Ba Za A Samu Ƙarancin Man Fetur A Lokutan Bukukuwan Ƙarshen Shekara Ba – Dangote
Published: 27th, October 2025 GMT
Wannan tabbacin ya zo ne a daidai lokacin da farashin famfon mai ke canzawa a faɗin ƙasar, wanda tun daga kusan ₦189 a kowace lita a shekarar 2023 zuwa sama da ₦1,000, kafin ya daidaita tsakanin ₦800 da ₦900 a farkon shekarar 2025.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Dangote na shirin faɗaɗa matatarsa don zama mafi girma a duniya
Alhaji Aliko Dangote, na shirin faɗaɗa matatar mansa domin ta riƙa tace gangar mai miliyan 1.4 a kowace rana.
A halin yanzu, matatar tana tace gangar mai 650,000 a rana, amma Dangote, ya bayyana cewa suna shirin ƙara adadin cikin shekaru uku masu zuwa.
Ba zan sake tsayawa takara ba, zan bai wa matasa dama — Dasuki El-Clasico: Real Madrid ta doke Barcelona da ci 2Ya bayyana haka ne yayin wani taro da manema labarai a ranar Lahadi, inda ya ce faɗaɗa aikin zai sa matatar ta zama mafi girma a duniya.
“Wannan shiri yana nuna yadda muke da cikakken shiri a Afirka da kuma dogaro da makomar Najeriya a ƙarƙashin shugabancin Bola Tinubu,” in ji shi.
Ya bayyana cewa aikin zai gudana cikin sauƙi saboda kamfanin ya riga ya gina muhimman kayan aiki da ake buƙata.
Dangote, ya ƙara da cewa wannan aikin zai taimaka wajen samar da man fetur ɗin da Afirka ke buƙata, da kuma rage shigo da mai daga ƙasashen waje.
A cewarsa aikin zai samar da guraben aiki har 65,000, inda kashi 85 cikin 100 na ma’aikatan za su kasance ’yan Najeriya.
“Manufarmu ita ce mu samar da guraben aiki da horar mutanenmu,” in ji shi.
Dangote, ya kuma sanar da cewa matatar za ta kasance a kasuwar hannun jari ta Najeriya a shekarar 2026, domin ’yan Najeriya su samu damar siyan hannayen jari.
“Muna so kowane ɗan Najeriya ya mallaki wani ɓangare na wannan matatar,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa za ake biyan kuɗin aikin daga ribar da kamfanin ke samu, tare da taimakon wasu manyan masu saka hannun jari.