Sin Za Ta Yi Tsayin Daka Wajen Kare Tsarin Cinikayya Tsakanin Mabanbantan Sassa
Published: 27th, October 2025 GMT
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce kasar Sin a shirye take ta yi aiki wajen kare tsarin cinikayya tsakanin mabanbantan sassa bisa matukar himma, tare da kasancewa cikin shirin aiki tare da dukkanin sassa, don kare martabar cudanyar mabanbantan sassa bisa gaskiya.
Li, ya yi tsokacin ne cikin jawabinsa a yau Litinin, yayin taron shugabanni karo na biyar, na cikakkiyar yarjejeniyar kawance ta cinikayya cikin ‘yanci ta yankin Asiya da Fasifik ko RCEP, wanda aka bude a birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia.
Kazalika, a birnin na Kuala Lumpur, yayin da yake jawabi a dandalin taron kasashen gabashin Asiya karo na 20, Li Qiang ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da mabanbantan sassa, wajen ingiza aiwatar da shawarar kyautata jagorancin duniya, da hada karfi-da-karfe wajen ingiza nasarar samar da zaman lafiya da ci gaban shiyyarta. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Babbar Kasuwar Fim Ta Sin Babbar Damar Nollywood Ce
Zuwa karfe 5:41 na daren ranar 7 ga watan Disamba, fim din Amurka “Zootopia 2” wanda aka fara nuna wa kwanaki 12 da suka wuce (tun daga ranar 26 ga Nuwamba), ya samu kudaden shiga a cikin kasar Sin da yawansa ya wuce yuan biliyan 30 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 424.8, adadin da ya zarce kudaden shiga da ya samu a kasashen Arewacin Amurka, har ya sa kasar Sin ta zama kasa mafi taka rawa wajen samar da kudin shiga ga wannan fim a duniya. Hakan kuma ya nuna yadda Sin ke da babbar kasuwar fina-finai.
Ibrahim Akopari Ahmed, jami’in kula da harkokin cinikayya a Najeriya, a zantawarsa da dan jarida a baya, ya taba bayyana cewa, “Najeriya na daya daga cikin manyan kasashe mafiya karfin tattalin arziki a Afirka, kuma sana’o’i masu alaka da samar da hidimomi ne ke ba da gudunmawa mafi yawa ga GDPn kasar, wanda ya zarce kashi 50 cikin 100 na GDP. Saboda haka, Najeriya tana da karfi a bangaren sana’o’in samar da hidimomi, musamman a fagen nishadantarwa, kamar masana’antun samar da fina-finai ta Najeriya (Nollywood). A wannan fage, muna kan gaba a Afirka.”
Najeriya babbar kasa ce ta samar da fina-finai a Afirka, yayin da Sin ke da babbar kasuwar kallon fina-finai. Hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ta fannin fina-finai yana da makoma mai haske, kuma a hakika Sin da Najeriya na karfafa hadin gwiwa a wannan fanni. Alal misali, an gudanar da bikin fina-finai na kasa da kasa na Zuma karo na 15 a farkon wannan watan a babban birnin Najeriya Abuja, inda aka nuna fina-finai biyu daga Sin: wato “Rooting” da “Shen Zhou 13”. Babban manajan kamfanin samar da fina-finai ta Najeriya Ali Nuhu ya bayyana cewa, yana fatan ta wannan taron, za a kara zurfafa hadin gwiwar sana’o’in samar da fina-finai tsakanin Sin da Najeriya. Muna fatan a karkashin tsarin “dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka” da ma sauran irin dandalin hadin gwiwa, Sin da Najeriya za su kara karfafa huldar al’adunsu, ta yadda a nan gaba za a samu karuwar shigowar kyawawan fina-finai daga Najeriya zuwa nan kasar Sin, don baiwa masu kallo na kasar Sin karin damammaki na fahimtar Afirka, musamman Najeriya.(Mai zane da rubutu: MINA)
ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA