ‘yan sandan Faransa sun dai kama ‘yar Iran din ce bisa zarginta da goyan bayan ta’addanci mai nasaba da nuna goyan bayan al’ummar Gaza . Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran,Esmail Baghaei ya ce...
Gwamnatin Jihar Ondo ta roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu bayan gargaɗin da Hukumar Tsaro ta DSS, ta yi na cewar wasu mayaƙan ISWAP na shirin kai hari wasu sassan jihar. A cikin wata sanarwa, Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Mista Idowu Ajanaku, ya bayyana cewa irin waɗannan rahotanni abu ne na yau da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ranar 26 ga watan Yuni, shekara ta 2025, gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan sabon tsarin haraji wanda za a fara aiwatarwa daga ranar 1 ga Janairu, 2026. Wannan sabon tsarin haraji na daga cikin matakan da gwamnati ke cewa zai taimaka wajen kara samun kudaden...
Shugaban ƙasa mai ci, Alassane Ouattara, shi ne wanda aka fi yi wa hasashen nasara a zaɓen da za a gudanar a Ivory Coast ranar Asabar, sakamakon rashin wasu jiga-jigan ’yan adawa da za a fafata da su a zaɓen. Ouattara, mai shekara 83, yana riƙe da madafun iko tun daga shekarar 2011, lokacin da...
A cewar sanarwar, “A ranar 15 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 11:00 na rana, wata mata da ke zaune a unguwar Federal Low-Cost, Gombe, ta bayyana cewa a daidai wannan ranar da misalin karfe 2:30 na dare, wani wanda ba ta san ko wanene ba, dauke da wuka ya kai mata hari, inda ya...
Ya ce tallafin da Shugaba Tinubu ya amince da shi ba rance ba ne, wani bangare ne na yunkurin gwamnati na cire shingen da ke hana ’yan kasuwa ci gaba. Ya ƙara da cewa gwamnati ta kafa asusun Naira Biliyan 75 da sunan tallafin ga ƙananan masana’antu da yan kasuwa (MSME Intervention Fund), wanda...
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya ce zai yi matuƙar wuya a samu shugaban da zai saita Najeriya, idan har Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya gaza cika alƙawuran da ya ɗauka. Shehu Sani, ya bayyana haka ne yayin hira a gidan talabijin na TVC, inda ya bayyana cewa Tinubu na da damar...
Majalisa Ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Kai Agajin Gaggawa Ga Waɗanda Fashewar Tanka Ta Shafa A Neja
Mummunan lamarin na ranar Talata ya kasance kwatankwacin abin da ya faru a watan Janairu kamar yadda rahotanni suka ce, mutane sun taru a kauyen Essa, suna kwasar mai daga wata tankar mai da ta kife, daga nan kuma sai ta fashe wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 35, da jikkata...
Ahmed maiyaki, ya dade yana bayar da gudummawa a harkar yada labarai a a fadin kasar nan bayan kasancewarsa tsohon ma’aikaci a sashin hausa na rediyon Faransa ( FRI). Jihar Kaduna ta kwashe shekaru takwas babu ma’aikatar yada labarai wacce tsohon gwamna Nasir El-Rufai ya rufeta , sai bayan lashe zaben gwamna Uba Sani...
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Zamfara ta gargaɗi direbobi da sauran jama’a game da rufe lambobin motoci, musamman a cikin garin Gusau, babban birnin jihar. Gargaɗin ya biyo bayan ƙaruwa da ake samu na rahotanni da kuma lura da direbobi da ke tafiya da lambobin motoci a rufe, wanda rundunar ta bayyana a matsayin karya...
Wannan tsarin na taimaka wa yara su samu ilimi mai zurfi da zai ba su damar daidaita da tsarin rayuwarsu na yau da kullum. Makarantun suna da ɗakunan kwana, gidajen malamai, wutar lantarki mai amfani da hasken rana, rijiyoyin burtsatse, kujeru, kayan karatu, da cibiyar koyon sana’o’i kamar ɗinki, sassaƙa, kwamfuta, da sauransu. Haka kuma,...
Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya, Fasaha da Kirkire-Kirkire ta Jihar Borno ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun Firamare da Sakandare na gwamnati da masu zaman kansu na tsawon kwanaki biyu domin gudanar da aikin rigakafin cututtukan ƙyanda da shan inna. Sanarwar umarnin rufe makarantun ta fito ne daga ofishin Kwamishinan Ma’aikatar, a ranar Talata, a birnin...
Piwuna, ya ce gwamnati ta gaza cika alƙawurran da ta ɗauka duk da sanarwar kwanaki 14 da ASUU ta bayar tun a ranar 28 ga Satumba, 2025. Ya ce babu wani abin da aka cimma wanda zai hana ƙungiyar aiwatar da shawarar majalisar zartarwarta na fara yajin aikin. “Dukkanin rassan ASUU a faɗin ƙasar nan...
Ya ƙara da cewa shirin ya dace da shirin jihar, inda zai mayar da hankali kan bunƙasa samar da abinci a gida da karfafa matan gida wajen kula da abinci mai gina jiki. Gwamnan ya bayyana cewa majalisar kula da abinci ta jihar za ta jagoranci tsara manufofi, haɗin kai da kuma kula da aiwatar...
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya karyata zargin kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya, yana mai cewa wannan ikirari ƙarya ne kuma bai kamata a ci gaba da yada shi ba. Sarkin ya bayyana hakan ne a taron Babban Majalisar Sarakunan Gargajiya na Arewa na shekarar 2025, wanda aka gudanar a Birnin Kebbi, Jihar...
Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta bayyana baƙin cikinta game da gobarar tankar mai da ta tashi a ƙaramar hukumar Katcha ta Jihar Neja, inda mutane 38 suka rasa rayukansu. A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta jajanta wa jama’a da gwamnatin Jihar Neja,...
Sanarwar ta ce, “Domin rage wahalhalun da al’umma ke fuskanta wajen samun kula da lafiya, gwamnatin Dauda Lawal ta ƙaddamar da wannan shiri na musamman domin tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi da ke buƙatar jinya.” Shirin, wanda aka fara a watan Agusta 2023, ya riga ya isa ga marasa lafiya sama da 3,400 zuwa...
Gwamna Yusuf ya lura cewa, wasu kafafen yada labarai na yanar gizo suna amfani da manhajojin su wajen yada “labarai masu raba kan addini da siyasa,” wanda a cewarsa, za su iya gurgunta hadin kan al’umma da kwanciyar hankali idan ba a magance su ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Majalisa Ta Tabbatar Da...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira biliyan ɗaya domin gyaran ajujuwan karatu a wasu makarantu na gwamnati. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse. A cewarsa, majalisar zartarwar jihar ta amince...
Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya rattaba hannu kan dokar ƙirƙirar sabbin masarautu 13 wadda za ta ba da damar naɗin hakimai sama 111 a faɗin jihar. Sabbin masarautun da gwamnan ya ƙirƙira sun haɗa da: Burra, Duguri, Dambam, Bununu, Lere, Darazo, Jama’a, Lame, Toro, Ari, Warji, Giade da kuma masarautar Gamawa. Uba Sani ya...
“Wadanda aka nada sun bayyana a gaban kwamitin don tantancewa a ranar Talata, 14 ga Oktoba, 2025,” in ji shi. “Kwamitin bai samu koke ko korafe-korafe ba a kansu, sun nuna shiri da cancanta akan ayyukan da aka zabo su”. Ya bayyana sunayen wadanda aka tantance a matsayin: “Aminu Yusuf (Jihar Neja) –...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia October 21, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Bayar Da Tallafin Dala Miliyan 3.5 Ga Shirin Samar Da Abinci A Zambia October 21, 2025 Daga Birnin Sin Matsayar Kasar Sin A Bayyane...
Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da aiwatar da ƙarin kashi 70 a albashin ma’aikatan dukkanin makarantun gaba da sakandare na gwamnati da ke jihar. Sabon tsarin albashin na CONPCASS/CONTEDISS 2024 wanda zai fara aiki daga Oktoban 2025, na daga cikin kokarin gwamnatinsa na inganta walwalar ma’aikata da farfaɗo da harkar ilimi a jihar....
Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi
Tattaunawar wacce aka gudanar a gidan gwamnati dake Kaduna, kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, da majalisar jihar Kaduna karkashin jagorancin Kwamared Ayuba Suleiman ne ta dauki nauyin gudanar da taron, kuma wakilan kungiyoyin ma’aikatan manyan makarantun ilimi na kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli, Zariya; Kwalejin Ilimi, Gidan Waya; da kwalejin koyon aikin jinya...
Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya sanar da shirinsa na ɗaga darajar Kwalejin Jinya ta Nafisatu da ke Kwankwaso zuwa cikakkiyar Jami’ar Kiwon Lafiya albarkacin bikin zagayowar ranar haihuwarsa. Taron na wannan Talatar, 21 ga watan Oktoban 2025, ya gudana ne a garinsa na Kwankwaso da ke Karamar Hukumar Madobi, inda aka yaba...
Sun ce wadanda suka mutu yawancinsu wadanda suka je kwaso man fetur ne a lokacin da tankar ta yi hatsari kafin fashewar. Shugabannin Direbobin Tankar Mai na Jihar Neja (PTD) da Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas ta Nijeriya (NUPENG) ta kasa, Kwamared Farouk Mohammed Kawo, sun tabbatar wa LEADERSHIP faruwar lamarin. ShareTweetSendShare MASU...
Kasar Equatorial Guinea, ta zargi Faransa da karan tsaye wa zaman lafiya a kasar. mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Nguema Obiang Mangue ya yi tir da “tsarin Faransa na neman da yunkurin kawo cikas ga zaman lafiya a kasar, . A wani sakon da ya wallafa a shafin X.. Faransa na goyan bayan ‘yan...
DSS ta gurfanar da su bisa tuhumar laifuka 32 da suka shafi ta’addanci. Usman ya amsa laifi ɗaya kacal na haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, amma ya musanta sauran. Abba kuwa ya ƙi amsa dukkanin laifukan da ake tuhumar sa da su. An zarge su da kai hari sansanin soja na Wawa da ke...
Kwamandan ya ƙara da cewa yayin yaƙin “Operation Zero” na shekarar da ta gabata (Disamban 2024 zuwa Janairun 2025), mutane 432 ne suka mutu, yayin da 2,070 suka jikkata a haɗura 533; adadin ya ragu idan aka kwatanta da na baya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako...
NLC ta kuma buƙaci gwamnati ta bi shawarar UNESCO wacce ta ke cewa ya kamata a ware aƙalla kashi 25 cikin 100 na kasafin kuɗi na kowace shekara ga ilimi. Ajaero, ya yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta kasa magance matsalolin cikin makonni huɗu, NLC za ta haɗa dukkanin ma’aikata na ƙasa don gudanar da...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu October 21, 2025 Labarai An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole October 20, 2025 Labarai Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU October 20,...