An Kashe Mutum 10 A Harin Ramuwar Gayya A Jihar Kebbi
Published: 28th, October 2025 GMT
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu October 28, 2025
Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno October 28, 2025
Manyan Labarai APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba October 27, 2025
এছাড়াও পড়ুন:
NSCDC ta yi alhinin mutuwar Kwamishinan Tsaron Gombe
Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) reshen Jihar Gombe, ta bayyana alhini bisa rasuwar Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar, Laftanar Kanar Abdullahi Bello (mai ritaya).
Haka kuma hukumar ta bayyana jimami kan da ɗan sandan da ke tsaron kwamishinan, Sajan Adamu Husaini, da direbansu, wadanda suka rasu a wani mummunan hadarin mota da ya afku ranar Juma’a.
Sojoji sun daƙile harin ISWAP a Borno An ba da tallafin N2m ga iyalan jami’in NSCDC da aka kashe a JigawaA wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na NSCDC a jihar, SC Buhari Sa’ad, ya fitar, Kwamandan hukumar, Jibrin Idris, ya ce rasuwar babban rashi ce ba ga iyalan mamatan kawai ba, har ma ga Gwamnatin Jihar Gombe da al’ummar jihar baki ɗaya.
Kwamandan ya mika ta’aziyyarsa ga Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, da iyalan mamatan da abokan aikinsu, yana mai jaddada irin jajircewar da suka nuna wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.
“Kwamishina Abdullahi Bello da Sajan Adamu Husaini da direbansu sun bayar da gudunmawa mai muhimmanci ga sha’anin tsaro a Gombe. Rasuwarsu babban rashi ne ga kowa da kowa,” in ji Kwamandan Idris.
Ya yi addu’ar Allah Ya jikansu, Ya ba su Aljannatul Firdausi, tare da ba iyalan da suka bari hakurin jure wannan babban rashi.
Laftanar Kanar Abdullahi Bello kafin rasuwarsa, shi ne Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Gombe, wanda aka san shi da jajircewa da kishin kasa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.